Ko Allah Yana Kula Da Gaske?

28/05/2026

Ta Yaya zan Magance Matsanancin Damuwa?

04/06/2026

Ko Allah Yana Kula Da Gaske?

28/05/2026

Ta Yaya zan Magance Matsanancin Damuwa?

04/06/2026

Samun Bege Cikin Rashin Lafiya

A ranar cikar shaker biyar na dana, ina zaune a wuri mai nisa, kusan mil ɗari shida, a wani asibitin kula da masu ciwon daji(cancer), ga igiyoyin jini da na magunguna jaka daban-daban an saka mani suna shiga jiki na. Ina fama da wani irin ciwon daji na dabam, don haka buƙata ta ta neman taimako ta kai ni nesa da miji na da ƙananan ‘ya’ya na uku har, na tsawon watanni da dama.

Duk bege da nake da shi a duniyar nan yana fuskantar ƙalubale. Koshin lafiyata ya tafi, kuma ta tafi da ƙarfi na, da gashin kai na, da Kuma makomar rayuwata da na dauka za ta kasance yadda na tsara. Maimakon kulawa da iyali na, ya zama kwanaki na suna cike da zama ina jira a ɗakunan asibiti, da kare-karen jini, da gwaje-gwaje, da yawan gajerun barci. Na rasa ganin lokutan kyawawan abubuwa da ke faruwa a rayuwar ‘ya’ya na, kuma ban ma sani ba ko har zan rayu in sami ganin wasu irin waɗannan muhimman lokutan ba.

Duk a cikin halin jarabci na ciwon dajin nan, da kai wa ga samun nasara kan sa, na kasance da buƙatar bege wanda zai kafu da ƙarfi cikin wannan halin rayuwa mai hawa da sauka na shan wahala domin lafiya ta. Saboda jinƙai da alherin Allah, muna da bege na ƙwarai wanda muke iya riƙewa wato: Ubangiji da Mai-Ceton mu, Yesu Kristi. Bitrus ya yi rubutu cikin wasiƙar sa ta farko  zuwa ga Kristoci masu shan tsanani kamar ni da kai, domin tabbatar mana cewa, rayayyar begen mu cikin Kristi ba za ta girgiza ba wai ko don saboda jarabobin duniya, kuma za ta jure har zuwa ga ƙarshen ta mai ɗaukaka.

Rayayyen Begen Mu

Bitrus ya fara wasiƙar sa da labari mai daɗi na rayayyen begen mu:

Albarka ta tabbata ga Allah da kuma Uba na Ubangijin mu Yesu Kristi! Wanda ta wurin tsananin jinƙan Sa ya sake haihuwar mu, domin mu yi rayayyen bege ta wurin albarkacin tashin Yesu Kristi daga matatu. (1 Bitrus 1:3)

Mu ba waɗanda Mai-Ceton su yake cikin kabari har yanzu bane. Ya tashi daga matattu, yana shelar nasara bisa zunubi da mutuwa (1Korintiyawa 15:54-57). Gaba da haka ma, tashin Sa ya zama soma taɓi ne na gagarumin labarin tashin Sa daga matattu. Shi ne nunan-fari na tashi daga matattu, kuma duka waɗanda ke nasa za su rayu har abada, domin shi ne rayayyen begen mu. (1Korintiyawa 15:20-23).

Sa’adda muke shan wahala na yanayin ciwo mai tsanani, babu wuya mu gaji, ko mu karai. Tana yiwuwa mu rasa bege na cewa rayuwa za ta sake dawowa yadda take a da mai kyau. Cikin waɗannan lokuta na duhu, za mu iya rungume rayayyen begen mu, Mai-Ceton mu, wanda ya yi nasara bisa kabari. Muna da rayayyen bege domin muna da rayayyen Mai-Ceto.

