Wane Alkawari Yesu Ya Bayar Kafin Hawansa Sama?

16/07/2026

Abin da ke Motsa Kauna

23/07/2026

Wane Alkawari Yesu Ya Bayar Kafin Hawansa Sama?

16/07/2026

Abin da ke Motsa Kauna

23/07/2026

Menene Ma’anar Kasancewa “Cikin Kiristi”?

Yabo ya tabbata ga Allah Uban Ubangijinmu Yesu Kiristi, wanda ya kawo mana kowace albarka ta Ruhu basamaniya. Gama ya zaɓe mu a cikin Kiristi tun dā can, kafin ma a halicci duniya don mu zama masu tsarki da kuma marasa aibi a gabansa. A cikin ƙauna, ya ƙaddara mu zama ’ya’yansa na riƙo ta wurin Kiristi Yesu, bisa ga nufinsa na alheri. Ya yi haka don mu yabi Allah saboda alherin da ya yi mana wanda ya yi mana kyautarsa a cikin Ƙaunataccen. A cikinsa muka sami fansa ta wurin jininsa, wato, yafewar zunubanmu. Kiristi ya yi wannan saboda yawan alherin Allah wanda ya ba mu babu iyaka tare da dukan hikima da fahimta. Allah ya yi abin da ya nufa, ya kuma sanar mana shirin asirin da ya riga ya shirya yă cika ta wurin Kiristi. Nufinsa ke nan, idan lokaci ya cika, yă harhaɗa dukan abubuwa a ƙarƙashin ikon Kiristi, wato, dukan abubuwan da suke sama da abubuwan da suke ƙasa.

A cikinsa ne kuma aka zaɓe mu mu sami gādo daga Allah, an kuwa ƙaddara mu ga haka bisa ga nufin wannan da yake zartar da dukan abubuwa yadda ya yi nufi yă yi. Manufar Allah ita ce cewa mu da muka fara sa bege a cikin Kiristi, mu yi zaman yabon ɗaukakar Allah. An kuma haɗa ku a cikin Kiristi lokacin da kuka ji saƙon nan na gaskiya, wanda yake labari mai daɗi na cetonku. Da kuka ba da gaskiya, sai aka yi muku alamar shaida a cikinsa da Ruhu Mai Tsarki. Ruhu Mai Tsarkin nan shi ne tabbacin da Allah ya yi na cewa zai ba mu kome da ya yi alkawari, har zuwa lokacin da za mu mallaki gādonmu gaba ɗaya. Wannan kuwa domin yabon ɗaukakarsa ne. (Afis. 1:3–14)

Sa’ad da mutane suka tambaye ku game da bangaskiyar ku, yaya kuke bayana kanku? Shin za ku ce “Ni dan Presbyterian Church ne” ko kuwa “dan Baptist Church ne”? Ko watakila, “Ni dan Episcopal ne”? Ko kuwa kawai ku ce, “Ni Kirista ne”?

Wataƙila mafi yawanmu ba mu taɓa yin tunanin cewa idan za mu iya tambayar masu bi daga zamanin Sabon Alkawari su bayyana kansu, wataƙila ba za su taɓa amsawa su ce, “Mu Kiristoci ne” ba. A gaskiya, kalmar nan Kirista ta bayyana sau uku kawai a cikin Sabon Alkawari. An fara kiran almajiran “Kiristoci” a Antakiya (Ayyukan Manzanni 11:26). Daga baya, Sarki Agrippa ya nuna kamar ya tofar da kalmar sa’ad da ya tambayi Manzo Bulus, “Cikin ƙanƙanin lokaci kana so ka lallashe ni in zama Kirista?” (Ayyukan Manzanni 26:28). Kuma daga baya, a wasiƙarsa ta farko, Siman Bitrus ya yi magana game da wahalar wani a matsayin “Kirista” (1 Bitrus 4:16).

A cikin waɗannan yanayi guda uku, Kirista wataƙila kalmar wulaƙanci ce, har ma da “kalaman ƙiyayya” waɗanda magabtan bishara suka ƙirƙira, kamar yadda kalmar Puritan take a ƙarni na sha bakwai. Yana iya kasancewa an tofar da ita ne kamar yadda ake yi da kalmar fundamentalist a yau. Waɗannan “kalmomin ƙiyayya” ne. Idan har ta haka ne kalmar Kirista ta fara shiga amfani, ba abin mamaki ba ne da yake a cikin Ayyukan Manzanni, Luka ya zaɓi yin amfani da kalmar “almajiri” (misali, a Ayyukan Manzanni 6:1; akwai misalai sama da gommai biyu) ko kuma lokaci-lokaci yakan bayyana masu bi a matsayin masu bin “Hanyar” (Ayyukan Manzanni 9:2; 22:4; 24:14), tunda sun bi Wanda ya ce, “Ni ne hanya” (Yuhanna 14:6).

Amma idan za ka tambayi Bulus, “Yaya kake tunani game da kanka?” wataƙila amsarsa ba za ta kasance ko guda cikin waɗanda aka ambata a sama ba, sai dai ya ce, “Ni mutum ne cikin Almasihu.”

