Yadda Za A Karanta Su Zaburan Hawan Zuwa Gaban Allah

23/06/2026

Yadda Za A Karanta Su Zaburan Hawan Zuwa Gaban Allah

23/06/2026

Shin Mutum a asali nagari ne ko kuwa gaba daya mai zunubi ne?

Ra’ayin cewa mutane a asali nagari ne yan maimaita tsohuwar koyarwar karya ta Pelagius, wadda ta tabbatar da cewa zunubin Adamu ya shafi Adamu ne kadai. Bisa ga wannan ra’ayi, faduwar Adamu ba ta shafi dabi’ar dan adam. Nassi ya koyar da akasin haka, yana mai tabbatar da cewa zunubin Adamu ya shafi dukkan zuri’a da aka haifa ta dabi’a (Rom. 5:12–14). A dabi’ance, ‘yan-adam “‘ya’yan fushi” ne (Afis. 2:3). Wannan shi ne ma’anar tauhidi a bayan kalmar nan lalacewar dabi’a gaba daya—wato harafin T a cikin TULIP (rukunai biyar na koyarwar Calvin). Ma’ana, zunubi ya bata dukkanmu (ban da Yesu) a zuciya, tunani, jiki, da kuma rai. Ana samun wannan koyarwa a dukan Tsohon Alkawari da Sabon Alkawari (misali, Far. 6:5; Zab. 14:1–3; 143:2; Maik. 7:20; Isha. 64:6; Mar. 7:18–23; Rom. 1:21–32; 3:10–18, 23; 8:5–8; Gal. 4:3; Afis. 2:1–3; 4:17–19; Titus 3:3).

Kiristoci za su iya rikicewa saboda Nassi yana koyarwa cewa Allah ne ya halicci ‘yan-adam a kamaninsa (Far. 1:26–27), kuma Allah ya kira duk abin da ya halitta nagari (aya 31). Idan komai da Allah ya halitta nagari ne, kuma idan Allah ne ya halicci dabi’ar dan adam, shin hakan ba yana nufin cewa dabi’ar dan adam lallai nagari ce ba? E. Kamar yadda aka halitta ta tun asali, dabi’ar dan adam nagari ce. Sai dai kuma, wani bangare na dabi’ar dan adam shi ne nufin mutum. ‘Yan-adam na farko suna da alhakin daidaita nufinsu da aka halitta daidai da nufin Allah—domin su yi masa biyayya. Maimakon haka, sai suka ki yi wa Allah biyayya. Kamar Shaitan, sun karkatar da nufinsu ya saba wa nufin Allah, hakan ya shigar da zunubi da wahala cikin duniya da kuma cikin dabi’unsu. Ma’ana, sun yi zunubi. Lokacin da suka yi haka, dabi’ar dan adam ta gurbace kuma ta lalace. Irin abin da aka haifa shi ne halinsa, kuma yanzu ana haifar dukkan mutane da dabi’ar dan adam gurbatacciya kuma fāɗaɗɗiya. Yanzu ana haifar ‘yan-adam bayi ga zunubi.

Wannan shi ne ya sa da’awar nan cewa “kowa yana yin dan zunubi kadan” ita ma ba daidai ba ce. Mun saba gwada kanmu da sauran ‘yan-adam, kuma muna son zabar mutane mafi muni don kwatanci. Muna son kwatanta kanmu da mutane kamar Adolf Hitler, Joseph Stalin, ko Mao Zedong. Yana da sauki mutum ya ji dadi da kansa idan ma’aunin shi ne kawai kin kkashe miliyoyin mutane. Amma wannan ba shi ne ma’aunin da Maganar Allah take auna zunubi da shi ba. Ma’aunin shi ne nufin Allah, kuma abin da ake bukata shi ne cikakkiyar biyayya ga wannan nufin. “Duk wanda ya kiyaye dukan doka, amma ya yi tuntuɓe a guda ɗaya, ya zama mai laifi da ita duka” (Yakubu 2:10; duba Gal. 3:10). Tambayar ba ita ce, shin ka Guji kashe miliyoyin mutane a yau ba? Tambayar ita ce, shin a yau ka “kaunaci Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka, da dukan ranka, da dukan hankalinka” sarai, kuma ka kaunaci “makwabcinka kamar kanka” (Mat. 22:37–39)? Sau nawa ka kasa yin wannan sarai? Shin “kadan” ne kawai? A’a. Muna kasawa wajen yin hakan sosai, kuma hakan yana nufin muna yin zunubi da yawa. Wannan shi ne ya sa muke bukatar cikakken adalci na Yesu Almasihu. Shi ne kadai wanda ya taba cika dokar sarai.


An wallafa wannan talifi ne asali a dandalin Ministirin Ligonier Blog. [Blog ɗin Ministirin Ligonier]

Ministirin Ligonier

Ministirin Ligonier

Mu ne zumuntar koyarwa ta Dr. R.C. Sproul. Mun wanzu don yin shelar, koyarwa, da kuma kāre tsarkin Allah cikin dukan cikarsa ga mutane da yawa gwargwadon iko. Manufarmu, sha'awarmu, da dalilinmu shi ne taimaka wa mutane su yi girma cikin sanin Allah da tsarkinsa.