
Abubuwa 3 Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Yowel
16/06/2026Abubuwa Uku Da Ya Kamata mu Fahimta Game Da Ibraniyawa
Wata hanya ɗaya da za a fahimci muhimman batutuwa na Ibraniyawa shi ne, a nazarci ainihin muhimman gudunmawa da ta yi ga tsayayyun manufofi uku na fannin koyarwar addini.
1. Ibraniyawa yana da muhimmanci ga fahimtar tauhidin alƙawari.
Zan kusan iya cewa, Ibraniyawa shi ne wasiƙar Sabon Alƙawari mafi muhimmanci idan za a fahimci tauhidin alƙawari, ko da ya ya ne ma wannan fahimtar take, za a sami ƙaruwa dangane da yadda mutum ya fassara littafin Ibraniyawa. Ya bincika manufar Tsohon Alƙawari, da kuma nuna dangantakar ta da na sabon alƙawari. Ya kasance madubin fassara, wanda ake amfani da shi wajen karanta Tsohon Alƙawari.
Masu karatu za su iya yin kuskuren tunanin cewa Ibraniyawa yana yin watsi da tsohon alƙawari. Amma sam wannan ba gaskiya bane. Ɗaukakan sabon alƙawari yana matuƙar haskakawa ne idan an dubi tsohon alƙawari cikin dukan ɗaukakar sa, duk da cewa wancan ɗaukakan yakan ɓata. Wannan bambancin yana bayyanuwa cikin kalamai dayawa na su “idan/haka kuma” dubi Ibraniyawa2:1-4; 13-14; 12:25). Ibraniyawa ya nuna cewa ba wai sabon alƙawari ya rusa tsohon bane ―ya cika shi ne. Wannan zai ba da tsari ga yadda muke karanta Littafi Mai Tsarki gaba-ɗaya. Ibraniyawa ya nuna mana cewa nassi tana ba da fassara ga nassi. Ba wai za mu kafa tsohon da sabon su yi adawa da juna ba, amma mu duba su bisa matakin da kowanne ke kai ―inuwa da ainihi, alƙawari da cikawar ta.
Marubucin ya yi himmar bayyana maɗaukakiyar dama, da kuma nauyin alhakin rayuwa a zamanin sabon alkawari (dubi Ibraniyawa1:2-3). Tun da yake muna ƙarƙashin shugabanci na alƙawari da yake nagari mafifici (Ibraniyawa 8:6), a gaskiya ma marar aibu ( Ibraniyawa 8:7-8), muhimmancin ya wuce misali. Kashedin sa ya fi tsauri, alƙawuran kuma sun fi daɗi, begen ma ya fi kowanne. Wannan ba alƙawari na haka kawai bane―madawwami ne (Ibraniyawa 13:20). Littafi Ibraniyawa ya bayyana sosai kuma dalla-dalla abin da Manzo Bulus ya fada a cikin 2 Korintiyawa 1:20: “ Gama duka alƙawuran Allah suna samun Eh ɗin su a cikin sa.” Alƙawari ɗayan nan na alheri mai ɓangarori daban-daban na aiwatar da ita, ya girma ya bunƙasa a zuwan Kristi. Ga Ibraniyawa kuwa wannan ne ya canza komai. Idan ka karanta Ibraniyawa, ka lura da ire-iren ɗaukaka na sabon alƙawari.
2. Ibraniya yana da muhimmanci ga fahimtar Tauhidin-Kristi.
Shi sabon alƙawari na da matuƙar ɗaukaka ne saboda Matsakancin ta. Idan bangaskiya shi ne hanyar morar alherin alƙawarin Allah ( kamar yadda yake a kullum), to kuma ya kasance dole abin da ake imani da shi Ya iya (ya amince) ya ɗauki nawayar imanin mu. A fili dalla-dalla Ibraniyawa ya tabbatar da fifikon Kristi bisa komai, shi ne zahiri na kowane abin da ke inuwa a tsohon alƙawar, Shi ne abu mafi girma da fifiko na bangaskiya da ibadar mu.
Ibraniyawa bai bar wani dama a rage girman Yesu ko a mai da shi kamar yadda mutum yake so ba. Shi ne walƙiyar ɗaukakar Allah, da ainihin halayyar Allah (Ibraniyawa 1:3) Mai-riƙe da komai bisa ga maganar ikon Sa. Shi ne madawwamin Ɗa, wanda ke gaba da mala’iku, Mai-Girma gaba da Musa, Shi ne Babban Firist Mafi-Girma na ƙarshe, wanda ya miƙa Kansa sau ɗaya tak domin duka, a matsayin hadaya. Shi ne yake gaba da komai dangane da dukan abubuwa, daga kan mala’iku har zuwa waɗannan muƙamai masu ɗaukaka wadanda Ubangiji da Kansa ya kafa a cikin tsohon alƙawari― Su annabawa, da firistoci, da sarakuna.
