
Shin Ikkilisiya tana cike da munafukai ne?
30/07/2026Menene Littafi Mai Tsarki ya ce game da mata Fastoci?
Tambayar ko mata za su iya yin hidima a matsayin fastoci ko dattawa ɗaya ce da ta taɓa zukatan Kirista da dama. Masu bi sun ga yadda wannan batu ya haifar da rikici har ma ya raba ikilisiyoyinsu. Wajen tattauna irin wannan al’amari mai muhimmanci kuma mai saurin tada hankali, yana da muhimmanci a koma ga Littafi Mai Tsarki. Wane haske ne Kalmar Allah take haskawa a kan wannan batu mai raba gardama?
A cikin 1 Timoti 2:8–15, Manzo Bulus ya bayar da bayyananniyar ja-gora da ikilisiya ke bukata don tsara rayuwarta ta hanyar da za ta faranta wa Allah rai. A cikin wannan wasiƙar, Bulus ya rubuta wa Timoti, ƙaramin abokin aikinsa a hidima. Timoti yana yi wa ikilisiya da ke Afisus hidima a wani lokaci mai wahala. Ya fuskanci matsalolin koyarwar ƙarya (1 Tim. 1:3–11; 6:2–10) da kuma ruɗani a wurin sujada (1 Tim. 2:1–15). Ikilisiya kuma tana buƙatar bayyananniyar ja-gora game da cancanta da aikin shugabanninta, wato dattawa da dikononi (1 Tim. 3:1–5:25).
Bayan ya ba Timoti umarni game da aikin addu’a a sujudar Kirista (1 Tim. 2:1–7), Bulus ya karkata don ba da takamaiman shawarwari ga maza da mata yayin da suke shiga cikin sujudar Allah a gaban jama’a (1 Tim. 2:8–15). A cikin waɗannan ayoyin, ya magance zunuban da suka fi addabar kowane jinsi. Dole ne maza su yi addu’a “ba tare da fushi ko jayayya ba” (1 Tim. 2:8). Mata kuma dole ne su fifita tsoron Allah fiye da ƙawa (1 Tim. 2:9–10).
Bulus ya ɗauki wani ƙarin batun da ya shafi shigar mace cikin sujudar jama’a. Da farko, Bulus ya zayyana kiran Allah ga mace dalla-dalla—”Mace ta riƙa koyo da kawaici da matuƙar biyayya.” (1 Tim. 2:11). Manzon ya tabbatar da haƙƙin mata na kasancewa a cikin sujudar ikilisiya da kuma koyon Kalmar Allah, tare da maza, yayin da ake karanta ta da kuma wa’azinta. Ta wannan fannin, almajiran Yesu mata daidai suke ta kowace hanya da almajiran Yesu maza.
Bulus sannan ya haramta wa mata “koyar ko kuma ta yi iko da maza ba” (1 Tim. 2:12). Maimakon haka, su “kasance a nitse.” Mata su shagaltar da kansu da abin da Allah ya kira su su yi—su zama masu koyo a nitse. Kada su ɗauki haramtattun ayyukan da aka zayyana a aya ta 12.
Menene waɗannan ayyukan? Bulus ya ambaci guda biyu. Na farko shi ne koyarwa. Mahalli yana da muhimmanci a nan. Bulus bai haramta wa mace kowane irin aikin koyarwa ba, har ma a cikin ikilisiya. Maimakon haka, Bulus ya haramta wa mata yin wa’azi a gaban jama’a da kuma koyar da Kalmar Allah sa’ad da ikilisiya ta taru don sujudar jama’a. Wannan aikin na dattawan ikilisiya ne (duba 1 Tim. 3:2; 4:11–16). Na biyu kuma shi ne yin iko bisa maza. A babi na gaba, Bulus zai damƙa ikon ruhaniya ga dattawan ikilisiya, ƙwararrun maza waɗanda suka nuna kansu a matsayin ƙwararrun masu gudanarwa da iyalansu (duba 1 Tim. 3:5). Za mu iya taƙaita haramcin Bulus a aya ta 12 ta wannan hanyar: ba a yarda wa mata su riƙe ofishin ko su gudanar da ayyukan dattijo a cikin ikilisiya ba.
