Menene Ma’anar Kasancewa “Cikin Kiristi”?

21/07/2026

Ragwanci & Himma

28/07/2026

Menene Ma’anar Kasancewa “Cikin Kiristi”?

21/07/2026

Ragwanci & Himma

28/07/2026

Abin da ke Motsa Kauna

A cikin sanannen littafinsa na ƙarni na ashirin, The Screwtape Letters, C.S. Lewis ya kwatanta yadda wani aljani mai sunaScrewtape yana rubuta wasika ga ɗan ɗan’uwansa Wormwood, yana gaya masa yagano asirin dalilin da ya sa Allah yake ƙaunar mutane. Ya rubuta:

Gaskiyar ita ce, saboda rashin kula na fadi cewa Makiyi (Allah) da gaske yana kaunar mutane. Amma hakan ba zai yiwu ba…Duk maganarsa game da kauna dole tana boye wani abu ne daban. Lallai yana da wani dalili na musamman da ya sa ya halicci mutane kuma yake damuwa da su sossai. Dalilin da ya sa muke magana kamar yana kaunar su da gaske shi ne saboda mun kasa gano ainihin dalilinsa. Mene ne yake son samu daga gare su? Wannan ita ce tambayar da ba ta da amsa. A nan ne babban aikin yake. Mun san cewa ba zai yiwu ya kaunace su da gaske ba; babu wanda zai iya yin irin wannan kauna; ba ta da ma’ana a gare mu. Da ace za mu iya gano abin da yake nufi da gaske!

Muna yi wa aljanun fatan alheri a ƙoƙarinsu na neman amsar. Mu da muke jama’ar Allah ne, babu buƙatar irin wannan binciken. Mun yi imani cewa Allah yana ƙaunarmu da gaske. Allah ƙauna ne (1 Yohanna 4:16). Saboda haka, ɗabi’arsa ce ya nuna ƙauna. Ya ƙaunace mu a lokacin rashin laifinmu kafin fāɗuwar ɗan adam, kuma ya ci gaba da ƙaunarmu a cikin halinmu na fāɗuwar. Don haka, Yesu ya iya cewa, “Ku ƙaunaci maƙiyanku . . . domin ku zama ‘ya’yan Ubanku wanda yake cikin Sama” (Mat. 5:44–45).

Ƙaunar Allah a gare mu ta bayyana sosai a lokacin da ya kawo mana ceto ta wurin giciye: “Gama Allah ya ƙaunaci duniya sosai har ya ba da wanda yake Ɗaya kuma Makaɗaicin Ɗansa domin duk wanda ya gaskata da shi kada yă hallaka sai dai yă sami rai madawwami” (Yohanna 3:16). Wannan ƙauna ce da ba ta siffantuwa, wadda kuma take cika mu da mamaki ƙwarai. Kamar yadda Charles Wesley ya bayyana:

Daga ina wannan yalwar ƙauna ta zo mini? Tambayi Mataimakina na sama! Dubi dalilin a fuskar Yesu, Yanzu a gaban kursiyin alheri.

A can Mai Ceto yana tsaye domin ni; Yana nuna raunukansa yana miƙa hannuwansa, Allah ƙauna ne; na sani, ina ji; Yesu yana da rai, kuma har yanzu yana ƙaunata.

Abin da Littati Mai Tsarki ya nuna mana game da kaunar Allah gare mu ne ya sa muka fara kaunarsa. Ina nufin, idan aka yi la’akari da waɗannan gaskiya masu ban mamaki, ta yaya ba za mu ƙaunace Shi ba? Hadayar Ɗan Allah kansa a kan gicciye ita ce murhun da muke dumama zukatanmu masu sanyi zuwa ga Allah. Ga mu da muke masu wa’azi, babu wata hadaya a cikin hidima da ta yi girman da ba za a iya bayarwa ba idan aka yi la’akari da hadayar da Allah ya yi domin mu. Ruhu Mai Tsarki yana amfani da wannan gaskiya domin ya ci gaba da kunna wutar kaunar Allah a cikin zukatarmu. Hakan yana sa himmarmu ga Allah ta ci gaba da karuwa kuma ba a iya kashewa. Shahararriyar waƙar yabon nan ta Isaac Watts ta bayyana wannan gaskiya sosai a cikin baiti na ƙarshe:

Ko da dukkan daular halitta tawa ce,

Wannan zai zama hadaya da ta yi ƙanƙanta da yawa;

Ƙauna mai ban mamaki, ta Allah,

Tana bukatar raina, da rayuwata, da dukkan abin da nake da shi.

