Magance Laifin Zubar da Ciki

02/07/2026

Shin Allah Yana Karɓar Ibada Daga Dukkan Addinai?

09/07/2026

Magance Laifin Zubar da Ciki

02/07/2026

Shin Allah Yana Karɓar Ibada Daga Dukkan Addinai?

09/07/2026

Matsayin Bege a Rayuwar Kirista

Uku daga cikin manyan halayen kirki na Kiristanci—bangaskiya, bege, da ƙauna—dukkansu suna da muhimmanci. Kamar yadda ƙauna take da muhimmanci (1 Kor. 13:13), mun sani cewa bangaskiya ma ba marar muhimmanci ba ce. Mun kasance muna nazari sosai a kan mahimmancin bangaskiya, kuma muna fahimtar muhimmancin ƙauna, amma sau da yawa ana yin watsi da wannan abu na uku cikin wadannan halaye kirki guda uku, wato bege, a cikin rayuwar Kirista.

Idan akwai wata kalma a Romawa 5 da za mu iya fahimtarta a kuskure sosai, ita ce bege. Akwai wani kashi na shakka koyaushe da ke dusar da fahimtarmu game da yadda Bulus ya yi amfani da kalmar. Sa’ad da muke amfani da kalmar bege, yawanci muna amfani da ita ne don siffanta wani buri ko sha’awa na cewa wani abu zai faru, wato abin da ba mu da tabbas ko zai faru a zahiri. Ba haka kalmar take aiki ba a cikin Sabon Alkawari. Lokacin da Ruhu Mai Tsarki ya sabunta mu, ana sake haifarmu zuwa ga bege wanda ya zama tushen kwarin gwiwarmu wajen gudanar da rayuwar Kirista. Bambancin kawai tsakanin bege da bangaskiya shi ne cewa bangaskiya tana duba abin da ya riga ya faru, mu kuma dogara gare shi. Shi kuwa bege, bangaskiya ce kawai da ke duban gaba.

Misalin da aka yi amfani da shi a cikin Sabon Alkawari bayana yanayin bege shi ne abin da yake rike jirgi kada ya motsa. An gaya mana cewa, bege ne yake rike zuciyar mutum ta tsaya da karfi. Sau da yawa muna samun wannan hoton na teku a cikin Sabon Alkawari. Ana kwatanta marasa natsuwa da jiragen ruwa marasa abin rikewa, waɗanda kowace iskar koyarwa take karkata su gaba da baya. Irin waɗannan mutane Suna cike da sauyin ra’ayi da rashin tabbas da jujjuyawa, amma begen da Ruhu Mai Tsarki ya dasa a cikin zuciya ba haka yake ba. Wannan bege yana ba da tushe da kwanciyar hankali da tabbaci. Bege shi ne abin da yake rike mu kada a yi ta kada mu nan da can. Shi ne bege cewa tabbas Allah zai cika kowane abu guda ɗaya a nan gaba wanda ya ce zai aikata.

’Ya’yan barata shi ne irin wannan bege. Barata, a wata ma’ana, ita ce biyan farko duk abin da Allah ya yi mana alkawari a cikin aikinsa na fansa. Ruhu Mai Tsarki ne yake halitta bege a cikinmu. A wani waje, Bulus zai yi magana game da baiwar da Allah ya yi mana na “jingina” ko kuma biyan farko na Ruhu Mai Tsarki, wanda yake ba mu cikakken tabbaci game da nan gaba. Bege ba wai yin dogon numfashi ba ne da fatan cewa abubuwa za su daidaita. Tabbaci ne cewa Allah zai aikata abin da ya ce zai aikata.


An wallafa wannan talifi ne asali a dandalin Ministirin Ligonier Blog. [Blog ɗin Ministirin Ligonier]

R.C. Sproul

R.C. Sproul

Dr. R. C. Sproul shi ne ya kafa Ministirin Ligonier, shi ne kuma mai bishara da koyarwa na farko a masujadar Saint Andrew’s da ke a Sanford, Fla., Shugaba na farko na Reformation Bible College, kuma Babban darekta na mujallar Tabletalk. Har yau, ana yaɗa shirin sa na Renewing The mind (sabonta tunani) a dubban tashoshin radiyo a kewayen duniya, haka kuma ana iya sauraro a yanar gizo. Ya wallafa litattafai fiye da dubu, sun haɗa da, The Holiness of God (TSarkin Allah), Chosen by God (zaɓin Allah), da kuma Everyone’s a Theologian (Kowa Dalibin Tauhidi ne). Ya zama sananne a kewayen duniya domin kalaman sa na kishin kare Littafi Mai Tsarki a matsayin babu kuskure a ciki, da kuma buƙatar mutanen Allah su tsaya daram bisa amincin su a kan Kalmar Sa (Allah).