
Abubuwa Uku Da Ya Kamata mu Fahimta Game Da Ibraniyawa
18/06/2026Yadda Za A Karanta Su Zaburan Hawan Zuwa Gaban Allah
Su Zabura na haurawa, shi ne sunan zabura goma sha biyar(120-134) da suka bayyana a Littafi na Biyar na (Psalter) littafin da ke ɗauke da waɗannan zabura. A matsayin zaburan haurawa, ko “zuwa sama,” wannan tarin zabura jeri ne da ake son rairawa sosai, a yadda ya kasance ga maza da matan Is’raila a lokacin da suke tafiya ta zuwa Urshalima domin tafiyar su ta ziyara na bukin ƙetarewa, da na makonni, da su alfarwar( dubi Fitowa 23:14-17; Maimaitawar Shari’a 16:16).
Kamar yadda ya kasance ga kakannin mu cikin bangaskiya, mu ma muna tafiyar masu-bi. Tafiyar mu ta ɗauke zuwa bi ta cikin wannan duniyar zuwa sabuwar Urshalima. Bisa wannan hanya mai wuya da matuƙar hatsari, mai-zabura ya tanada mana jagoranci mai hikima da ingantaccen kosarwa na ruhaniya.
Idan ya kamata waɗannan zabura su taimake mu cikin tafiyar mu ta masu-bi, to, ya ya ne ya kamata mu karanta su? Akwai tsararrun hanyoyi biyar da za su taimaka mana mu fara.
1. Karanta kowane zabura sau da dama sannan ka tsara takaitacen tsarin ta
Tun da wadannan zaburai wakokin Ibranci ne, ya kamata ka fahimci yadda ake karanta irin wannan rubutu. Abubuwa kamar yadda layukan suke kama da juna da kuma yadda suke haduwa za su taimaka maka ka fara fahimtar ma’anar kowace zabura. Domin samun ƙarin bayani game da waɗannan ƙa’idoji, dubi taƙaitaccen bayani na Matthew H. Patton a kan “How to Read Hebrew Poetry.”
2. Koyi gane da muhimmancin da hotunan misalai da ke bayyana a cikin wadannan Zabura.
Sa’adda kake fassara wani misali, dole ne ka amsa tambayoyi uku. Na farko, mene ne batun da ake tattaunawa a kai? Na biyu, wane misali ne mai-zabura yayi amfani da ita domin bayyana batun? Na uku, mene ne wurin dangantaka da ke tsakanin batun da kuma misalin?
Akwai muhimman misalai biyu da suka bayyanu a Zabura 133, wadda tarayya ta zumunta jama’ar Allah shi ne jigon ta. Misali ta farko ita ce Mai:
Duba, abu mai kyau ne mai daɗi kuma
Yan’uwa su yi zama tare cikin tarayya!
Yana kama da man ƙanshi mai-daraja a kai,
wanda yake gangara zuwa gemu,
wato gemun Haruna,
Ya gangara har zuwa wuyan rigunan sa! (Zabura 133:1-2)
Idan zumunta tare shi ne batun, sannan mai shi ne misalin, to ina ne wuri na kamanta su? Shi man da Dauda ke nuni da shi a nan, shi ne mai shafaffen mai-tsarki (Fitowa:30:22-38). An yi masa turare matuƙa kuma yana barin ƙamshi mai daɗi. Idan jama’ar Allah suka yi zumunta tare suka zama daya yana haifar da ƙamshi da yanayi mai gamsarwa.
Misali ta biyu ita ce raɓa:
Yana kamar raɓa ta Hermon,
Wanda kan sauka bisa duwatsun Sihiyona!
Gama daga can Ubangiji ya umurta albarka,
Rai na har abada. (Zabura 133:4)
Kamar dai yadda raɓa ke wartsakarwa da sabunta ciyayi, haka masu-bi sukan sami wartsakarwa na sabuntawar ruhu sa’adda suke ɗauke da zuciya da tunani ɗaya tare domin aikin Allah.
