Yadda Za A Mangance Tsananin Gajiya Aikin Bishara

09/06/2026

Yadda Za A Mangance Tsananin Gajiya Aikin Bishara

09/06/2026

Ta’aziyyar Allah a cikin Rashin Ɗa Ko ‘Ya

A wannan ɓangare na rayuwar duniya, ba a yi wa Krista alƙawarin lafiya da arziki, da kuma farin ciki ba. Abin baƙin ciki na gaske a wannan rayuwa na duniyar da ta lalace, shi ne cewa, kowannen mu zai fuskance rashi da dama, kuma iri daban-daban: lafiyar mu, ko aiki, ko dangantaka, ko kuma mafi muni fiye da kowanne― rasa wata ko wani ƙaunatacce namu. Sa’adda muka fuskanci irin waɗannan abubuwa, yakan zama da wuya mu iya ganin komai sai dai wannan rashin shi kansa. Yana iya lulluɓe mu gaba ɗaya ta yadda tsananin baƙin ciki zai mamaye komai, har ma da dukkan gaskiya- mai ba da rai da ke Littafi Mai Tsarki.

Na fuskanci irin wannan yanayi sa’adda na haifi ‘ya ta Leila babu rai, na haife ta sati ɗaya kafin ranar da aka bayar na haihuwar ta. Na gigice gaba ɗaya saboda firgitarwa na rashi da ya same ni: Jaririyar da na yi marmarin zuwan ta, ta mutu; ba zan sami damar ciyar da ita ba, ko saka mata tufafi ba, ko kulawa da ita ba. Ɗa na Ben, ya ci gaba da kasancewa ɗan mu guda ɗaya tak, mai yiwuwa ba zan sake haihuwa ba; an binne ‘ya ta a kabari; haka nan ɗaya bayan ɗaya, na ci gaba da gani a cikin zuciya, ina juyayi kan waɗannan munanan gaskiya, daga wannan zuwa wancan. Amma da na kafa idanuna a kan wannan rashi da waɗannan abubuwa da ya ƙunsa, sai na daina duban Wanda Shi kaɗai ne zai iya bani ta’aziya daga wannan baƙin ciki nawa, ya iya kawo haske ga duhu na.

Marubuciyar waƙar nan Helen Lemmel ita ta san mafita daga wannan matuƙar tsanin damuwa: (fassara da Hausa)

Juyo idanu zuwa ga Yesu,

Zuba ido gaba ɗaya kan fuskar Sa mai al’ajibi,

Haka kuwa abubuwan da ke duniya, za su yi ta dushewa su ɓata,

Cikin hasken ɗaukakar Sa da alherin Sa.

A lokacin da na juyo idanu na zuwa ga Yesu, sai ya zamana wannan rashi na ‘ya ta, cikin ban mamaki ya dushe sa’adda hasken Sa ya haskaka duhun. Kafa idanun mu gare Shi ba wai ya kasha zafin da nake ji bane, amma ya kawo mani matuƙar ta’aziya a cikin tsananin.

Mai-Ceto Mai Kulawa

Lokacin da na juya ga Yesu cikin yanayin rashin ɗiya ta, sai na haɗu da Mai-Ceto wanda ke cike da tausayi. A Littafi Mai Tsarki a cikin litattafan Wasiƙu, an bayyana yadda zuciyar Yesu ta ke da tausayi ga raunanan mutanen da suka taɓa ɗanɗana ire-iren rashi masu yawa. Ɗaya daga cikin kyawawan misalai na irin haka shi ne, lokacin da wani mutumin da ke ɗauke da cutar kuturta ya roƙi Yesu don ya tsarkake shi. Markus ya rubuta cikin wasiƙar sa: “ Da tausayi ya kama Yesu, Sai ya miƙa hannun Sa, ya taɓa shi, ya ce masa, ‘Na yarda, ka tsarkaka’” (Markus 1:41). Wannan mutumin ba shi da tsarki bisa ga dokokin firistoci ( Leviticus 13), don haka ana hulɗa da shi a matsayin wanda aka kora daga cikin mutane, an ware shi daga sauran mutane, da rata. Amma Yesu Ya ji tausayi, Ya miƙa hannun Sa Ya kawar da wannan ratar da ta ware shi, ya kuma taɓa shi. Allah kaɗai ya san tsawon lokacin da mutumin nan ya taba samun tabin na wani?

Litattafan Wasiƙu sun nuna mana misalai dayawa na yadda Yesu yake taɓa rayuwar waɗanda ke ɗauke da nauyin kaya da kuma karaya a wannan duniya da ta lalace. Cike da tausayi ne, Yesu ya bi macen nan da ɗan ta tilo ya mutu ( Luka 7:11-15), da marasa lafiya (Matiyu 14:14), da waɗanda ke cikin yunwa (Matiyu 15:32), da makafi (Matiyu 20:30-34), da waɗanda ake tsanantawa, da marasa ƙarfi (Matiyu 9:35-36). Idan muka dubi waɗannan misalai, ba za mu ga Mai-ceton da ba ya jin komai game da mutane da ke shan wahala ba, amma said ai Mai-Ceto ne da ke “miƙa hanuwan Sa” gare mu cikin tausayi.

