
Ta Yaya zan Magance Matsanancin Damuwa?
04/06/2026Yadda Za A Mangance Tsananin Gajiya Aikin Bishara
Tsananin gajiya a lokacin aikin bishara abu ne da yake ta ƙaruwa a rayuwar yau da kullum a cikin aikin bishara ta gaskiya. Akwai dalilai da dama da suka sa fastoci da malamai masu tsoron Allah, waɗanda suke aikin bishara suke fuskantar tsananin gajiya. Ƙaruwar ƙiyayya duniya mai tsanani yana iya kashe gwiwa da baƙanta rai. Gaba da haka ma, yadda wasu masu kiran kan su masu-bi suka fi saurin amincewa da bin tsare-tsaren al’adu fiye da tsarin- Littafi Mai Tsarki yana kasancewa abu mai matuƙar kashe ƙuzari. Haɗe kuma da waɗannan yaƙe-yaƙe na ruhaniya, wasu bayin Allah maza da mata suna da wata tsarin tunani wanda duk wani ɗan ƙalubale, babba ko ƙarami, yakan mamaye su ya fi ƙarfin su.
A wannan ɗan gajeren bayani, ina so in mai da hankali kan baƙin ciki da gajiya da ya matuƙar taɓa tsarkakakkiyar mutuntaka ta Ubangiji Yesu Kristi. Ba wai ina cewa ya ɗanɗana tsananin gajiya a aikin bishara bane. Amma an bayyana mana Mai-Ceton mu a cikin Littafi Mai Tsarki a matsayin kwatanci na mutum mai Imani, bawan Ubangiji wanda ya kamata kowane mai aikin-bishara ya yi koyi da Shi. Riƙe da wannan a zuci, ina so in yi abubuwa biyu: Na farko, in haskaka gaskiyar ɗanɗana wahala da Ubangijin mu marar-aibu ya fuskanta, da jarabobi na aikin bishara da sukan kusa fin ƙarfi. Na biyu kuma, in sake haskaka naciyar miƙa wuya da Yesu ya yi sa’adda ya fukanci waɗannan wahaloli.
1. Yesu ya tuna kuma ya sani
Da farko, yi tunanin waɗannan kalmomi:
Ya ce mani, “Kai bawa Na ne ,
ya Israila, wanda za a ɗaukaka Ni ta wurin ka”
Amma Ni na ce, “Na yi wahala a banza;
Na ba da ƙarfi Na haka kawai ne, a banza kuwa.” (Ishaya 49:3-4)
A lokacin da nake koyarwa, ina yawan tambayan dalibai na cewa, “Wane ne ya furta waɗannan kalmomin?” Babu wani ko ɗaya da ya taɓa bani amsar da ta yi daidai. Wanda ya furta waɗannan kalmomi shi ne amintaccen bawan Yahweh marar aibu, Shi wanda a cikin Sa zai sami “ɗaukaka.” Waɗannan kalmomi sun fito daga bakin Ubangiji Yesu Kristi.
Waɗannan magana biyu, “haka kawai” da kuma “a banza kawai” suna tunatarwa mai zurfi. A harshen Ibraniyanci kalmar “haka kawai” ita ce tohu, kalma da ake samu a Farawa 1:2: “Duniya kuwa sarari (tohu) ce.” Banza kawai kuma ‘hevel’ kalmar da muke gani an jejjefa ta ko’ina cikin Littafin Mai-Wa’azi: banza ne, “banza ne sarai.” Gab da lokacin giciye shi, a sa’adda Mai-Ceton mu ya yi juyayin aikin Sa na bishara da manufar zuwansa, ya jimre wani lokaci na wahala don bishara da jikin sa kuma, amma bai kasance da zunubi ba. Adawar ta yi tsanani, kuma jikunan almajiran Sa sun mutu, sun karaya yadda Shi kaɗai ya ji nauyin baƙin-cikin da mai-zabura ya furta sa’adda ya rubuta cewa duhu ne kaɗai abokin sa (dubi Zabura 88:18).
Ya kamata kowane Krista ya sani, akwai buƙata kuma kowane mai aikin-bishara ya sani, cewa muna da Mai-Ceto wanda ya san tsananin baƙin ciki da matuƙar gajiya na bayin Sa, domin Shi Kansa ya ɗanɗan hakan. Aikin bishara cikin aminci da gaskiya yana da tsada ƙwarai. Yi tunani kan kalmomin mai-zabura sa’adda ya yi kuka ya ce:
Me ya sa nake bakin ciki haha?
Me ya sa nake damuwa kwarai?
