
Shin Yesu Cikakke Ne?
13/10/2026
Shin Aure Na har Abada Ne?
20/10/2026Ta Yaya Zan Iya Girma a Cikin Hikima?
Littafi Mai Tsarki ya koya mana cewa muna rayuwa ne a cikin duniyar da ke cike da abubuwa masu gaba da juna, waɗanda a cikinsu akwai hikima da wauta. Waɗannan biyun suna wakiltar hanyoyi ne masu bambanci da juna waɗanda ke tsara rayuwar mutane. Hikima tana da alaƙa da hanyar rai, wauta kuma da hanyar mutuwa.
Sau da yawa ana fassara hikima a matsayin ilimin aikace-aikace ko kuma ƙwararren amfani da ilimi. A matsayinmu na Kiristoci, muna bukatar mu ƙara zurfafa ta hanyar tunawa da kalaman Sulemanu: “Tsoron Ubangiji shi ne farkon ilimi” (K. Mag. 1:7). A bisa koyarwar Littafi Mai Tsarki, hikima tana amfani da ilimin Allah ne ga rayuwa, ko kuma a fadi ta wata hanya, hikima ita ce kwarewar yin rayuwa bisa ga ka’idodin Allah.
Ana buƙatar wannan kwarewa a kowane fanni na rayuwa. Ya kamata mu kasance da hikima a cikin maganganunmu, dangantakarmu, gidajenmu, sana’o’inmu, motsin zuciyarmu, jima’iyyarmu, shugabancinmu, kasancewarmu ‘yar kasa, tsare-tsarenmu, da kuma yadda muke sarrafawa da amfani da albarkatun da muke da su. Babu wani abu a cikin ayyukanmu na yau da kullum da ba ya buƙatar hikima, domin burinmu shi ne mu kasance masu kwarewar yin komai cikin hikima, domin girmamawar da daukakar Allah.
Amma ta yaya za mu iya girma cikin hikima? Wataƙila zai taimaka idan muka yi tunani game da yadda muke girma a cikin kowace kwarewa. Lokacin da muke son koyan yin wani abu da kyau, yana bukatar ƙoƙari na niyya, koyarwa, da kuma aiwatarwa. Girma a cikin kwarewar hikima ba shi da bambanci.
Ƙoƙari Da Niyya Don Samun Hikima
kwarewar hikima duka abu ne da muke roƙo kuma muke nema. A ƙarshe, hikima wata fa’ida ce da aka ba mu cikin Yesu Almasihu. Manzo Bulus ya ce a cikin Yesu akwai ɓoyayyun “dukan taskokin hikima da na ilimi” (Kol. 2:3). Ubangijinmu yana da wannan hikimar domin zaɓaɓɓunsa, kamar yadda Bulus ya faɗa a wani wuri, Shi “ya zama mana hikima daga wurin Allah” (1 Kor. 1:30). Da yake an ɗauke mu a matsayin ‘ya’ya a cikin iyalin Allah, an yi mana alkawarin hikima a cikin Yesu wadda ke ba mu karfin gwiwar yin roƙo da kuma tabbacin cewa Allahnmu mai yawan kayauta zai bayar (Yaƙub 1:5). Amma ba a raba bayarwar hikima da hanyoyin da Allah yake amfani da su wajen ba da ita.
Littafi Mai Tsarki ya kuma koyar da cewa girma cikin hikima yana zuwa ne ta hanyar ƙoƙari na niyya. Hikima ba wata baiwa ce da mutum yake samuwa a haifuwa ba, ban kuma ba ta zo da kanta kai tsaye. Har ila yau, sarki mai hikima ya umurci cewa dole ne mu neme ta:
Idan kana nemanta kamar azurfa
kuma ka neme shi kamar ɓoyayyun dukiya,
sa’an nan za ka fahimci tsoron Ubangiji
kuma ka sami ilimin Allah. (K. Mag. 2:4–5)
Muna girma cikin hikima ta hanyar roƙo da nema: “Ku yi roƙo, za a ba ku; ku nema, za ku samu” (Mat. 7:7).