Ubangiji Yesu Kristi shi ne ainihin Zahiri na sabon alƙawari, wanda kamar yadda muka gani yana da fifiko da kyau gaba da alƙawarin da ke tsoho (Ibraniyawa 7:22). Rayuwa ta Krista, kamar yadda Ibraniyawa ya nanata, ba ruhaniya ta haka kawai ba ce, tsayayyar amintacciyar biyayya ce ga wannan Ma-daukaki Kristi, wanda ke fitowa daga dangantaka ta al’ajibi tare da Shi. Domin haka, ya kamata Shi ya zama abin ƙaunar mu, Shi ne madogaran begen mu, gare Shi bangaskiyar mu take sa ido. Sa’adda ka karanta Ibraniyawa, Sai ka ga ɗaukakar Yesu Kristi.
3. Ibraniyawa na da muhimmanci domin fahimtar tauhidin-Ikklisiya.
Wannan fahimta na tauhidin-ikklisiya, wanda kusan kamar masu karatu na zamanin yau ba su san shi sosai kamar yadda su ka san tauhidin-Kristi ba, da kuma yadda Ibraniyawa ya nanata batun alƙawari, duk bai hana shi kasancewa da muhimmanci ba. Marubucin Ibraniya ba wai ya yi waiwaiye ne kawai ya dubi tsara da suka yi tafiya a jeji don nuna wata faruwa a tarihi kawai ba ne; Ya gano zahirin kasancewar ikklisiya da ainihin ta cikin wannan yanayi na jeji.
Wannan ainihin ba kwantanci bane; ainihin haka ne; a zahirin gaskiya ikklisiya ita ce ci-gaba na sabon alƙawarin wannan tafiyar-masu-bi (pilgrimage).
Waɗannan kalmomi na tafiyar-masu-bi tana nan a ko’ina cikin littafin Ibraniyawa: “Gama a nan ba mu da madawwamin birni, amma muna biɗan birni da ke zuwa” (Ibraniyawa 13:14). Marubucin ya ƙarfafa masu karatu―waɗanda suka fuskanci jaraba na ja da baya zuwa ga jin daɗi da samun tabbas da ke cikin tsarin tsohon alƙawari―da su jimre kamar baki wanda suna kan hanyar su ta komawa ƙasar su ta ainihi.
Babu wurin da wannan tauhidin-ikklisiya ya fi bayyanuwa sosai kamar yadda yake a sura 3 da 4. An gargaɗi ikklisiya da cewa, kada ta taurare zuciyar ta kamar yadda da suka yi tawaye (Ibraniyawa 3: 7-8). Wannan tsara sun mutu a jeji saboda rashin gaskantawa. Ibraniyawa na haɗa tsattsauran gargadin da ke cikin ta kafaɗa-da-kafaɗa da matuƙar ƙarfafawar ta. Alƙawarin nan na shiga hutun Allah yana nan (Ibraniyawa 4:1), kuma ana samun wannan hutu a cikin Kristi, Babban Firist din mu Mafi-Girma, wanda ke tausaya mana cikin kasawar mu ( Ibraniyawa 4:15). Ikklisiyar ita ce kenan al’umma ta alƙawari wadda ke ɗauke da alama ta jimiri, da ibada, da kuma bege mai duban nan-gaba. Ta taru ta haɗ a wurin Yesu cikin jeji, da samun ciyarwa daga Kalmar Sa, tare da tafiya zuwa birnin Urshalima ta Sama.
Amma dole ne mu zurfafa fiye da haka. A cikin dukan Littafi Mai Tsarki, Ibraniyawa shi ne ya fi bamu kyakkyawan bayani na hoton martabatar ibadar Sama, kuma wannan ma ya ƙara haske ga tauhidin mu na ikklisiya. A sura na 12, marubucin ya kawo kwatancen bambanci tsakanin Dutsen Sinai da Dutsen Sihiyon zuwa ƙarin bayyanuwar ta. Ya ce ba mu zo ga tsoratarwa da ke Sinai ba, amma ga Sihiyona, “Birnin Allah Mai-rai, Urshalima ta Sama.” Kuma wanene ke tare da mu a wurin? “Rundunar mala’iku da ba a ƙidayuwa,” “taron Ɗan fari, Allah, alƙalin kowa,” kuma ga “Yesu, matsakaici na sabon alƙawari” (Ibraniyawa12:22:24). Wannan ba kawai hoton abin da ke zuwa nan gaba ba ne. Zahiri ne da ke faruwa a zamanin yau. Ikklisiya― a duk lokacin da ta taru domin ibada― za ta tattare zuwa cikin wannan taro na Sama. Ikklisiya mai gwagwarmaya tana haduwa da ikklisiya mai nasara domin yin taron tunawa na alkawari, wanda aka kafa bisa jinin madawamin alkawari. (Ibraniyawa 13:20). Sa’adda da kake karanta Ibraniyawa ka lura da ɗaukakar ikklisiya.
Karanta Ibraniyawa, da sa ido a lura da waɗannan jigogi uku, ba wai zai taimake ka fahimtar saƙon wannan littafi ɗaya shi kaɗai ba, amma har da sauran litattafai sittin da biyar.
An fara buga wannan labarin a shafin yanar gizon Ministirin Ligonier Blog. [Blog ɗin Ministirin Ligonier]


