
Ta’aziyyar Allah a cikin Rashin Ɗa Ko ‘Ya
11/06/2026
Abubuwa Uku Da Ya Kamata mu Fahimta Game Da Ibraniyawa
18/06/2026Abubuwa 3 Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Yowel
Abin da yawancin mutune suka sani game da Littafin Yowel shi ne babban anabcin nan a cikin Yowel 2:28-29, a wurin da Allah ya yi alƙawarin zuba Ruhun Sa a bisa dukan masu-rai, saboda dukan membobi na al’umar mutanen Allah su yi annabci. Amma ba za a iya fahimtar ma’anar waɗannan ayoyi haka kawai su kaɗai ba, sai dai in an dubi babban saƙon littafin gaba-ɗayan shi. Akwai abubuwa uku da ya kamata ku sani game da littafin Yowel wanda zai taimake ku fahimtar saƙon.
1. Ba a san ainihin shekarar ko lokacin da aka rubuta littafin Yowel ba.
Da farko, tarihi na yanayin faruwar mafi yawa cikin litattafan annabawa yana da muhimmanci ga saƙon litattafan, amma ba a san lokaci taƙamammen da aka rubuta littafin Yowel ba. Misali, haikali yana nan, wanda ke nufin haikalin Sulemanu ne da ke nan kafin a tafi da su bauta (an rusa a ƙarni na 586 kafin zuwan Kristi), ko kuma haikalin da aka keɓe bayan sun dawo daga bauta ( a ƙarni na 516 kafin zuwan Kristi). Ba a ambaci wani sarki ba, ko a ambaci ko ɗaya daga abokan gaban Isra’ila ba, ko kuma na Juda ba. Ƙwararrun malamai sun ba da zaɓi daban-daban game da lokacin, amma babu wata tsayayyar rana da ke nuna ainihin wannan lokacin. Kamar dai littafin yana ɗauke da ra’ayoyi na abubuwa da suke nan kafin zuwan su bauta, waɗanda suka danganci lokacin da aka rusa haikalin, kamar yadda aka yanke yin hadaya (Yowel 1:9), da samun barazana daga mayaƙan arewaci (Yowel 2:20), da bayyana alƙawarin kuɓutarwa mai zuwa a nan gaba (Yowel 2:23-29). Waɗansu suna gani cewa yana da wuya a gane lokacin rubuta littafin, domin littafin ya zo ya zama abin da ake amfani da shi a tsarin ibada, wanda akan yi ta furtawa a duk lokacin da wata masifa ta sami ƙasa gaba-ɗaya.
2. Yanayin na lokacin rubuta littafin shi ne Annobar Fara.
Abu na biyu da ya kamata ku sani game da littafin Yowel shi ne, yanayin da ake ciki lokacin rubuta littafin yana da dangantaka da babban saƙon littafin. Halin da ake ciki lokacin rubuta littafin shi ne yanayi na annobar fara. Sura ta ɗaya kira ne ga al’uma gaba-ɗaya su tuba domin wani annoba na fara ya yi mummunan ɓarna da ba a taɓa yin irin sa ba. An bayyana annobar a Yowel 1:4, yanayin da ɗumbin fara sun hallakar da duk wani abu da ake iya ci. An yi kira ga ƙungiyoyi daban-daban su yi makoki saboda sakamakon wannan faruwa: An buƙaci mashaya su yi makoki domin an hallaka bishiyoyin inabi (Yowel 1:5-7), firistoci ma su yi makoki domin hadaya ta yanke ( Yowel 1:8-10), Manoma su ma su yi makoki domin ba za a sami amfanin gona ba ( Yowel 1:11-12). An yi kira ga firistoci su jagoranci taron jama’ar Allah zuwa ga sujada ta makoki, wanda ya ƙunshi kuka da azumi (Yowel 1:13-14).
