
Samun Bege Cikin Rashin Lafiya
02/06/2026
Yadda Za A Mangance Tsananin Gajiya Aikin Bishara
09/06/2026Ta Yaya zan Magance Matsanancin Damuwa?
Idan bege shi ne marmari na rai, to, gajiya da azabar rayuwa shi ne marmarin a kai ƙarshen ta. Kamar yadda ya kasance wa Iliya a ƙarƙashin bishiyar kwakwa (1Sarakuna 19:1-10), da Ayuba, sa’adda ya la’anci ranar da aka haife shi (Ayuba 3), ko kuma Bulus, wanda nauyin tsananin wahala ya sa shi gajiya da azabar rayuwar sa (2Korintiyawa 1:8), masu-bi da aka haifa zuwa rayayyar bege za su iya jin kansu ɗaure cikin tarko a lokaci tsananin azabar rayuwa.
Mai-zabura ya yi kuka ya ce,
Dukan raƙuman ka na ruwa da ambaliyan Ka sun sha kaina. (Zabura 42:7)
Ayuba ya yi kuka ya ce, “Raina ya mutu, kwanaki na sun ƙare.” (Ayuba 17:1). Waɗannan ba kawai iya kwalyar harshe na mawaƙi bane―nuni ne na ainihin abin da ke faruwa, na yadda tsananin azaba kan iya tura mu cikin matuƙar taƙura fiye da abin da ƙirar halittar mu kan iya ɗauka.
Gajiya da azabar rayuwa ba yana zuwa ne ga waɗanda suka yi kama da shan wahala ba, wato: masu damuwa, masu rashin gamsuwa, ko waɗanda ba su da fahimta sosai. A’a ba haka bane, ko adilai irin su Charles Spurgeon, da Martyn Llyod-Jones, da kuma John Bunyan sun ɗanɗana yanayi na matuƙar ɓacin rai da azaba. Yanayi ne da ba ya nuna wariya bisa matsayin zuciyar mutum ko girman sa a ruhaniya.
Mutumin da ke cikin tsananin azabar rayuwa yakan buƙaci abu ɗaya ne kaɗai: sauƙi daga yanayin. Yanayin wannan gwagwarmaya yana say a ji kamar ya sha kashi gaba daya, kuma rayuwa ba ta da ma’ana, ba tare da wata mafita ko hanyar tsira ba. Mai-zabura ya bayyana kamar haka:
Na faɗa cikin ruwaye masu-zurfi,
Inda rigyawa sun sha kai na. (Zabura 69:2)
Kamar tafiya cikin tekun da yake bori, yakan zama kamar ruwan zai cinye mu a fili, nesa da wurin iya samun taimako.
Ko dai a hankali abin yana faruwa, ko kuma kwatsam zuciya da rai sun kai ga iyaka, matsanacin damuwa yana bata yadda mai bi yake ganin bege, kuma yana rage karfin jiki, tunani, da rai. Saboda haka, warkewa yana nufin a dawo da fahimta da karfi, yanayin da muke dogara ga Almasihu cikin rauninanmu, mu kuma nuna bangaskiya ta hanyar kananan matakan biyayya, hakuri, de bege wadanda ke karya karfin damuwa.
Tsayar da yawan Tunani mara Amfani
A cikin littafin The Pilgrim’s Progress na John Bunyan, lokacin da Kirista ya wahala a gidan kurkukun Giant Despair, duhun ba rudi ba ne; abu ne nag aske da ake ji, mai Takura numfashi. Haka ma, mu kan ya kasancewa cikin mawuyacin hali sosai, amma tsananin azabar rayuwa zai sa mu yi ta zagayawa cikin wadannan abubuwa ba karewa, yana kuma rufe begenmu cikin Almasihu. Kubutarwar Kirista ta zo ne ba domin duhun ya yanke ba, amma domin ya tuna ya yi amfani da maƙullin alƙawari wanda ke aljihun sa.
Maganar Allah tana bukatar ta rika katsewa tare da mu, ta gyara tunaninmu akai-akai. Sa’adda muka ji kamar an yi banza da mu, sai mu tuna fa cewa Ya yi alƙawarin ba zai taɓa barin mu ko Ya yashe mu ba. Sa’adda muka shiga yanayi mai zurfi da ya yi kamar Allah ba zai iya kaiwa ya fitar da mu ba, mu tuna fa cewa, Ya sauka zuwa jihannama ita kanta. Sa’adda ba ki ko baka san abin da za ki ko za ka yi addu’a a kai ba, ka sani cewa Ruhu Mai-Tsarki yana nishe-nishe a madadin mu.
Kulawa Da Jikin
Sa’adda Iliya ya ji wahalar rayuwa ta mamaye shi, Allah ya tanada masa abinci, da hutu, da kuma kasancewar Sa. Mu halittu ne da duk wani abu namu yake da ƙarshe, yake buƙatar sake sabuntawa a duk lokacin da ya lalace. Kenan, rayuwar tawali’u na buƙatar motsa jiki kullum, samun issasshen barci, ciyar da jiki da abinci da ya kamata, samun isasshen hasken rana, neman taimako daga ma’aikatan kiwon lafiya, mu kuma tabbatar cewa muna hutu, maimakon mu yi ta tura kan mu cikin ayyuka daban-daban. Ko dayake kulawa da buƙatun mu na jiki zai iya zama kamar ba shi da muhimmanci ko kuma aikin banza ne, to, amma a gaskiya nuna biyayya ne ga girmama iyaka da muke da ita a tsarin halitta da aka yi mu, da kuma amincewa da tanadin Allah.
