
Fitaccen Matsakaici
18/08/2026Saboda ƙaunar da Allah ya yi wa Duniya
Kowane Kirista ya yi imani da kafara mai iyaka. Hakan yana iya zama abin ban dariya ga abokaina ’yan Arminiya domin an daɗe ana zaton cewa ’yan Calvin ne kawai suke riƙe da harafin “L” da ake tsoro a cikin TULIP. Amma idan an fahimci mutuwar Yesu Almasihu a matsayin kafara ta gaskiya (kuma ba kawai wadda za ta iya zama kafara ba), to ba za a iya kauce wa batun iyaka ba, sai dai idan kun gaskata kuskuren koyarwar cewa kowa zai sami ceto.
Sanin cewa mutuwar Almasihu ta yi kaffara ta gaskiya domin zunubai ne yake jagorantar fassararmu na waɗancan nassosi masu ban al’ajabi da suke magana game da faɗin aikinsa na ceto. Misali, Yohanna ya rubuta cewa Yesu ne “hadayar sulhu domin zunubanmu, ba domin namu kaɗai ba amma har da zunuban dukan duniya” (1 Yohanna 2:2). Zaɓin a nan ba tsakanin ma baye Calvin da ma biye Arminius ba ne. Tsakanin ma biye Calvin ne da wadanda sun yarda da kuskuren koyarwar nan da ta ce kowa zai sami ceto. Idan “duniya” tana nufin “kowane mutum da ya taɓa rayuwa ko zai rayu” to kowa zai tsira saboda haƙiƙanin yanayi na hadayar sulhu. Babu zunubin da za a bari ba tare da an biya shi ba — har da zunubin rashin imani.
Babu wanda yake ɗaukar koyarwar Littafi Mai Tsarki a kan jahannama da shari’a da muhimmanci da zai taɓa tabbatar da koyarwar nan cewa kowa zai sami ceto a karshe duka, wanda hakan yana nufin cewa Yohanna yana amfani da “duniya” a nan ne don nufin wani abu dabam ba kowane mutum da zai taɓa rayuwa ba (kamar yadda yake yi sau da yawa; duba Yohanna 14:19; 16:8; 18:20; 1 Yohanna 2:15,). Burin Yohanna shi ne ya tabbatar da cewa Yesu ne kaɗai Mai Ceton da duniya take da shi. Mutuwarsa tana fansar mutane ba kawai daga cikin Yahudawa ko Amurkawa ko daga kowane rukuni ɗaya ba, amma daga cikin dukan duniya.
koyarwar ma biyen Calvin yana kare mutum daga karkatacciyar koyarwa da ta ce duka mutane za su sami ceto, a gefe guda, da kuma kuskuren rage haƙiƙanin yanayi na kaffara a ɗayan gefen. Ma biye Calvin ya fahimci cewa mutuwar Yesu tana ceton dukan waɗanda aka yi ta dominsu. Ma’ana, ana kallon kaffara a matsayin mai iyaka a fannin iko da manufarta. Dukan waɗanda Almasihu ya mutu dominsu za su tsira.
Koyarwar Arminius,ba zai iya kiyaye wa daga irin waɗannan kurakuran cikin nasara ba. Koyarwan yana da’awar cewa an tsara mutuwar Yesu ne domin ya ceci kowane mutum a tarihi ba tare da lallai hakan ya faru ba. To, hakan na nufin kaffara ba ta ceci dukan waɗanda aka yi niyya dominsu ba. Ma’ana, ra’ayin wannan koyarwa, yayin da yake da’awar cewa kaffara ba ta da iyaka a fannin faɗinta, tilas ne ya kammala da cewa tana da iyaka a fannin ingancinta. Ta kasa cimma babban burinta na duniya baki ɗaya.
Bambanci tsakanin waɗannan ra’ayoyi guda biyu yana kama da bambanci tsakanin ƙunƙuntar gada da ta ratsa ko’ina cikin kwararo da kuma faffadar gadar da ta tsaya a rabi kawai. Wa zai damu da faɗin gadar idan har ba za ta kai ka ɗayan ɓangaren ba?
Wannan bambancin shi ne ya sa Charles Spurgeon ya yi jayayya cewa Koyarwar Arminius, fiye da koyarwar Calvin, tana iyakance kaffarar Almasihu. Arminian ya ce:
“Almasihu ya mutu domin kowane mutum ya sami damar tsira idan” — sa’an nan wasu sharudda na ceto suka biyo baya. Yanzu wanene yake iyakance mutuwar Almasihu? To, kai ne. Ka ce Almasihu bai mutu ba ta yadda zai tabbatar da ceton kowa ba tare da kuskure ba. Muna neman gafararka sa’ad da kake cewa muna iyakance mutuwar Almasihu; muna cewa, “A’a, ya kai maigida, kai ne kake yin hakan.” Muna cewa Almasihu ya mutu ta yadda ya tabbatar da ceton babban taro wanda babu wanda zai iya ƙirgawa, waɗanda ta wurin mutuwar Almasihu ba wai kawai za a iya ceton su ba ne, amma cetattu ne, dole a cece su, kuma babu yadda za a yi su shiga kasadar zama wani abu in ba cetattu ba. Kana da ikon riƙe kaffararka; kana iya riƙe ta. Ba za mu taɓa yin watsi da tamu domin tata ba. (Spurgeon’s Sermons, vol. 4, p. 228)
To, mene ne “namu” ra’ayin kaffara wanda Spurgeon ya kāre da ƙwazo sosai? Musamman ma, fahimta ce cewa lalle Yesu ya fanshi kowa da ya yi nufin fansa sa’ad da ya zubar da jininsa a kan gicciye. Kamar yadda babban firist a ƙarƙashin tsohon alkawari ya ɗauki sunayen kabilu goma sha biyu na Isra’ila a kan farantin ƙirjinsa sa’ad da yake gudanar da hidimar hadaya, haka nan babban Firist namu a ƙarƙashin sabon alkawari yana da sunayen mutanensa a rubuce a zuciyarsa sa’ad da ya miƙa kansa a matsayin hadaya domin zunubansu.
