28/07/2026
Domin fahimtar muhimmancin aikin ɗan adam a cikin Nassi, abin da ake buƙata kawai shi ne a yi la'akari da nassosi da dama da suke la'antar ragwanci da kasala cikin kalmomi mafi tsanani: "Mutum mai mai da hankali ga aikinsa zai sami iko, amma ragwanci zai sa mutum ya zama bawa." (K. Mag. 12:24). "Manomin da ya cika lalaci, ya kasa nome gonakinsa a kan kari, a lokacin girbi ba zai sami kome ba." (K. Mag. 20:4). "Yin shiri a tsanaki zai kai ka ga biyan bukatarka, idan kuwa ka cika gaggawa ba za ka sami abin da zai ishe ka ba." (K. Mag. 21:25).