Ruɗani na annobar fara ya zama kamanci na ranar Ubangiji. Zai kasance ranar shari’a ga waɗanda suka ƙi amincewa da Allah, sannan ya zama ranar albarka ga waɗanda suka juyo ga Allah. Wannan annoba ta fara tana gabatar da shari’a mai zuwa na ranar nan wadda aka fara ambata a cikin Yowel 1:15:
Kaiton wannan rana!
Gama ranar UBANGIJI ta yi kusa.
An bayyana hallakarwa na wannan rana a Yowel 1:16-20, tare da kira mai gaggawa na gargadi a cikin Yowel 2:1-2, wanda ya taru ya haɗe cikin nanata irin hali na wannan “ rana” a matsayin “ranar duhu da damuwa” da kuma “rana mai gizagizai da duhu baƙin ƙirin! Wannan duhu ya warwatsu bisa manyan tsanuka, yana nuni ga runduna mai yawa mai ƙarfi, da suke a shirye domin yaƙi da mayaƙan wadanda ba za a iya tsayar da su ba. Mutane suna ruɗe saboda tunani na fuskantar wannan runduna, domin ta fi duk wasu runduna na duniya; rundunar Ubangiji ce. Ubangiji da kansa ya furta muryar Sa a gaban wannan runduna, duk halitta takan girgiza, kuma rana da wata sukan duhunta (Yowel 2:10-11).
A cikin Yowel, ranar Ubangiji ta fi ƙarfin duk wani faruwa na kawai a tarihi; tana bayyana abin da zai faru bayan mutuwa da tashi, lokacin da duk wani tarihi zai kare. Yowel ya yi amfani da wannan mummuna bala’i na hukuncin Allah mai zuwa a ranar Ubangiji domin kiran jama’ar Allah su tuba(Yowel2:15-17). Ya yi masu alƙawarin albarku a cikin jiki wanda zai kasance canzawa na mummunan bala’i na annobar fara (Yowel 2:21-27), da kuma albarka ta ruhaniya wanda zai zo tare da zuba Ruhun Sa Mai-Tsarki (Yowel 2:28-32).
3. Manzo Bitrus ya ambaci Littafin Yowel domin bayyana abubuwan da suka faru a ranar Fentakos.
Abu na uku da ya kamata ku sani game da littafin shi ne, manzo Bitrus ya ambaci Yowel 2:28-32 a cikin Ayyukan Manzanni 2:17-21 domin ya yi bayani na abubuwan da suka faru a ranar Fentakos. Albarku na ruhaniya da Yowel ya yi annabcin su suna cika a sa’adda Allah ya zubo Ruhun Sa bisa duk mai-rai domin dukan wanda ya yi kira ga sunan Ubangiji zai tsira.
Bayan haka ma, aikin annabci na yaɗa maganar Allah ya faɗaɗa har ya haɗa da dukan kowane irin mutane a cikin al’umma, haɗe da al’ummai, waɗanda suke magana kuma kowa yake fahimtar su cikin harshen sa a daidai yadda Ruhu ya ba su damar yi (Ayukan Manzanni 2:4). Maimakon hukuncin ƙarshe da zai sauko a kan maƙiyan Allah ya faru a wannan lokacin (Yowel 3:1-8), sai aka haɗa cikakkiyar sake maido da jama’ar Allah (Yowel 3:17-21), tare da aiwatar da nufin Allah na aikin ceto ta wurin shelar labari mai-daɗi na Yesu Kristi ga dukan duniya. Saboda haka, ta wurin Yesu Kristi mun mori biyan hakkin fari na ceton mu. Muna jiran cikawar ceton mu sa’adda Mai-Ceton mu zai dawo duniyar nan domin ya cika ranar Ubangiji, a hukuncin ƙarshe na maƙiyan Allah, da kuma cikakkiyar sake maido da mutanen Sa. A wannan lokaci, za mu mori cikakkiyar madawwamiyar kasancewar Sa da kuma albarkun Sa na ruhaniya da na jiki a yalwace wanda kasancewar Sa ne ke kawowa.
An fara buga wannan labarin a shafin yanar gizon Ministirin Ligonier Blog. [Blog ɗin Ministirin Ligonier]