A aya ta 13–14 ne Bulus ya ba da dalilan umarninsa da ke aya ta 11–12. Bulus ya tunatar da Timoti game da tsarin da Allah ya bi wajen halittar Adamu da Hauwa’u: “Gama Adamu ne aka fara halitta, sa’an nan Hawwa’u.” (1 Tim. 2:13). Bayan haka Bulus ya tunatar da Timoti game da yadda iyayenmu na farko suka faɗa cikin zunubi: “Ba kuma Adamu ne aka yaudara ba; macen ce aka yaudara ta kuma zama mai zunubi.” (1 Tim. 2:14). Bulus ba ya ba wa Adamu kariya daga alhakin faɗuwa cikin zunubi. Akasin haka, zunubin Adamu ya saba wa bayyanannen hasken Kalmar Allah (duba Far. 2:15). Haka kuma Bulus ba yana cewa a nan Hauwa’u mutum ce mai saurin yarda da yaudara ba. Kawai yana lura da koyarwar Littafi Mai Tsarki ne cewa Hauwa’u ta ci haramtaccen ’ya’yan itace bayan maciji ya yaudare ta.
Ta yaya maganar Bulus a 1 Timoti 2:13–14 ta goyi bayan dokokinsa a aya ta 11–12? Suna yin hakan aƙalla ta hanyoyi biyu. Na farko, haramta wa mata daga koyarwa da gudanar da iko da aka bayyana a aya ta 12 yana da tushe a hanyar da Allah ya halicci ’yan adam (1 Tim. 2:13). Ma’ana, yana da tushe a cikin halitta. Haramcin Bulus ba na musamman ba ne ga yanayin da ke Afisus; kuma ba a iyakance shi ga ƙarni na farko ba. Hakika ba za mu iya jingina shi ga takaitaccen ra’ayi na Bayahude na ƙarni na farko ba. Wannan haramcin yana nuna tsarin da Allah ya kafa a cikin halitta ga maza da mace.
Na biyu, haramcin Bulus a aya ta 12 ya samar da labarin gargaɗi a aya ta 14. Lokacin da Hauwa’u ta yi ƙoƙarin “zama kamar Allah” kuma ta ƙi yin biyayya ga Kalmar Allah, masifa ta biyo baya (Far. 3:5). Babu wani alheri da ke fitowa daga bijire wa kyakkyawan tsarin da Allah ya kafa domin jin daɗinmu. Saboda haka, Bulus ya ci gaba da cewa, bai kamata mata su yi ƙoƙarin neman abin da Allah ya haramta musu ba. Ya kamata su sadaukar da kansu ga abin da Allah ya kira su su yi. Allah yana kiran yawancin mata (amma ba duka mata ba) zuwa ga aure da haihuwa (1 Tim. 2:15). Lokacin da mace mai bi ta rungumi wannan kiran tare da “imani da ƙauna da tsarki, tare da kamun kai,” to za ta iya samun tabbacin ceton da Allah ya ba ta kyauta a cikin Almasihu.
Muna bukatar kalaman Bulus a cikin ikilisiya a yau. Suna nuna mana tsari ko misali da Allah ya shimfiɗa wa maza da mata a cikin Ikilisiyarsa. Suna nuna mana haɗarin kauce wa wannan tsarin. Amma ba kawai shimfiɗa hane-hane ga ikilisiya suke yi ba. Suna gabatar da kyakkyawan hangen nesa na abin da Allah ya kira mata su zama da kuma abin da za su aikata. A zamanin da ake yawan ƙasƙantar da mata a matsayin waɗanda suka ƙasa maza ta fuskar hankali da ɗabi’a, Bulus ya gaya wa Timoti cewa mata, ba su gaza maza ba, suna da haƙƙin zama masu koyo a makarantar Almasihu (1 Tim. 2:11). Za su ƙawata kansu da bin Allah—ba kawai sa’ad da suke taruwa mako-mako tare da ikilisiya don yin sujada ba (1 Tim. 2:9) har ma a cikin ayyukan yau da kullum na kula da yaransu (1 Tim. 2:15). A cikin yanayi na natsuwa da na yau da kullum na rayuwa ne Allah yake jin daɗin aiwatar da manufofinsa masu ban mamaki na alheri. Kuma wannan bishara ce ga dukan mutanen Allah a kowane zamani.
An fara wallafa wannan talifi ne a shafin Blog na Ministirin Ligonier. [Blog ɗin Ministirin Ligonier]