Ina tunawa, sa’ad da nake matashi, na karanta 2 Korinthiyawa 12:1–10—wurin da Bulus ya yi magana game da wahayi na musamman da ya karɓa da kuma ƙaya a cikin jiki wadda ta hana shi yin girman kai. Sa’ad da yake gabatar da wannan nassi, ya ce ya san “wani mutum cikin Almasihu” wanda ya sami wahayi na musamman na al’ajabi da alherin Allah, masu ban mamaki sosai har ya ji cewa ba zai dace ba ya bayyana su ga wasu. Na tuna ina mamaki, “Wane ne wannan ‘mutum cikin Almasihu’ wanda ba a ambaci sunansa ba da Bulus yake magana a kansa?” Wataƙila ni mai jinkirin fahimta ne, amma a hankali na gano amsar: Bulus yana magana ne game da kansa! Wannan ita ce hanya ta asali da yake bayyana kansa domin ita ce hanya ta asali da yake tunani game da kansa. Shi “mutum ne cikin Almasihu.”

Rike waɗannan kalmomi guda biyu “cikin Almasihu” da makamantansu (misali, “cikin sa”) a zuciyarka. Sannan ka yi saurin dubawa cikin shafuka kusan sittin na Littafi Mai Tsarki waɗanda suka ƙunshi wasiƙun Bulus guda goma sha uku. Za ka tarar da kalmar nan “cikin Almasihu” ko makamancinta sama da sau tamanin. Kalmomi makamantansu “cikin Ubangiji” (ko wani lokacin “cikin Ubangiji Yesu”) sun kusan ninka wannan yawa.

Idan ba ka taɓa lura da wannan ba, wataƙila za ka yi mamakin yadda Bulus yake yawan amfani da waɗannan kalmomi, kuma za ka yi mamakin yadda ba ka taɓa ba su muhimmiyar kulawa ba. Kuma duk da haka yana yiwuwa mutum ya kasance yana karanta wasiƙun Bulus na shekaru masu yawa, har ma da shekaru da dama, ba tare da ya lura da muhimmancin wannan ɗan ƙaramin furci ba, wanda a fili yake cewa shi ne hanyarsa ta asali ta bayyana abin da ake nufi da zama Kirista.

Waɗannan kalmomi guda biyu, wato “cikin” da “Almasihu”, su ne babban batu da wadannan shafuka suke magana a akai. Kafin ƙarshen littafin nan, za a iya yafe maka idan ka yi tunanin cewa wannan shi ne bayani mafi tsawo na kalmomi guda biyu da ka taɓa karantawa! Duk da haka, waɗannan shafuka za su ɗan taɓa saman wannan koyarwa mai zurfi da ban al’ajabi ne kawai. Amma ina fata za su ƙarfafa ka ka gani, ta mahanga daban-daban na nassosi, abin da ake nufi da kasancewa “cikin Almasihu.” Idan kai na sa ne, to lallai wannan shi ne ainihin wanda kake, a kowace rana ta rayuwarka—namiji ko mace wanda yake “cikin Almasihu.”

Wani masanin Sabon Alkawari ya nuna cewa a cikin fim ɗin nan The Godfather, ba a taɓa amfani da kalmar Mafia ba, amma duk da haka ita ce ginshiƙin tunanin dukan fim ɗin. Haka ma, ko da ba a yi amfani da wannan takamaiman furcin na “cikin Almasihu” ba, abin da ake nufi da shi tushe ne ga duk abin da Manzo Bulus yake faɗa game da yin rayuwar Kirista. Kuma fiye da haka, shi ne kuma maganin matsaloli da dama da suke damun ɗaiɗaikun masu bi ko dukan ikilisiya.

Sabon Alkawari ba ya taɓa bayyana ma’anar “cikin Almasihu” ba. Hanya mafi kyau ta fahimtar muhimmancinsa ita ce yin tunani a kan nassosi daban-daban da suke bayyana abin da yake tattare da shi. A nan, babban aikinmu shi ne mu gabatar wa kanmu muhimmancin kasancewa “cikin Almasihu.” Ɗaya daga cikin mafi kyawun hanyoyin yin hakan ita ce ta yin tunani a kan bayyanar wannan furci a babi na farko na wasiƙar Bulus zuwa ga Afisawa.


Constantine R. Campbell, Paul and Union with Christ: An Exegetical and Theological Study (Zondervan, 2012), 24n4. ↩


Asali, an buga wannan talifi ne a shafin yanar gizon ma’aikatar wallafa littattafai ta Ligonier. [Blog ɗin Ministirin Ligonier]

Sinclair B. Ferguson

Sinclair B. Ferguson

Dr. Sinclair B. Ferguson babba kuma ƙwararren farfesa ne na Systematic Theology a Reformed Theological Seminary. A da ya yi aiki a matsayin babban fasto na First Presbyterian Church a Columbia, S.C. Ya wallafa litattafai da dama, sun haɗa da In The Year Of Our Lord.