Mai-Ceto Mai Kuka

Kusan  babu wani wuri da ke nuna taushin zuciyar Yesu kamar yadda aka bayyana a aya mafi gajarta duka cikin Littafi Mai Tsarki: “ Yesu ya yi kuka” (Yahaya 11:35). Sa’adda ya isa gidan da ake zaman makoki wurin da abokin Sa Li’azaru ke kwance matacce, Yesu bai yi kuka sama-sama na ‘yar ƙwayar hawaye ɗaya ba―ya yi kuka ne matuƙa. Duk da cewa ya san zai kira Li’azaru ya tashe shi da rai, amma Ya ji baƙin ciki da ɓacin rai mai nauyi a zuciyar Sa.

Bayan da aka haifi Leila babu rai, na yi kuka sosai fiye da yadda na taɓa yi, amma na sami ƙarfafawa a sannin gaskiyar cewa, Shi Mai-Ceto na ma ya yi kuka a fuskar mutuwa. A sharhin da John Calvin ya yi na wannan aya, ya rubuta cewa, “ Yana (Yesu) matuƙar jin tsananin mu kamar Shi Kansa ne ke cikin wahalar.” Cikin rashi da ka fuskanta ko na fuskanta, Ubangijin mu Yesu ba ya jin daɗi a lokacin baƙin cikin mu. Shi ne Kalma da ya zama Jiki wanda ya ji tsananin zafin baƙin ciki a ƙirjin Sa da hawaye a kumatun Sa.

Mai-Ceto Mai Nasara

Sannin cewa Yesu ya damu da mu, yana kuma kuka, abu ne da ke ta’azantarwa a lokacin rashi, amma  wannan kaɗai bai isa ba. Domin kuwa da mene ne amfanin a ce Yesu Ya kasance da mu a lokacin shan wahala da bakin ciki ne kaɗai, idan a ƙarshe, Ba zai yi nasara mana a kan waɗannan abubuwan ba? Idan Yesu ba Mai-nasara bane, to lallai gaba ɗaya ma, Shi ba mai ta’azantarwa bane. A lokacin da muke cikin tsananin wahala, ba wanda zai tausaya mana kadai ne muke buƙata ba ― muna buƙatar  Mai-Ceto.

Ba wai Yesu Ya zo don ya rufe jin zafin mu da wani bandeji bane: Ya je tushe na dalilin duk shan wahalar mu―mai suna, zunubi. “Shi Kansa ya ɗauke zunuban mu a kan gungume” domin ya juya la’anar da faɗuwa ta jawo (1Bitrus 2:24). Kafin zunubi ta watsa mummunan ƙazanta a kan abubuwa duka, ai babu babu wani asara. Babu kuka, babu takaici, babu karayar zuciya, babu mutuwa.

Sa’adda Yesu ya kira Li’azaru daga matuwa zuwa rai, Yana nuna mana abin da Ya zo Ya yi ne: “Don Ya hallakar da mai ikon mutuwa, wato Ibilis,” (Ibraniyawa 2::14). Da yake Yesu Ya yi nasara  bisa mutuwa kuma aka tashe shi zuwa rai a rana ta uku, Ya ba mu sabon bege na wata duniya mai zuwa, wadda a cikin ta dukan baƙin ciki da nauyin zuciya za su tsere gaba ɗaya, duniya wadda mutuwa da rashi ba za su kasance ba.

Mai-Ceto Mai Ta’azantarwa

A lokacin da na sami bayanin cewa Leila ta mutu a cikin cikina, na nutse cikin wani bakin ciki mai tsanani da ya kusan cinye ni. Amma da na sa idanuna ga Yesu, Mai-Ceto da Ya damu, Yake kuka, Ya kuma yi nasara cikin duniya mai zunubi, da shan tsanani, da baƙin ciki, sai na sami ta’azantarwa―wadda ita ce kaɗai nake da ita cikin rai da cikin mutuwa. Da na juya idanuna zuwa gare Shi, cikin ikon Allah, sai rashi na, “ya dushe dalilin kasancewar hasken ɗaukakar da alherin Sa.”

Ya rai, ka gaji ne kuma kana damuwa,

Ba ka ganin wani haske a cikin duhu?

Akwai haske idan ka dubi Mai-Ceto,

Da rai a yalwace matuƙa, kuma kyauta.


An fara buga wannan labarin a shafin yanar gizon Ministirin Ligonier Blog. [Blog ɗin Ministirin Ligonier]

Jackie Gibson

Jackie Gibson

Jackie Gibson ta yi aiki tare da mijin ta, Jonathan, a Westminster Theological Seminary na Philadelphia. Ita uwa ce mai ‘ya’ya huɗu, kuma ta wallafa littafi You Are Still A Mother: Hope For Women Grieving a Stillbirth or Miscarriage.