
Ragwanci & Himma
28/07/2026
Menene Littafi Mai Tsarki ya ce game da mata Fastoci?
04/08/2026Shin Ikkilisiya tana cike da munafukai ne?
Kimanin shekaru talatin da suka gabata, abokina na kurkusa kuma abokin aiki, Archie Parrish, wanda a lokacin yake jagorantar shirin Evangelism Explosion (EE) a Fort Lauderdale, ya zo mini da wata bukata. Ya bayyana cewa a cikin dubban ziyarce-ziyarce na wa’azin bishara da ƙungiyoyin EE suka yi, sun adana bayanan martanin da mutane suka bayar game da tattaunawar bishara. Sun tattara tambayoyi da hujjojin ƙi da mutane suka fi bayarwa game da bangaskiyar Kirista, sannan suka rarraba waɗannan tambayoyi ko hujjoji zuwa guda goma da aka fi fuskanta. Dr. Parrish ya tambaya ko zan rubuta littafi don amsa waɗancan hujjojin don masu bishara su yi amfani da shi a aikinsu na wa’azi. Wannan ƙoƙarin ya haifar da littafina Objections Answered, wanda yanzu ake kira Reason to Believe. Daga cikin manyan hujjoji guda goma da aka kawo, akwai hujjar nan cewa ikklisiya cike take da munafukai. A wancan lokacin, Dr. D. James Kennedy ya mayar da martani ga wannan hujja da cewa, “To, ai koyaushe akwai wuri don karin mutum daya.” Ya gargaɗi mutane cewa idan suka sami cikakkiyar ikklisiya, kada su shiga cikinta, domin yin hakan zai ɓata ta.
Kalmar munafuki ta samo asali ne daga duniyar wasan kwaikwayon Girka. An yi amfani da ita ne wajen bayyana abin rufe fuska da ’yan wasan kwaikwayo ke amfani da su domin kwaikwayon wasu matsayoyi. Har wa yau, ana wakiltar gidan wasan kwaikwoyo da fuskoki biyu na abin rufe fuska – daya na dariya, daya na bakin ciki. A zamanin dā, wasu ’yan wasan kwaikwayo sun taka matsayoyi fiye da guda ɗaya, kuma suna nuna matsayinsu ne ta hanyar riƙe abin rufe fuska a gaban fuskarsu. Wannan shi ne asalin manufar munafunci.
Amma zargin nan cewa ikklisiya cike take da munafukai a bayyane yake cewa ƙarya ne. Ko da yake babu wani Kirista da yake kaiwa ga matakin tsarkakewa cikakke a wannan rayuwar, kasancewar dukanmu muna fama da zunubi da ke ci gaba ba ya ba da kyakkyawar hujjar yanke hukuncin cewa mu munafukai ne. Munafuki shi ne mutum da yake yin abin da yake cewa ba ya yi. Masu lura da ikklisiyaKirista daga waje suna ganin mutanen da suke cewa su Kiristoci ne kuma suna lura cewa suna yin zunubi. Tun da yake suna ganin zunubi a rayuwar Kiristoci, sai su yi gaggawar yanke hukunci cewa saboda haka waɗannan mutanen munafukai ne. Idan mutum ya fadi cewa shi ba shi da zunubi sannan kuma ya nuna zunubi, tabbas wannan mutumin munafuki ne. Amma don Kirista ya nuna kawai cewa shi mai zunubi ne, hakan ba ya tabbatar da shi a matsayin munafuki.
Tunani karkatacce ya kasance kamar haka: Dukan munafukai masu zunubi ne. Yahaya mai zunubi ne; saboda haka, Yahaya munafuki ne. Duk wanda ya san ka’idojin nazarin tunani ya san cewa wannan tsarin tunani ba mai inganci ba ne. Idan za mu sauya zargin kawai daga “ikklisiya cike take da munafukai” zuwa “ikklisiya cike take da masu zunubi,” za mu yi gaggawar amincewa da laifinmu. Ikklisiya ita ce kadai kungiyar da na sani wadda dole mutum ya amince cewa shi mai zunubi ne kafin a karbe shi a matsayin memba. Ikklisiya cike take da masu zunubi saboda ikklisiya ita ce wurin da masu zunubi waɗanda suka furta zunubansu suke zuwa don neman fansa daga zunubansu. Don haka a wannan ma’anar, kasancewar ikklisiya cike take da masu zunubi kawai ba ya ba da hujjar yanke hukuncin cewa ikklisiya cike take da munafukai. Bugu da ƙari, dukan munafunci zunubi ne, amma ba dukan zunubi ne zunubin munafunci ba.
Sa’ad da muke duba matsalar munafunci a zamanin Sabon Alkawari, za mu ga ta fi bayyana a rayuwar wadanda suke gani kansu a matsayin mafi adalci. Farisiyawa rukunin mutane ne waɗanda bisa ga ma’anar sunansu suka ɗauki kansu a matsayin waɗanda aka ware daga zunubi na yau da kullum na talakawa. Sun fara da kyau, suna neman rayuwar sadaukarwa ga ibada da kuma miƙa wuya ga dokar Allah. Duk da haka, sa’ad da halayensu suka kasa kaiwa ga matakin manufofinsu, sai suka fara nuna riya. Sun yi riya cewa su masu adalci ne fiye da yadda suke. Sun nuna sura ta adalci a waje, wanda kawai ya kasance abin ɓoye mummunar lalacewa a rayuwarsu.
Duk da cewa ikklisiya ba cike take da munafukai ba, babu musun cewa munafunci zunubi ne wanda ba a taƙaita shi ga Farisiyawa Sabon Alkawari kawai ba. Zunubi ne wanda dole ne Kiristoci su yi kokawa da shi. An kafa wa ikklisiya babban ma’auni na ruhaniya da halin adalci. Sau da yawa muna jin kunya saboda gazawarmu na kaiwa ga waɗannan manyan manufofin kuma muna karkata ga yin riya cewa mun kai wani babban matsayi na adalci fiye da wanda muka kai a zahiri. Sa’ad da muke yin hakan, muna sanya abin rufe fuska na munafuki kuma muna fuskantar shari’ar Allah saboda wannan takamaiman zunubin. Sa’ad da muka tsinci kanmu a lulluɓe cikin irin wannan riya, ya kamata ƙararrawa ta tashi a tunaninmu cewa muna buƙatar mu gaggauta komawa ga giciye da kuma ga Almasihu don mu fahimci inda adalcinmu na gaskiya yake. Dole ne mu samu a cikin Almasihu, ba abin rufe fuska da yake ɓoye fuskarmu ba, amma cikakken rumbun tufafi, wanda shi ne adalcinsa. Hakika, ƙarƙashin sifar adalcin Almasihu ne kawai, wanda aka karɓa ta wurin bangaskiya, kowannenmu zai iya samun begen tsayuwa a gaban Allah mai tsarki. Sanya tufafin Almasihu cikin bangaskiya ba aikin munafunci ba ne. Aiki ne na fansa.
An fara wallafa wannan talifi ne a shafin Blog na Ministirin Ligonier. [Blog ɗin Ministirin Ligonier]