3. Karanta wannan zabura a matsayin wahayi na Yesu Kristi.
Tsararrun hanyoyin jagora biyu na farko suna buƙatar mu lura mu sa hankali ga fasaloli na adabin kowane zabura. Ka’ida ta uku kuma tana juya hankalinmu daga adabi zuwa tauhidi Yesu ya ce, “Dukan abin da aka rubuta a kaina a cikin Attaurar Musa, da Annabawa, da Zabura, dole a cika su (Luka 24:44). Waɗannan Zabura a kan Kristi ne. Yawanci masu karatu basu cika samun wahala wajen gane hakan a Zabura ta 1 ba, domin Yesu Shi ne Mutum mai albarka na Kalmar. A Zabura ta 22, Shi ne Wanda aka yashe Shi. Shi ne Makiyayi Mai-Kirki a Zabura ta 23.
Amma a ina za mu iya ganin Yesu cikin su Zabura na hawan Sama? Muna samun shi a hanyar zuwa Urshalima yana raira waɗannan zabura a matsayin mai-bi amintaccen matafiyi. Tun daga shekara goma sha biyu, da ya fara zuwa Urshalima domin Idin Ƙetarewa ( Luka 2:41-51, Sau da dama Mai-Ceto ya aiwatar da bukin mai-bi Matafiyi ( dubi Yahaya 2:13; 6:4; 7:1-24; 13:1). Da lokacin giciye Shi ya kusato, Ubangiji Ya ɗauki niya don tabbatar da hanyar Sa zuwa Urshalima domin Bukin Ƙetarewa (Luka 9:51). Shi matafiyi-mai-bi ne da ya dage ya nace, duk da cewa ya san Amincin Sa zai kai shi ga shan tsananin wahala da kuma mutuwa (Luka 9:21-22). Sa’adda kike ko kake karanta waɗannan zabura, Ka kanka ko yaya Yesu ya raira su, da kuma yaya za su jagorance ka ga raira waƙa a kan Yesu.
4. Bayan ka fahimci yanayin zabura, sai a koma ga yadda za a yi amfani da ita.
Ka’ida ta hudu tana barin adabi da tauhidi, tana mai da hankali kan amfani da shi a rayuwa Saka kanka a matsayin ɗan Isra’ila da ke tafiya kan hanya zuwa ƙasa mai tsarki, sannan ka tambayi kanka waɗannan tambayoyi:
• Menene ma’ana a gare ni in zama mai-bi amintacen mai tafiya zuwa Sabuwar Urshalima?
• Ya ya zan iya bi in yi nasara bisa Kalubalen da nake fuskanta? (dubi Zabura 121:1)?
• Yaya fata da farin cikin ibada ya kamata su kasance a rayuwata?
5. Koyi yadda za ka fahimci rawar jama’ar Allah tare da juna a cikin wadannan zabura.
A lokacin da Isra’ilawa suka yi tafiya zuwa Urshalima domin biki, sun tafi cikin ƙungiya-ƙungiya. Maryamu da Yusufu ba su damu ba da suka fara rasa Yesu a hanyar dawowa zuwa Nazaret daga wurin Bukin Ƙetarewa, domin sun zaci cewa Yana tare da sauran cikin taron jama’a da ke takawa zuwa arewa (Luka 2:43-44). Duk da cewa dukan mu masu-bi ne da ke tafiya, amma ba mu kaɗai muke wannan tafiyar ba. Saboda haka, dole ne mu ƙarfafa juna (Zabura 122:1), mu damu da lafiyar da kuma jin dadi dukan waɗanda suke tafiya tare da mu (Zabura 122:8), mu fahimci cewa dukan mu muna fuskantar tsanani (Zabura 123:2-4), sannan mu koyi jin matuƙar daɗi da farin ciki a wannan zumuncin kasancewa tare (Zabura 133)
An wallafa wannan talifi ne asali a dandalin Ministirin Ligonier Blog. [Blog ɗin Ministirin Ligonier]


