Shafin Ligonier

Tsararrun rubuce-rubuce masu motsa tunani daga fastoci masu hazaka da malaman Littafi Mai Tsarki suna magana akan jigo na Littafi Mai Tsarki, tauhidi, da kuma jigogi masu amfani don ƙarfafa Kiristoci masu girma cikin bangaskiyarsu.


 


03/09/2026

Mene Ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce Game Da Auren Mata Fiye Da Guda Ɗaya?

Auren mata fiye da guda ɗaya al'ada ce da aka keɓe ga abin da za mu iya kira "kashi ɗaya cikin ɗari." Yayin da Tsohon Alkawari ya ambaci waɗannan misalan auren mata fiye da guda ɗaya, bai taɓa nuna amincewa da wannan al'ada ba.
01/09/2026

Menene Kiristoci Suka Yi Imani Da Shi Game Da Wahayin Allah?

Allah yana sanar da kansa da kuma nufinsa ga 'yan adam ne kawai ta hanyar bayyana kansa, wato wahayi. Wannan ya zama dole ga 'yan adam a matsayin halittu domin su san Allah, domin Allah a matsayin Mahalicci ya daukaka kuma ya bambanta da halittunsa. 'Yan adam ba za su iya sanin Allah ba sai dai idan ya zaɓi ya bayyana kansa.
27/08/2026

Yaushe Yesu ya mutu?

Duk da yake Littafi Mai Tsarki bai lissafa kwanan watan gicciye shi ba yadda muke tsammani a zamanin yau, babu musun lokaci da wurin da abin ya faru. Ta fahimtar yanayin wannan gaskiyar tarihi, muna amfani da irin dabarar da muke amfani da ita wajen amsa tambayar nan, “Shin Yesu ya kasance a cikin kabari har tsawon kwanaki uku?” Mutuwar Yesu Banazare a tarihi sanannen abu ne. An gicciye shi ranar Juma’a, 3 ga Afrilu, shekara ta 33 bayan haihuwar Almasihu (AD 33), kuma ya mutu da karfe 3 na rana, a Golgota, kusa da birnin/wajen kofar birnin Urushalima.
25/08/2026

Halayen Ƙauna

Mene ne ƙauna? Ta yaya za ku sani ko kuna kiyaye dokar Kristi ta ƙaunar ’yan’uwanku Kiristoci? Ta yaya mutum mai ƙauna yake bi da wasu? Kafofin yaɗa labarai na yau da kullun sukan gabatar da ƙauna a matsayin jan hankali da jin dadi, amma irin waɗannan abubuwan jin daɗin suna tashi suna kuma sauka kamar yadda ma’aunin zafi yake hawa da sauka. Muna buƙatar ƙauna wadda ba ta yi kama da ma’aunin zafi ba, amma ta fi kama da na’urar daidaita zafi — wadda ke sarrafa yadda muke mayar da martani maimakon su sarrafa mu.
18/08/2026

Fitaccen Matsakaici

Ingantaccen dalilin kwarewa shi ne neman nasara domin manufar ɗaukaka Allah. Wannan shi ne babban dalilin da aka halicce mu dominsa, wato mu ba da shaida ga ɗaukakarsa. Abin da ba ya nuna daukakar Allah shi ne mutum ya saba da yin abin a matsakaici, ko ya gamsu da yadda yake ba tare da kokarin ingantawa ba.
13/08/2026

A Lokacin da Nake Jin Nake Jin Kamar Na Tsaya Cik

A wannan wuri mai nisa, muna zama ganima cikin sauƙi ga wani baƙin tauhidi da aka gina a kan yadda muke ji. Wani yanayi na makawa mai baƙanta zuciya yana biyo baya: Ba ma jin Allah yana magana, don haka muna daina karanta Littattafanmu masu Tsarki. Ba ma jin Allah yana sauraro, don haka muna daina yin addu'o'inmu. Rashin kuzari yana dusashe komai; ba mu samun wani ci gaba. Mene ne ya kamata a yi?
11/08/2026

Wuri Mafi Tsarki

Ubangiji ya ba wa mutanensa alfarwar domin ta hanyar Maganarsa, da alamun sakalamenti na alheri da ke cikin firistoci da hadayu, da kuma addu'o'in da aka miƙa a can, ya zauna a tsakaninsu cikin alheri da jinƙai. Abin ban mamaki, har yanzu yana zaune a tsakaninmu a yau (Afis. 2:18–22).
06/08/2026

Menene Alkawarin Ayyuka?

Muna kiran alkawari da Allah ya yi da Adamu Alkawarin Ayyuka domin biyayyar mutum ita ce hanyar da za a sami albaarkar alkawarin. Idan Adamu ya yi biyayya ga Allah ta wurin cika umurinsa – ya hayayyafa, ya mallaki duniya yadda Allah ya umarta, kuma ya guji cin daga itacen da aka hana – da ya sami rai na har abada. Haka kuma, zuriyarsa ma da sun amfana da wannan albarka. (Far. 1:28; 2:15–17).