
Shin Yesu Misalinmu Ne?
17/09/2026Menene Bautar Gumaka?
Sa’ad da mutane suka ji kalmar bautar gumaka, suna tunanin abubuwa daban-daban. Wasu suna tunanin tsofaffin al’adu inda masu bauta suke rusunawa a gaban sassaƙaƙƙun gumaka. Wasu kuma suna tunanin yadda magoya baya suke “girmama” fitattun jarumansu na wasan kwaikwayo, ‘yan wasa, ko mawaƙa. Har yanzu wasu na iya amfani da kalmar a matsayin misali na shagaltuwa da wani abu.
To, menene bauta wa gumaka? Ainihi, bauta wa gumaka shi ne bauta wa duk wani abu da aka halitta maimakon Mahalicci.
Me ya sa Allah yake damuwa da wannan sosai? To, abu ne mai sauƙi: Allah yana damuwa da bautar gumaka domin Allah yana damuwa da sujada.
Wani lokaci wannan ra’ayi yana damun masu karatu na zamani domin suna iya kallon Allah a matsayin mai matukar son kansa, wanda ya shaku da bautar da ake yi masa ta hanyar da ba ta dace ba. Wannan zai zama gaskiya idan da Allah halittaccen abu ne maimakon ya zama Mahalicci. Amma a matsayinmu na mutane, Allah ya halicce mu domin mu bauta masa. Wannan daidai ne. Abu ne mai kyau domin Allah shi kadai ne ya cancanci bauta. Amma idan muka juya wannan yanayi, har ya zamanto Allah bai daukaka ko kare daukakarsa da darajarsa ba, to ba ya aiki a matsayin Allah ke nan. Sau da yawa, mutane suna tunanin Allah kamar shi mutum ne (bangaren halitta) yayin da a lokaci guda suke tunanin halitta kamar ita ce Allah (wadda ta cancanci bauta). Ta haka, daukaka halitta da kaskantar da Mahalicci duka biyun ba su dace ba. Wannan bautar gumaka ce.
Manzo Bulus ya kwatanta bautar gumaka a matsayin musaya. Maimakon a ba Allah ɗaukaka, sai aka musanya ta da ɗaukakar siffofin abubuwan da aka halitta. Domin yin haka, mai bautar ya “musanya gaskiyar Allah da ƙarya, ya kuma bauta wa abin da aka halitta, ya yi masa hidima maimakon Mahalicci, wanda shi ne abin albarka har abada! Amin.” (Rom. 1:25).
Musayar ɗaukakar Allah da gumaka yana kama da auna darajar Allah ne a kan ma’auni. Maimakon ganin ɗaukakarsa (nauyinsa, darajarsa, da jigon kasancewarsa marar iyaka), mai bautar ya ƙaddara cewa Shi ba shi da daraja kamar wani abu da aka halitta (idan aka kwatanta, wani abu marar nauyi kuma fanko). Wannan musayar ita ce ƙololuwar wauta. Ka yi tunanin mutum yana ganin giwa da gashin tsuntsu ana auna su a kan ma’auni sai ya yanke shawarar cewa gashin tsuntsun ya fi nauyi. Babu shakka, irin wannan mutumin ya fita daga hayyacinsa na sanin gaskiya. Ta yaya kowa zai yi tunanin haka? Ta yaya za mu iya maye gurbin Allah da gumaka? Sai dai ta hanyar musayar gaskiya game da Allah da ƙarya. Sa’ad da muka danne wahayin Allah na ko shi wane ne, muna yanke shawarwarin da ba su da kyau (Rom. 1:18).
Domin tsaro daga bauta wa gumaka da kuma inganta bauta ta gaskiya ga Allah, Ubangiji yana koya mana a cikin Kalmarsa:
Ni ne UBANGIJI Allahnku, wanda ya fitar da ku daga ƙasar Masar, daga gidan bauta.
Ba za ka sami waɗansu alloli ba sai ni. (Fit. 20:2–3)
Wannan sanannen nassi an sanya shi da gangan a farkon Dokoki Goma. Kada mu bar kowa ko wani abu ya ɗauki madaidaicin matsayin Allah na fifiko.
Amma mene ne muke samu akai-akai a cikin Littafi Mai Tsarki? Ko a cikin littafin Fitowa kansa, mutanen da aka fansa daga Masar sun kera allah daga zinariyarsu sannan suka bauta masa (Fit. 32). Bayan haka, Sarki Jeroboam ya ji tsoron kada ya rasa iko, ya sake maimaita wannan bautar gumaka, kuma ya ƙirƙiri nasa tsarin bautar. Suna musanya darajar Allah, sun bauta wa abin da suka ƙera da hannunsu: “Ga allolinku, ya Isra’ila, waɗanda suka fitar da ku daga ƙasar Masar” (1 Sarakuna 12:28). Waɗannan shahararrun misalai suna tsaye ne kamar fitilun gargaɗi masu haske da suke yi mana kashedi game da bautar gumaka. Allah yana ƙyamar bautar gumaka saboda Yana son ɗaukakarsa. Allah Yana son ɗaukakarsa saboda ita kyakkyawa ce.
Mutane da yawa sun lura cewa doka ta fari ita ce harsashin sauran guda tara; sabawa sauran yana nufin kauce wa Allah na gaskiya domin bauta wa gunki. Wannan yana nuna irin haɗarin da ke tattare da nau’o’in bautar gumaka daban-daban. Za mu iya tunaninta a matsayin yin sujada ga wani mutum-mutumi na zahiri, amma kuma tana iya kasancewa sha’awar wani abu da ba ka da shi wanda wani yake da shi (duba Fit. 20:17).
Sa’ad da muka zama Kiristoci, mun juyo daga gumaka don mu bauta wa Allah mai rai (1 Tas. 1:9). Amma wannan ba shi ne ƙarshen yaƙin ba. Dole ne mu ci gaba da juyowa daga gumaka (1 Kor. 10:14), muna aiki don kiyaye kanmu da wasu daga gare su (1 Yohanna 5:21).
Manzo Bulus ya ba mu misali mai dacewa kuma mai ƙalubale. Yayin da yake kewaya Atina, yana jiran abokan aikinsa na hidima su tarye shi, ya kalli wuraren. Maimakon gine-ginen su burge shi, sai fantsamar bautar gumaka ta sa shi fushi (Ayyukan Manzanni 17:16). Bulus ya kasance mai kishin ɗaukakar Allah sosai har ma ya ji haushin yadda ba a ba Allah girmamawar da ta dace da Shi ba. Sakamakon haka, ya fita ya raba bishara da kowa da ke kewaye da shi.
Wannan ƙauna ga ɗaukakar Allah kariya ce mai dacewa daga bautar gumaka. Don haka, ka yi tunani sosai a kan ƙima mafi daukaka ta Allah a kan kowa. Ka zurfafa tunani a kan amincinsa marar gushewa, ƙaunarsa marar ragi, alherinsa marar ƙarewa, adalcinsa marar karkata, nagartarsa marar lalacewa, hikimarsa marar kusakure, da kuma halinsa marar canzawa. Wane ne kamar wannan? Sa’an nan ka yi tunani game da yadda, a cikin Yesu Kristi, wannan shi ne Allah wanda ya san ka kuma yake ƙaunarka.
Za mu iya yin addu’a cewa Allah ya taimake mu, kuma mu ƙudura aniyar ba Allah girman da ya dace da Shi, mu kuma kasance cikin rashin jin daɗi da duk wani abu dabam.
An fara wallafa wannan talifi ne a shafin Blog na Ministirin Ligonier. [Blog ɗin Ministirin Ligonier]