Duk da haka, ba wai kawai muna mayar wa Allah da ƙauna ba ne, amma kuma muna karkatar da ƙaunarmu ga waɗanda Allah ya ƙauna, waɗanda kuma yake ci gaba da ƙauna. Muna so mu zama hanyoyin da ƙaunar Allah za ta kai ga waɗanda aka nufa dominsu. Za mu ƙetare ƙasashe da tekuna ba kawai don mu gargaɗi rayukan da suka ɓace game da fushin Allah ba, har ma don mu roƙe su da gaske su amsa wa ƙaunar da Allah yake nuna musu a cikin Kiristi Yesu. Hakika, idan mun san wannan ƙauna, ya zama dole mu yi hakan.

Wannan shi ne abin da Bulus yake nufi sa’ad da ya ce:

Ƙaunar Kiristi a gare mu, ita take mallakarmu, saboda haka mun tabbata, da yake wani ya mutu saboda dukan mutane. . . . Saboda haka, mu jakadu ne na Kiristi, sai ka ce Allah kansa yake magana ta wurinmu. Muna roƙonku a madadin Kiristi. Ku sulhuntu da Allah. (2 Kor. 5:14, 20)

Idan wannan ƙauna ba ita ce take dalilinka a cikin ayyukanka na bishara ba, to lallai kana aiki ne ƙasa da iyawarka sosai.

Yayin da muke ƙaunar Allah a cikin hasken ƙaunarsa gare mu, muna kuma samun kanmu muna ƙaunar amaryarsa—wato ikklisiya. Mutanen Allah, waɗanda aka saya da jininsa, suna zama ababen daraja gare mu ƙwarai. Tare da Bulus, muna gaya musu:

Ina addu’a domin Kiristi yă zauna a cikin zukatanku ta wurin bangaskiya. Ina kuma addu’a saboda ku da kuka kahu sosai cikin ƙauna, don ku sami iko, tare da dukan tsarkaka, ku fahimci fāɗi, tsawo, da kuma zurfin ƙaunar Kiristi take. Ku kuma san wannan ƙauna wadda ta fi gaban sani, domin a cika ku da dukan cikar Allah. (Afis. 3:17–19)

Domin wannan manufa, muna fadi-tashi muna kuma fafitika da dukkan iko da ƙarfin da Allah yake ba mu.

Yayin da aljannun da Lewis ya kwatanta suke ta kokarin gano ainihin dalilin da ya sa Allah yake cewa yana kaunar mu, muna samun cewa wannan ƙauna tana motsa mu ba kawai mu ƙaunaci Allah ba, har ma mu ƙaunaci mutanen da Ya halitta kuma Ya fansa. Muna gaya wa kanmu (a cikin kalmomin John Kent):

A kan irin wannan ƙauna, ya raina, ka ci gaba da tunani, ƙauna mai girma, mai yalwa da kuma kyauta; Ka ce, yayin da ka zurfafa cikin mamaki mai tsarki, Don me, ya Ubangiji, irin wannan ƙauna gare ni? Haleluya! Alheri zai yi mulki har abada.


Asali, an buga wannan talifi ne a shafin yanar gizon ma’aikatar wallafa littattafai ta Ligonier. [Blog ɗin Ministirin Ligonier]

Conrad Mbewe

Conrad Mbewe

Rev. Conrad Mbewe fasto ne a Kabwata Baptist Church da ke Lusaka, Zambia. Shi ne kuma marubucin littafin nan Foundations for the Flock: Truths about the Church for All the Saints.