
Menene Littafi Mai Tsarki ya ce game da mata Fastoci?
04/08/2026Menene Alkawarin Ayyuka?
A cikin alkawarin ayyuka, wanda wani lokaci ake kira alkawarin halitta ko alkawarin rai, Allah ya hana Adamu da Hauwa’u cin itacen sanin nagarta da mugunta (Far. 2:15–17). Cikakkiyar biyayya ga wannan alkawari za ta tabbatar da Adamu da Hauwa’u cikin rai; da za a lissafa su a matsayin masu adalci a gaban Ubangiji kuma da sun gaji rai madawwami.
Muna kiran alkawari da Allah ya yi da Adamu Alkawarin Ayyuka domin biyayyar mutum ita ce hanyar da za a sami albaarkar alkawarin. Idan Adamu ya yi biyayya ga Allah ta wurin cika umurinsa – ya hayayyafa, ya mallaki duniya yadda Allah ya umarta, kuma ya guji cin daga itacen da aka hana – da ya sami rai na har abada. Haka kuma, zuriyarsa ma da sun amfana da wannan albarka. (Far. 1:28; 2:15–17).
Kamar yadda muka sani, Adamu da Hauwa’u sun karya alkawarin ayyuka, wanda ya jefa su da dukan zuriyarsu—ban da guda ɗaya, Yesu—cikin zunubi. A cikin Adamu, mun rasa ikonmu na kiyaye alkawarin ayyuka (Rom. 3:9–20), amma hakan ba ya nufin an yi watsi da alkawarin ba. Har yanzu muna ƙarƙashin sharuɗɗansa, amma saboda rashin iyawarmu, begenmu kaɗai shi ne wani ya kiyaye shi a madadinmu (Gal. 3:10–14).
Domin sake samun Aljanna ga mutanensa, dole ne Yesu ya zama Adamu na biyu. Wato, ya zama dole ya zo cikin kamaninmu domin ya yi cikakkiyar biyayya ga Allah kuma ya yi nasara a inda Adamu ya gaza a matsayin wakilinmu. Bulus ya koyar da wannan a sarari (1 Kor. 15:45), amma wannan gaskiya tana kuma bayyana a cikin labaran jarabawar Yesu da ke cikin Bishara ta Matta, Markus da Luka.
Bayan baftismarsa, aka kai Yesu zuwa cikin hamada inda ya fuskanci wanda ya yi amfani da maciji don jarraba Adamu. An jarrabi Adamu na farko ya dogara ga hikimar kansa maimakon ga nufin Ubangiji da aka bayyana. Haka kuma an jarrabi Adamu na biyu ya yi watsi da nufin Allah—cewa zai ci nasara a kan macijin ta wurin wahala—sa’ad da Shaiɗan ya yi ƙoƙarin sa Yesu ya biya buƙatunsa a lokacin da bai dace ba ko kuma ya shiga cikin mulkinsa nan take ba tare da shan wahala ba (Mat. 4:1–11). Duk da haka, ba kamar Adamu na farko ba, Yesu ya yi nasara a kan jarrabar Shaiɗan, yana kafa harsashin shan kashin Shaiɗan na ƙarshe a kan giciye (Kol. 2:13–15).
An fara wallafa wannan talifi ne a shafin Blog na Ministirin Ligonier. [Blog ɗin Ministirin Ligonier]