Begen Mu Marar Girgizuwa

Ba wai an sake haihuwar mu ga rayayyen bege kaɗai ba, amma an sake haihuwar mu zuwa ga madawwamiyar gado, tsattsarka, marar ɓacewa, ajiyayya a Sama domin mu, wanda ta wurin ikon Allah ake tsare mu cikin bangaskiya zuwa ga ceton da za a bayyana a lokacin ƙarshe. (1 Bitrus 1:4-5)

Waɗanda ke na Kristi suna iya dubawa nesa, gaba da wahalolin wannan duniya zuwa ga gado mai ɗaurewa. Cuta da kan iya cinye jikunan mu kamar gobara ma ba za ta iya taɓa wannan ba. Wasu irin yanayi da kan fi ƙarfin mu ma ba za su iya rage madawwamiyar cikar sa da tsarkin sa ba. Babu wani abin da zai yi barazana ga abin da Allah ke ajiye wa a sama domin mu.

Ya ya muke iya sanin tabbas cewa a zahiri za mu karɓi wannan gado marar ɓacewa? Bitrus ya ce, ikon Allah shi ke jagorantar mu ta wurin bangaskiya. Mun karɓi wannan gado ta dalilin rahamar Allah, kuma muna riƙe da ita ta dalilin ikon Allah. Begen mu ba ya girgizuwa domin riƙon da Allah ke yi mana ba ya girgizuwa (Yahaya 10:27-29).

Begen Mu Mai-Ɗaukaka 

A lokacin da Bitrus ya yi rubutu dangane da wannan rayayyen bege marar girgizuwa, ba wai bai san jarabobin rayuwa bane. Amma duk da haka, Bitrus ya ƙarfafa mu da mu yi murna a lokacin da mu ke baƙin ciki saboda wahalolin:

Cikin wannan kuna murna, ko da yake na ɗan lokaci za ku yi baƙin ciki ta dalilin gwaje-gwaje iri-iri, wannan kuwa domin a tabbatar da sahihancin bangaskiyar ku (wadda ta fi zinariya daraja nesa, ita zinariya kuwa ko da yake mai ƙarewa ce, akan jaraba ta da wuta), za ta jawo maku yabo, da girma, da ɗaukaka a bayyanuwar Yesu Kristi. (1 Bitrus 1:6-7).

Alƙawuran Allah suna ɗaga idanun mu daga matsaloli na nan duniya zuwa ga madawwamiyar ɗaukaka. Ta dalilin aikin Allah a cikin mu, gwaji na wahaloli yana tabbatar da bangaskiyar mu ta zahiri ce. Sa’adda Kristi zai dawo, bangaskiyar nan da Allah ya rayar a cikin mu ta hanyar waɗannan jarabobi, zai “haifar da yabo, da daukaka da martaba”(1Bitrus 1:7). Wannan martaba na iya nufin martabar Kristi, martaba da muka samu tare da Shi, ko kuma duka biyun. Amma dai mun sani cewa rayuwar mu ta nan gaba tare da Kristi za ta kasance mai-ɗaukaka ce, kuma dalili kenan da za mu yi murna a cikin shan wahala a yau. Begen mu cikin Kristi tabbataccen mafaƙa ne a lokacin da tsanani ya mamaye mu, ko tsoro ya lulluɓe mu, ko kuma sauye-sauye da ke faruwa ga jikinmu da makomarmu sun matuƙar gajiyar da mu. Saboda rayayyen begen mu, marar girgizuwa, maɗaukakiyar bege, za mu iya cewa tare da Bitrus: “Yabo ya tabbata ga Allah da Uban Ubangijinmu Yesu Almasihu.” (1Bitrus 1:3).


An fara buga wannan labarin a shafin yanar gizon Ministirin Ligonier. [Blog ɗin Ministirin Ligonier]

Marissa Henley

Marissa Henley

Marissa Henley takan yi jawabai a tarurruka, kuma ita ce ta rubuta littafin Loving Your Friend Through Cancer And After. Tana rubuce-rubucen ta a MarissaHenley.com