Allah ne Yake Koya Mana Hikima
Girma a cikin jerin kwarewa kuma yana buƙatar koyarwa, kuma haka yake tare da hikima. Muna koyo game da hikima daga Maganar Allah da kuma duniya. Littafi Mai Tsarki ya ce,
Gama Ubangiji ne yake bayar da hikima;
daga bakinsa ilimi da fahimta suke fitowa. (K. Mag. 2:6)
Koyarwa daga Nassosi tana zuwa ta hanyoyi da dama, amma Littafi Mai Tsarki a kowane lokaci yana nanata muhimmancin iyaye wajen koyar da ’ya’yansu hikima. Sulemanu ya nuna wannan misali a fili, domin sashen farko na littafin Karin Magana ya ɗauki surar uba ne yana koyar da ɗansa. Ya ce:
Ku saurara, ya ku ‘ya’ya, ga koyarwar uba,
kuma ku kasa kunne, domin ku sami fahimi,
gama na ba ku kyawawan farillai;
kada ku yi watsi da koyarwata.
Lokacin da nake ɗa tare da ubana,
mai tausayi, makaɗaici a gaban mahaifiyata,
ya koya mini, ya kuma ce mini,
“Bari zuciyarka ta kiyaye maganata.” (K. Mag. 4:1–4).
Misalin Timoti ya kuma ƙarfafa mu, wanda tun yana yaro ya san Nassosi masu ikon ba shi hikima domin ceto (2 Tim. 3:15). Akwai ƙwaƙƙwaran dalilin yin imani cewa ya mai da hankali ga koyarwar mahaifiyarsa da kakarsa yayin da suke koya masa wannan hikima (duba 2 Tim. 1:5).
Halitta kuma littafi ne wanda zai iya koya mana game da hikimar Allah. Wannan haka yake domin Hikima ta taka rawar gani a halitta, saboda haka alamar yatsar Hikima tana ko’ina (K. Mag. 8:22–31). Cikin abin tunawa, kalmomin Agur kusa da ƙarshen littafin Karin Magana sun ce,
Abubuwa huɗu a duniya ƙanana ne,
amma suna da hikima ƙwarai da gaske. (K. Mag. 30:24–28)
Ya ci gaba da ambaton hikimar tururuwa, rema, fara, da ƙadangare. Hatta ƙanana da marasa muhimmanci a cikin halitta suna koya mana ƙa’idodi don rayuwa mai kwarewa da ta biyan Ubangiji.
Amfani da Hikima a Aiki
Babu wata kwarewa da ake samu ko a ƙarfafa ta sai dai idan mun duƙufa ga yin ta. Sulemanu ya ce,
Ya ɗana, kada ka manta da koyarwata,
amma bari zuciyarka ta kiyaye dokokina. (K. Mag. 3:1)
Wannan shi ne dalilin da ya sa ake kamanta hikima da wauta da tafarkin hanya—ainihin dalilin kowace hanya shi ne mutum ya ɗora ƙafafunsa a kanta kuma ya yi tafiya. Idan muna son mu girma cikin hikima, dole ne mu yi aiki da hikima, mu kasance ba masu ji kawai ba amma masu aikata ta. Yayin da muke yin haka, za mu iya ci gaba a hankali, amma an yi alkawarin girmanmu:
Hanyar masu adalci tana nan kamar hasken alfijir,
wanda yake ƙara haskakawa har zuwa cikakkiyar rana.
Hanyar miyagu tana nan kamar babban duhu;
ba su san abin da ya sa su tuntuɓe ba. (K. Mag. 4:18–19)
Girma cikin hikima ba shi da bambanci da koyo da girma a kowace kwarewa. Ta hanya mai sauƙi, muna biɗar ta da ƙoƙari na niyya, muna samun koyarwa akai-akai daga Magana da halitta, muna kuma aiwatar da ka’idodinta, muna rayuwa cikin tsoron Allah mai kwarewa har sai, ta wurin alherin Yesu, an kamalta mu a duniya mai zuwa.
An wallafa wannan makala ne da fari a Ministirin Ligonier Blog. [Blog ɗin Ministirin Ligonier]


