Abin da ke Motsa Kauna

23/07/2026

Abin da ke Motsa Kauna

23/07/2026

Ragwanci & Himma

Sa’ad da mutum yake tunani game da gadon da ya dade yana wanzuwa na Gyaran Furotesta na ƙarni na sha shida, akwai abubuwa da dama da ke zuwa zuciya—abubuwa kamar baratarwa ta wurin bangaskiya kaɗai, cikin Almasihu kaɗai, bisa ga Maganar Allah kaɗai, kuma domin ɗaukakarsa kaɗai. Amma akwai wani muhimmin abin tarihin Gyaran da galibi ake mancewa da shi. An adana shi cikin jimlar nan “ɗa’ar aiki ta Furotesta.” Wannan furucin ya kasance yana da alaƙa da wasu kamar “cikakken biyan yini guda don cikakken aikin yini guda.” Amma dalilin da ya sa ake kiran wannan ɗa’ar aiki ta Furotesta shi ne saboda ɗaya daga cikin abubuwan da masu Gyaran suka bayyana ko suka sake kafawa shi ne ra’ayin nan cewa dukkan halattaccen aiki (ba kawai aikin addini ko wanda ya shafi ikklisiya kadai ba) Allah ne yake tsarkake shi. A takaice, masu Gyaran sun sake dawo da fahimtar Littafin Mai Tsarki game da martaba da darajar aikin dan adam.

Domin fahimtar muhimmancin aikin ɗan adam a cikin Nassi, abin da ake buƙata kawai shi ne a yi la’akari da nassosi da dama da suke la’antar ragwanci da kasala cikin kalmomi mafi tsanani: “Mutum mai mai da hankali ga aikinsa zai sami iko, amma ragwanci zai sa mutum ya zama bawa.” (K. Mag. 12:24). “Manomin da ya cika lalaci, ya kasa nome gonakinsa a kan kari, a lokacin girbi ba zai sami kome ba.” (K. Mag. 20:4). “Yin shiri a tsanaki zai kai ka ga biyan bukatarka, idan kuwa ka cika gaggawa ba za ka sami abin da zai ishe ka ba.” (K. Mag. 21:25). “Ai, ko dā ma, sa’ad da muke a tare, mun yi muku wannan umarni, cewa duk wanda ya ƙi yin aiki, kada a ba shi abinci. Gama mun ji labari cewa waɗansunku malalata ne kawai, ba sa aikin kome, masu shisshigi ne kurum. To, irin waɗannan mutane muna yi musu umarni, muna kuma gargaɗinsu da izinin Ubangiji Yesu Almasihu, su riƙa aiki da natsuwa, suna ci da kansu.” (2 Tas. 3:10–12). Kamar yadda waɗannan nassosi suka nuna, zunubi ne mai babban sakamako ga mutumin da yake da ƙarfin jiki ya zauna ba tare da yin aiki ba. Manzo Bulus ya bayyana wannan batu dalla-dalla a cikin 1 Timoti 5:8: “Duk wanda bai kula da danginsa ba, tun ba ma iyalinsa ba, ya mūsa wa bangaskiya ke nan, ya kuma fi marar ba da gaskiya mugunta.”

Ɗa’ar aikin Furotesta ba kawai tana jaddada darajar aikin gaskiya ba ne, har ma da yin himma a cikin wannan aikin. Karin Magana 18:9 ya bayyana wannan: “Rago yana daidai da mutumin da yake lalatar da abubuwa.” A cikin dukan littafin Karin Magana, ba mutumin da yake yin aiki kawai ake yaba wa ba, sai dai wanda yake yin aiki da himma. Ma’ana, ya kamata mu sa dukan ƙoƙarinmu a cikin ayyukanmu.

Amma saboda yanayinmu na fāɗuwar ɗan adam ne ya sa wasu suke zama ragwaye kuma suke ƙin yin aiki, yayin da wasu kuma suke kasancewa masu kasala da sakaci a aikinsu. Zunubi yana sa wasu su kalli aiki cikin son kai—kawai daga ra’ayin kuɗi. Ma’ana, ba su damu sosai da hidimar da za su iya yi wa Allah ba ko kuma ɗaukakar da ta kamata a ba shi. Suna kallon aiki ne kawai a matsayin hanyar samun kuɗi da kuma abubuwa domin kansu.

