
Yaya Za Mu “Amfani da Baftismarmu yadda ya kamata”
15/09/2026
Menene Bautar Gumaka?
22/09/2026Shin Yesu Misalinmu Ne?
Kristi kuma ya sha wahala domin ku, ya bar muku misali, domin ku bi sawunsa. (1 Bitrus 2:21)
Ta wani fanni, amsar tana da sauki. Shin Yesu misalinmu ne? E. Yesu misalinmu ne, amma ba wai kawai misalinmu ba ne, kuma koyi da Shi ba shi ne harsashin bangaskiyarmu ba.
Aikin Fansa na Musamman na Kristi
Kafin ya rubuta cewa Yesu ya bar mana “misali, domin ku bi sawunsa,” Bitrus ya fara da’awar cewa “Kristi ya sha wahala domin ku”—wato, a wata hanya da ba ma shan wahala a madadin wasu. Lokacin da Yesu ya sha wahala a gicciye, Ya “ɗauki zunubanmu a jikinsa”; Ya warkar da raunukanmu ta hanyar raunata shi da aka yi dominmu (1 Bitrus 2:24). Mu ne waɗanda muke ɓata kamar tumaki, kuma aikinsa na musamman dominmu ya fanshe mu daga zunubinmu domin mu rayu cikin tsarki (1 Bitrus 2:25).
A cikin rayuwarsa, mutuwarsa, da tashinsa daga matattu, Yesu ya yi mana—waɗanda aka haɗa su da Shi ta wurin bangaskiya—abin da ba za mu iya yi wa kanmu ba ko kuma wa wani daban. Ba za mu iya mutuwa don fansar ’yan uwa masu zunubi daga sakamakon zunubinsu na har abada ba. Amma Yesu, a matsayinsa na Allah da kansa kuma cikakken Mutum, ya maye gurbin kansa domin masu zunubi a kan gicciye. Kristi ya sha wahala dominmu waɗanda muka gaskata da Shi.
A ƙarshen bisharoyi huɗu, Yesu yana yi mana abin da ba za mu iya yi wa kanmu ba. Manufa ta farko kuma babba ta bisharoyin ba ita ce mu yi koyi da abin da Yesu yake yi ba, amma, kamar yadda Yohanna ya rubuta a fili, mu yi imani da Yesu: “Amma an rubuta waɗannan don ku gaskata Yesu shi ne Almasihu, Ɗan Allah, kuma ta wurin gaskatawa ku sami rai da sunansa” (Yohanna 20:31).
Yin koyi da Kristi a matsayin almajiransa
Kai, bisharori suna da matukar wadata ga duk mai neman ya bi sawun. Yesu! Ainihin abin da Almasihu ya cika domin cetonmu ba abin koyi ba ne, amma duk da haka rayuwarsa ta ɗan-adam, maganganunsa, da ayyukansa suna cike da abubuwan koyi masu ban al’ajabi. Kamar mu, shi mutum ne na gaske, wanda yake neman ɗaukaka Ubansa yayin da yake rayuwa cikin jiki da jini na ɗan-adam a gaban adawa ta masu zunubi da kuma yanayin wannan duniya da ta faɗi. Yesu shi ne kafararmu ta musamman (kafarar zunubanmu) kuma misalinmu na kowa na rayuwar Kirista.
Yesu da kansa ya kira mabiyansa su koya daga gare shi, su kuma bi sawunsa. “Ku ɗauki karkiyata [mai sauƙi da marar nauyi] a kanku,” in ji shi a cikin Matiyu 11:29, “kuma ku koya daga gare ni.” Wannan, a gaskiya, shi ne abin da ake nufi da zama “almajiri” na Yesu—almajiri yana nufin mai koyo. Almajiransa su ne waɗanda suke koyo daga gare shi, kuma suke bin misalin rayuwarsa da koyarwarsa. Don haka, sa’ad da Yesu ya wanke ƙafafun almajiransa a daren da zai mutu, ya ce: “Idan ni fa, Ubangijinku da Malaminku, na wanke ƙafafunku, ku ma ya kamata ku wanke ƙafafun juna. Gama na ba ku misali, domin ku ma ku yi daidai yadda na yi muku” (Yohanna 13:14–15).
Yayin da ba za mu iya maimaita darajar kafarar da ke cikin rayuwa da mutuwar Kristi ba, za mu iya—hakika, za mu yi—koyi da ƙanƙan da kai da ƙaunar sadaukarwa da ya nuna, ko da tawul ne a ɗaure a ƙugunsa ko kuma da jikinsa da aka kafa a kan gicciye.
Manzannin kuma suna gargaɗe mu da mu ɗauki Yesu a matsayin misalinmu. Bulus ya ce, “Ku kasance da wannan tunani a tsakaninku, wanda yake naku ne a cikin Kristi Yesu, wanda . . .”—sa’an nan ya nanata yanayin ƙanƙantar da kai da ɗaukakar gicciye da tashin matattu (Filib. 2:5–8). Haka nan kuma, Yohanna ya rubuta a wasiƙarsa ta farko, “Duk wanda ya ce yana zaune a cikin [Yesu] ya kamata ya yi tafiya kamar yadda shi ma ya yi tafiya—wato, a hanyar bada kai, da ƙauna mai ɗaukaka Allah (1 Yohanna 2:6).
Ikon Ruhiun Almasihu mai Zaune a Cikinmu
Don haka, mene ne ma’anar mu a matsayin Kiristoci mu yi “rayuwa ta tsoron Allah”? Bulus ya bayyana hakan a cikin wasu kalmomi na musamman da ba a mantawa da su ba a 1 Timoti 3:16, inda ya rubuta cewa, “Lalle ne, muna shaida, asirin tsoron Allah mai girma ne.” E, tsoron Allah. Mene ne wannan zai iya haɗawa da shi? Wataƙila muna sa ran samun jerin halaye masu kyau ko ayyukan adalci na gaggawa. Maimakon haka, Bulus ya biyo baya da muhimmancin misalin Allah-mutum ga rayuwar Kirista mai tsoron Allah. Mun samu waƙar yabo game da Yesu:
An bayyana shi a cikin jiki,
wanda Ruhu ya kuɓutar,
mala’iku sun gan shi,
aka yi shelar sa a tsakanin al’ummai,
aka bada gaskiya gare shi a duniya,
aka ɗaukaka shi cikin daraja.
Kuna son sanin mene ne ibada ta kwarai? Dubi Yesu. Shi ne “ibada” a cikin surar mutum. Don haka, Kiristoci sukan kira sha’awoyi da ayyukan ibada “kamar Almasihu.” A zuciyar bangaskiyarmu akwai aikin fansa na musamman da ya yi, kuma babban misali na rayuwar Kirista shi ne rayuwarsa ta ɗan-adam mai ban mamaki wadda za a iya yin koyi da ita.
Muna karanta Bisharu/Linjiloli, kuma muna cike da mamakin yadda Ya rayu da kuma ayyukansa. Muna tsayawa cikin girmamawa saboda aikin cetonsa na musamman wanda ba wanda zai iya maimaitawa domin masu zunubi. Muna lura da ƙaunarsa, da haƙurinsa, da hikimarsa, kuma ta wurin ikon Ruhunsa mai zaune a cikinmu, muna neman mu bi sawunsa.
An fara wallafa wannan talifi ne a shafin Blog na Ministirin Ligonier. [Blog ɗin Ministirin Ligonier]