A cikin Yohanna 10, Yesu ya sanar a fili game da takamaiman abin da mutuwar kaffararsa ta sa gaba. Ya kira kansa “Maikiyayi Mai Kyau” wanda “yakan ba da ransa saboda tumaki” (Yohanna 10:11). Jim kaɗan bayan haka, ya bayyana tumakinsa a matsayin waɗanda Ubansa ya ba shi. Haka kuma, ya bayyana wa wasu Isra’ilawa marasa biyu a fili cewa, “ba kwa ba da gaskiya ba ne, domin ba ku cikin tumakina” (Yohanna 10:26–29, NKJV).
Addu’ar babban firist na Ubangijinmu a cikin Yohanna 17 tana nuna irin wannan iyakantaccen fanni. Yayin da yake shirin mutuwarsa ta hadaya domin mutanensa, ya yi addu’a musamman—hakika, ga su kaɗai—domin su. Su ne waɗanda Uba ya ba shi daga cikin duniya (Yohanna 17:6). Saboda haka, roƙon cetonsa na firist ya iyakantu ga su kaɗai: “Ina yin addu’a dominsu. Ba na yin addu’a domin duniya ba, sai dai domin waɗanda ka ba ni, domin su naka ne” (Yohanna 17:9). Ba za a iya tunanin cewa Yesu zai kasa yin addu’a ga waɗanda yake shirin mutuwa dominsu a matsayin hadaya ta musaya ba. Waɗanda ya yi addu’a dominsu, su ne waɗanda ya mutu dominsu.
Koyarwar iyakantaccen kaffara, ko kuma takaitaccen fansa, ba ta nuna wata tawaya a cikin mutuwar Kristi ba. Domin matsayin wanda ya sha wahalar ne ya sa mutuwar Yesu take da kima mara iyaka. Dokokin Dort sun yi babban ƙoƙari wajen tabbatar da wannan batu kuma sun bayyana a fili cewa “mutuwar Ɗan Allah . . . tana da ƙima da daraja mara iyaka, tana kuma da isasshen iko na kaffara zunuban dukan duniya” (2.3).
Iyakancewar da ke cikin kaffarar ta samo asali ne daga nufi da kuma manufar Allah na aiko Yesu zuwa gicciye. An tsara aikin fansa na Kristi domin ya zama takaitaccen kaffara ga mutanensa—waɗanda Uba ya ba shi. Mutuwarsa tana da nufin ceton zaɓaɓbu.
Yesu ya koyar cewa dukan hidimarsa ta fansa an aiwatar da ita ne domin cika tsarin da Allah ya riga ya tsara. Wannan shi ne abin da yake nufi a cikin Yohanna 6:38–39:
Gama na sauko daga sama ne ba domin in yi nufin kaina ba, sai dai nufin wanda ya aiko ni. Kuma nufin wanda ya aiko ni shi ne, kada in rasa kome daga dukan abin da ya ba ni, sai dai in tada shi a rana ta ƙarshe.
Masana tauhidi suna kiran wannan tsari da alkawarin fansa inda, kafin farkon tarihi, Uba, Ɗa da kuma Ruhu Mai Tsarki suka yi alkawarin kawo ceton fāɗaɗɗun mutane. Domin tsantsar jinkai da alheri, Uba ya zaɓi mutane da za a ceta (Rom. 9:11–13; Afis. 1:4; 2 Tas. 2:13). Waɗannan zaɓaɓbu ya ba Ɗansa (Yohanna 6:37, 39; 17:6, 9, 24) wanda ya ƙaddamar da kansa don ya tabbatar da ceton su ta hanyar manzancinsa na fansa a cikin jiki (Markus 10:45; Yohanna 10:11). Domin kiyaye wannan tsari na Allah, Uba da Ɗan suna aiko Ruhu zuwa duniya (Yohanna 15:26; 16:5–15) domin ya tabbatar da aikin Kristi ga waɗanda Uba ya ba Ɗan kuma waɗanda Ɗan ya mutu dominsu.
Wannan ra’ayi na kaffara yana tabbatar da nasarar bishara. Allah yana da mutane waɗanda za a ceta babu kuskure ta hanyar wa’azin bishara. Ya zaɓe su. Kristi ya mutu dominsu. Kuma Ruhu zai sake haifarsu ta hanyar saƙon ceto. Wannan gaskiya ta ƙarfafa Bulus sa’ad da yake fuskantar sanyin gwiwa a Koranti (Ayyukan Manzanni 18:9–10), kuma za ta ci gaba da ƙarfafa mu a ƙoƙarinmu na bishara a yau—ba kawai a mazauninmu ba, har ma a duniya baki ɗaya (Ru’uya 5:9).
An fara wallafa wannan talifi ne a shafin Blog na Ministirin Ligonier. [Blog ɗin Ministirin Ligonier]