Zunubi yana sa wasu su shagala sosai a cikin aikinsu har su yi watsi da iyalansu har ma da jin dāɗin rayuwarsu ta ruhaniya. Halin nan na nuna ƙwazo da son aiki fiye da kima da yake nuna halin yawancin mutane a zamaninmu yana basaja ne a matsayin himmar da Nassi ya yi kira gare ta. Amma wannan yaudarar kai ne. Ba a nufi aikinmu na himma ya yi gogayya da Allah da iyali ba.

Zunubi yana sa wasu su kasance da babban ra’ayi game da kansu (tare da raina wasu) saboda irin aikin da suke yi. Al’adunmu sun cika da ayyuka da ake dauka masu daraja da daukaka, wadanda suke yaudarar mutane su yi tunani cewa sun fi wasu daraja ko muhimmanci saboda matsayinsu. Wannan yana kaiwa ga yanke hukunci na raini game da aikin mutane, halayensu, da kuma mutuncisu, musamman wadanda ba su da irin wadannan ayyuka “masu daukaka.”

Dole ne Kiristoci su kiyaye kansu daga irin waɗannan karkatattun ra’ayoyi na aiki kuma su tuba sa’ad da aka bayyana irin waɗannan tunani a gare mu. Domin wannan dalili, kowace tattaunawa game da aiki daga ra’ayin Kirista ya kamata ta haɗa da Asabar. Farawa 2:3 ta ce, “Domin haka Allah ya sa wa kwana na bakwai albarka, ya tsarkake shi, don a cikinsa Allah ya huta daga dukan aikin da ya yi na halitta.” Yayin da muke yin bimbini da kuma ɗaukaka Mahaliccinmu a cikin aikinmu, dole ne mu yi bimbini kuma mu ɗaukaka shi a kiyaye Asabar kuma. A can ne ake sanya aikinmu a cikin madaidaicin ra’ayi. Marubucin Ibraniyawa ya bayyana cewa Kristi ne matuƙar hutunmu kuma Asabar (Ibran. 3:7–4:10). Sa’ad da muka dakata daga ayyukanmu don mu yi bimbini a kansa da kuma aikinsa a madadinmu, godiyarmu tana sake ruruwa kuma ra’ayoyinmu game da rayuwa da aiki suna kasancewa a kan mayar da hankali ga Kristi.

To, mene ne wasu sakamakon dabi’ar aiki ta Protestant? Kasala, rashin abin yi, da raggonci nuna tawayen ɗan adam ne ga Mahaliccinmu da kuma tozarta ɗaukakarsa.

Idan muka bar tunaninmu game da aiki duniya ta siffanta su, za mu kasance masu sauƙin karkata zuwa ga mayar da kiranmu ya zama gunki. Yin aiki kawai bai isa ba, amma dole ne mu yi aiki da kwazo, ta yadda ba za mu ba wa raggonci sarari ba, kuma ba za mu zama masu neman faranta wa mutane rai kawai ba. Ya kamata mu saka wa zuciyarmu kakkausan harshen Nassosi game da raggonci da kasala. A cikin aikinmu da kuma dukan fannonin rayuwarmu, ya zama dole mu yi rayuwa don ɗaukakar Allah.


An fara wallafa wannan makala ne a shafin yanar gizo na Ma’aikatar Ministirin Ligonier Blog. [Blog ɗin Ministirin Ligonier]

Ken Jones

Ken Jones

Rev. Ken Jones shi ne faston Glendale Missionary Baptist Church a Miami. Shi ne mai ba da gudunmawa ga littattafai da dama, ciki har da Experiencing the Truth: Bringing the Reformation to the African-American Church. Rev. Jones abokin gabatarwa ne na shirin podcast mai suna Saints and Sinners Unplugged.