Neman Taimako A Waje
Kamar yadda ɗabi’ar neman tsira takan mamaye mutum, haka matuƙar tsananin azaba na rayuwa yakan mamaye kowane ɓangare na wanda ke cikin wahalar, ya sa shi mai da hankali ga kansa kaɗai, da kuma janyewa daga cikin mutane. Abin da zai karya ikon wannan yanayi mai karkata tunani shi ne, ba da lokaci da kuma karɓan lokaci na kulawa da kasancewa tare da wasu. Yana da kyau ka bari wasu su san halin da ka ke ciki, ba domin ka karɓi ƙauna kaɗai ba amma don kai ma ka nuna ƙauna ma wasu ta hanyar hira da ba su lokaci. kananan ayyukan kulawa suna sa mu fifita wasu, kuma suna zama wata hanya mai karfi ta yaki da yawan mayar da hankali ga kanmu kawai. Yi addu’a domin waɗanda da ke kusa da ke ko kai, rubuta masu ɗan saƙo na ƙarfafawa, hirar da za ku yi ma ta kasance game da su ne―duk waɗannan hanyoyi ne da ke ‘yantarwa, su sake mayar da hankalin mutum zuwa ganin yadda ya kamata, sannan ta koma ga Allah da kuma maƙwabci na kusa.
Kuɓuta ta Hanyar Ayukan Yau Da Kullum
Idan tsananin azaban rayuwa ya janye mu daga muhimman abubuwa na rayuwa, sai mu rungumi abubuwan da ke akwai su zama hanyar kuɓutar mu. Ayukan da muke yi na yau da kullum, duk da cewa wasun su ƙanana ne, amma sukan kawo oda. Ƙananan ayuka masu sauƙi, kamar tashi kowane safiya, yin wanki, da yanke ciyawa sukan zama mafita zuwa ga dawowar rayuwa a yadda ya kamata, da kuma samun dalilin ci-gaba da ita rayuwar. Ko da kuwa ƙoƙarin mu na kasancewa kamar mu robot ne, dagewa mu rungumi abin yi na gaba shi ma aiki ne na bege. Nuna aminci a ƙananan abubuwa (Luka 16:10) zai sake gina iyawar mu, da nanata ma’ana da manufa, da kuma canza abin da muka ɗauka ba komai bane ya zama hanyar kuɓuta.
Ƙarfafawa Ga Halitta
Sa’adda tsoro ya zo da girma, tunawa da ƙanƙancin mu in an kwatanta shi da Girman Allah da ikon Sa bisa kowa da komai yana kawo sauƙi. Shi ne ke riƙe da dukan halitta, har da mu. Tsananin azabar rayuwar Ayuba ta canza zuwa ibada sa’adda Allah ya bayyana halayyar Sa da girman ikon Sa na rike da komai, daga tsarin taurari da sauran halittun sararin sama, zuwa ƙofofin teku. Tafiya ana kallon hallittar Allah, da kwanciya ƙarƙashin taurari, da shuka furanni, ko kulawa da dabbobi―dukan waɗannan kyawawan abubuwa na halitta na ta’azantarwa da ƙarfafa mu, Yana kuma sake canzawa da gyara fahimtar mu a lokacin da Yake yi mana hidima ta hanyar halittun duniya.
Jimiri Tare Da Haƙuri
Sa’adda da duhu ya dage, kuma sauƙi bai samu ba, tuna fa cewa tafiya daga shan tsananin wahala zuwa bege yana buƙatar jimrewa. Wannan yana nufin samun lokaci da aminci. Zama cikin tashin hankali ba abu mai sauƙi bane, amma kuma rashin ƙarfi da buƙata sun zama sharuɗɗa zuwa ga koyan yin dogaro ga Kristi gaba-ɗaya. Ya gayyace mu ba ga yin tarayya cikin nasarar Sa da ikon tashin Sa daga matatu kaɗai ba, amma har ga tarayyar zumunta cikin shan wahalar Sa (Filbiyawa 3:10). Ka ci gaba da dagewa cikin wadannan tafiya ta dakyar na bangaskiya – domin su ne ainihin aikin alheri da ya shirya maka a wannan lokaci. Kada ka ji tsoron duhun. Ko dayake sun yi kamar ba za su kare ba, gaskiyar ita ce, ba da daɗewa ba [har sai] Allahn dukan alheri, wanda ya kiraye ku zuwa ga madawwamiyar darajar Sa cikin Kristi, Shi da Kansa zai sake raya ku, da ba ku tabbaci, da ƙarfi, Ya kuma sake kafa ku (1 Bitrus 5:10). Duhun na iya ci-gaba da ƙaruwa, amma ba za su iya karɓe waɗanda aka ƙwato daga mulkin duhu, aka canza masu wuri zuwa mulkin Ɗan ba (Kolosiyawa 1:13).
An fara buga wannan labarin a shafin yanar gizon Ministirin Ligonier Blog. [Blog ɗin Ministirin Ligonier]


