06/08/2026

Menene Alkawarin Ayyuka?

Muna kiran alkawari da Allah ya yi da Adamu Alkawarin Ayyuka domin biyayyar mutum ita ce hanyar da za a sami albaarkar alkawarin. Idan Adamu ya yi biyayya ga Allah ta wurin cika umurinsa – ya hayayyafa, ya mallaki duniya yadda Allah ya umarta, kuma ya guji cin daga itacen da aka hana – da ya sami rai na har abada. Haka kuma, zuriyarsa ma da sun amfana da wannan albarka. (Far. 1:28; 2:15–17).
16/07/2026

Wane Alkawari Yesu Ya Bayar Kafin Hawansa Sama?

Alkawari na ƙarshe da Yesu ya ba manzanninsa kafin hawansa zuwa Sama shi ne alkawarin cewa Ruhu Mai Tsarki zai sauko musu don ya ba su ikon kai bishara har iyakar duniya (Ayyukan Manzanni 1:8). Luka ya rubuta cikar wannan alkawari tun daga Ayyukan Manzanni 2, wanda yake ba mu labarin yadda Ruhu ya sauko wa Ikkilisiya a ranar Fentikos.
09/07/2026

Shin Allah Yana Karɓar Ibada Daga Dukkan Addinai?

A duniyar yau, ya zama ruwan dare ga mutane masu gaskata da Allah su tabbatar da cewa Allah yana karɓar ibadar dukkan addinai matukar mai yin ibadar yana da kyakkyawar niyya. Duk da haka, babu wata shaida a cikin Littafi Mai Tsarki da ke goyon bayan wannan ra'ayi. A gaskiya ma, tun daga Farawa har zuwa Ruya ta Yohanna, Nassi yana bayyana akasin haka sosai.
25/06/2026

Shin Mutum a asali nagari ne ko kuwa gaba daya mai zunubi ne?

A dabi'ance, 'yan-adam "'ya'yan fushi" ne (Afis. 2:3). Wannan shi ne ma'anar tauhidi a bayan kalmar nan lalacewar dabi'a gaba daya—wato harafin T a cikin TULIP (rukunai biyar na koyarwar Calvin). Ma'ana, zunubi ya bata dukkanmu (ban da Yesu) a zuciya, tunani, jiki, da kuma rai.