Zan dogara ga Allah
Zan sake yi yabonsa, Mai Cetona, Allahna (Zabura 42:5)
Ya shiga zurfin ba wai don bai yi biyayya bane, amma domin yana begen yanayin da bawan Ubangiji, Yesu Kristi zai ɗanɗana.
Ainihin maƙasudin batun da nake nunawa shi ne: Sa’adda amintattun bayin Allah na gaskiya suka sami kansu cikin yanayi mai-zurfi, ruwayen rayuwa da na aikin bishara suna kai da komowa bisa tunanin su da zunkatan su (Zabura 69:1-2), lallai suna da Mai-ceto amintacce, wanda ya bi hanyar zurfin jigata da baƙin ciki. Ya san me aka halicce ka da shi, Ya tuna, kuma Ya sani cewa kai turbaya ne (Zabura 103:14).
2. Bangaskiyar Yesu Ta Jagoranci Ayukan Sa
Na biyu, yanzu yi tunani kan kalmomin da suke biyo baya:
Duk da haka shari’a ta tana wurin Ubangiji,
Sakamako na kuma yana wurin Allah na.(Ishaya 49:4).
Duk da cewa Ubangiji Yesu Kristi, Ɗan Allah marar zunubi, amintaccen Bawan Sa, ya ɗanɗana yanayi zuzzurfa na jarabobi a aikin bisharar da kuma tsananin ƙunci. Amma a haka ya kafa zuciyar sa mai-damuwa da tunanin sa cikin amincin Yahweh. Ya kasance da bangaskiya tsayayya kan alherin Allah, da alƙawarin Sa na sakamako don wahalolin Sa da azabar ƙunci da baƙin ciki. Gaskantawa kan alheri da kuma ƙaunar Uba na Sama lallai zai taimake mu ga yin nasara akan wannan guguwa, sannan mu ci gaba da tsayawa daram a sa’adda kome da ke kewaye da rayuwa yake wargajewa.
An buƙaci wasu bayin Ubangiji zaɓaɓɓu su yi tafiya cikin duhu, har cikin duhun da kamar babu ko haske. Yi tunani kan waɗannan kalmomi masu jan hankali a Ishaya 50:10:
Wanene daga cikin ku mai-tsoron ALLAH
kuma mai-biyayya da muryar bawan Sa?
Bari wanda ke cikin duhu, da ba shi da haske kuwa,
Ya dogara ga sunan UBANGIJI
Ya dangana ga Allahn sa
Ta hanyar Ishaya, Allah ya sake nanata mana cewa, tunawa da ko wanene Allah, yana ba mu madogara a lokacin da tsananin gajiya na aikin bishara yake barazanar wargaje rayuwar mu, da ɓatar mana da hankali har mu kasa yin aikin Ubangiji da na ikklisiyar Sa.
Wannan shi ne ainihin abin da Mai-Ceton mu ya ɗanɗana. Bangaskiyar Sa ga Allah ne ya kiyaye Shi daga fid da rai, da juya baya a sa’adda duk wani haske daga cikin Sa ya fice a lokacin da yake rataye, Shi kaɗai da aka yi watsi da Shi kan giciye na ƙwaluwa. Cikin matsayi na kaɗaicin Sa, Ya ci gaba da matuƙr riƙe bangaskiyar Sa ga Allah, “ Ya Allah Na, Ya Allah Na . . .” (Zabura 22:1; Matiyu 27:46; Markus 15:34). Duhu ya lulluɓe shi, amma bangaskiyar Sa ta haskaka da ɗaukaka cikin wannan duhun.
Kammalawa
Akwai dalilai dayawa da ke jawo tsananin gajiya a aikin bishara: ire-iren fama na mutum shi kansa, ko saɓani tsakanin iyali, ko matsaloli cikin ikklisiya, da rashin zaman lafiya a kasa, ko kuma rikice-rikice a duniya ita kanta. Ko da mene ne dalilan, Yesu ya ce wa duk wasu mutanen Sa, waɗanda ya saye su da jinin Sa, yake matuƙar ƙaunar su: Ku ba da gaskiya ga Allah―Uba wanda ke ƙaunar ku da madawwamiyar ƙauna, da Ɗan wanda ya ba da Kansa domin ku, kuma kullum a raye Yake Yana roƙo domin ku, da kuma Ruhu Mai-Tsarki da ke cikin ku don taimakon ku ( Irimiya 31:3; Romawa 8:26; Ibraniyawa 7:25). Ba da gaskiya ga Allah, kuma ku riƙe Shi matuƙa, kamar da yadda Mai-Ceton mu Ya yi.
An fara buga wannan labarin a shafin yanar gizon Ministirin Ligonier Blog. [Blog ɗin Ministirin Ligonier]


