18/08/2026
Ingantaccen dalilin kwarewa shi ne neman nasara domin manufar ɗaukaka Allah. Wannan shi ne babban dalilin da aka halicce mu dominsa, wato mu ba da shaida ga ɗaukakarsa. Abin da ba ya nuna daukakar Allah shi ne mutum ya saba da yin abin a matsakaici, ko ya gamsu da yadda yake ba tare da kokarin ingantawa ba.








