Matsayin Bege a Rayuwar Kirista

07/07/2026

Kuduri don Rayuwar Kirista

14/07/2026

Matsayin Bege a Rayuwar Kirista

07/07/2026

Kuduri don Rayuwar Kirista

14/07/2026

Shin Allah Yana Karɓar Ibada Daga Dukkan Addinai?

A duniyar yau, ya zama ruwan dare ga mutane masu gaskata da Allah su tabbatar da cewa Allah yana karɓar ibadar dukkan addinai matukar mai yin ibadar yana da kyakkyawar niyya. Duk da haka, babu wata shaida a cikin Littafi Mai Tsarki da ke goyon bayan wannan ra’ayi. A gaskiya ma, tun daga Farawa har zuwa Ruya ta Yohanna, Nassi yana bayyana akasin haka sosai.

Ana iya ganin wannan a fili a cikin dokar farko ta Dokoki Goma: “Kada ka kasance da waɗansu alloli sai ni” (Fit. 20:2). Tsohuwar duniyar Gabas ta Tsakiya inda Isra’ila ta rayu tana cike da kowane irin addinai da “alloli.” Allah ya yi watsi da waɗannan sauran addinan. Me ya sa? Domin “alloli” na waɗannan sauran addinan a gaskiya aljanu ne, kuma bautar waɗannan aljanun abin ƙyama ce (Fir. 17:7; Maim. 32:16–17). Manzo Bulus ya koyar da hakan a cikin Sabon Alkawari (1 Kor. 10:20).

A lokacin gwajinsa, Yesu ya ambaci Maimaitawar Shari’a 6:13 ga Shaiɗan, yana mai cewa, “Ubangiji Allahnka ne za ka yi wa sujada, shi kaɗai kuma za ka bauta wa” (Mat. 4:10). Wannan shi ne keɓantaccen ra’ayin nan na addini. A cikin fitowa a jiki, Maganar nan wadda take tare da Allah, wadda kuma Allah ce, ta zama jiki, ta kuma zauna a tsakaninmu (Yohanna 1:1, 14). Yanzu Shi ne Mai Shiga Tsakani guda ɗaya tsakanin Allah da mutane (1 Tim. 2:5). Babu wani daban.

Idan da Allah ya karɓi ibadar dukkan addinai, da babu buƙatar zama jiki, mutuwa, da kuma tashin Almasihu daga matattu.

Yesu da kansa ya bayyana keɓancewar addinin Kiristanci a fili sa’ad da ya ce: “Ni ne hanya, da gaskiya, da kuma rai. Babu mai zuwa wurin Uba sai ta wurina” (Yohanna 14:6). “Babu kowa” yana nufin babu kowa. Wannan ya sa Bitrus, sa’ad da yake cike da Ruhu Mai Tsarki, ya yi shelar abin da ke biyowa game da Yesu: “Babu kuwa ceto a wurin wani, gama babu wani suna a ƙarƙashin Sama da aka bayar a tsakanin mutane, wanda lalle za mu cetu ta cikinsa” (Ayyukan Manzanni 4:12). Ga waɗanda ke neman ceto, babu wani daban.

Idan da Allah yana karbin ibadar dukkan addinai, da babu buƙatar shigowar Almasihu cikin jiki, mutuwa, da kuma tashin Almasihu daga matattu saboda akwai addinai da dama da suka wanzu tun a ƙarni na farko. Da Allah yana karbar ibadar dukkan addinai, da babu kuma buƙatar Babban Umurni da kuma bisharar ga al’ummai. Idan Allah ya karɓi ibadar dukkan addinai, bisharar da Yesu ya yi umurni da ita ɓata lokaci ne. Allah ba ya karɓar kowane addini in ban da wanda ya tanada ta wurin alherinsa. Ba ya karɓar addinan da suke musanya bautar halitta maimakon bautar Mahalicci. Allah ba ya karɓar ibadar ƙarya. Sai dai, Allah yana karɓar masu ibada na kowane addini sa’ad da suka tuba daga waɗancan addinai suka kuma dogara ga Almasihu.


An fara buga wannan labarin a shafin yanar gizon Ministirin Ligonier Blog. [Blog ɗin Ministirin Ligonier]

Ministirin Ligonier

Ministirin Ligonier

Mu ne zumuntar koyarwa ta Dr. R.C. Sproul. Mun wanzu don yin shelar, koyarwa, da kuma kāre tsarkin Allah cikin dukan cikarsa ga mutane da yawa gwargwadon iko. Manufarmu, sha'awarmu, da dalilinmu shi ne taimaka wa mutane su yi girma cikin sanin Allah da tsarkinsa.