
Shin Allah Yana Karɓar Ibada Daga Dukkan Addinai?
09/07/2026
Wane Alkawari Yesu Ya Bayar Kafin Hawansa Sama?
16/07/2026Kuduri don Rayuwar Kirista
A yau, za mu bincika wani nassi na sabuwar shekara daga ɗaya daga cikin wasiƙun Manzo Bulus. Wataƙila ka saba da shi, kuma wataƙila ma ka hadace shi. Amma ko da ba ka san shi ba, ina jin za ka iya tunawa da shi cikin sauƙi. ƙudurin Bulus ne ta kansa a Filibiyawa 3:10–14:
Ina so in san Kiristi da ikon tashinsa daga matattu da kuma zumuncin tarayya cikin shan wahalarsa, in kuma zama kamarsa a cikin mutuwarsa, yadda kuma ko ta yaya, in kai ga tashin nan daga matattu.
Ba cewa na riga na sami dukan wannan ba ne, ko kuma an riga an mai da ni cikakke ba, sai dai ina nacewa don in kai ga samun abin da Kiristi Yesu ya riƙe ni saboda shi. ’Yan’uwa, ban ɗauki kaina a kan cewa na riga na sami abin ba. Sai dai abu guda nake yi. Ina mantawa da abin da yake baya, ina kuma nacewa zuwa ga samun abin da yake gaba, ina nacewa gaba zuwa ga manufar, don in sami ladar da Allah ya yi mini na kiran nan zuwa Sama a cikin Kiristi Yesu.
A farkon wasiƙar Filibiyawa, Bulus ya nuna cewa matashin abokin aikinsa Timoti yana tare da shi. Bulus yakan faɗi wasiƙunsa ana rubutawa, kuma nakan yi mamaki ko ya ambaci Timoti ne saboda ya yi aiki a matsayin sakatarensa na wannan wasiƙar. Ta fara ne da kalmomin “Bulus da Timoti,” kuma ina mamaki ko ya yi wa ɗansa a cikin imani ɗan murmushi sa’ad da ya gaya masa ya rubuta sunan kansa.
Amma idan haka ne, na tabbata ƙwarai cewa sa’ad da Bulus ya zo ga wannan nassin, “Amma abu ɗaya nake yi,” wataƙila Timoti zai kalli Bulus da kallon mamaki da neman ƙarin bayani. Kuma idan Bulus ya tambaye shi ko ya faɗi abin da Timoti bai gane ba, wataƙila zai sami ƙarfin hali ya amsa: “Bulus, da gaske kake son in ce abu ɗaya kawai kake yi? Tun lokacin da na san ka, kana yin abubuwa da yawa a koyaushe, kuma a lokaci guda. Kai ne babban Manzon nan da ya zarce kowa wajen iya haɗa ayyuka dabam-dabam a lokaci guda. Kullum kana tafiya; kullum kana wa’azi; kullum kana addu’a; kullum kana ziyara; kullum kana ba da gargaɗi. Ban taɓa ganinka kana yin abu ɗaya kawai ba.”
Ina tsammanin Bulus zai mayar wa matashin abokinsa Timoti da murmushi ya ce: “Na gane abin da kake nufi, Timoti. Babu wanda ya san abin da nake yi da kuma yadda nake da ayyuka da yawa kamar ka. Amma kana bukatar ka fahimci cewa ba na cikin ayyuka masu yawa ne dabam-dabam ba. Ina cikin aiki guda daya ne a hanyoyi masu yawa dabam-dabam. Kuma duka waɗannan sun shafi sanin Ubangiji Yesu Almasihu ne da kyau, da tarayya cikin rayuwarsa, da kuma zama kamarsa. Wannan ne zuciyar al’amarin – ta wata hanya kuma shi ne sirrin—dukkan abin da nake yi, a kowace sa’ar farkawa da kowane aiki daban-daban. Dukkansu hanyoyi ne kawai daban-daban na yin wannan abu guda ɗaya.”
Sa’ad da nake ƙaramin yaro a ƙasar Scotland, a kowane daren jajiberin sabuwar shekara (Hogmanay, yadda ake kiranta), iyayena sukan gaya mini in je ɗakina in rubuta ƙudurori guda goma na sabuwar shekara don shekara mai zuwa. Idan na waiwayi baya, nakan yi dariya yanzu sa’ad da na tuna yadda na yi tsammanin yana da wuya in sami hanyoyi goma da nake bukatar in inganta kaina a kai. Ina zaton zan iya rubuta su cikin sauƙi fiye da haka a yau.
Amma idan kai Kirista ne, a gaskiya kana bukatar ƙudurin sabuwar shekara guda ɗaya kawai, kuma na Bulus zai zama babban taimako a gare ka. Musamman idan kai matashin Kirista ne ko kuma matashi, abubuwa kaɗan ne za su iya zama masu taimako a gare ka fiye da fahimtar cewa wannan ita ce hanyar da za ka sauƙaƙa kuma ka haɗa dukan sassan rayuwarka waje guda. Wannan ne zai ba ka jagora. Wannan ne zai taimake ka ka amsa babbar tambayar nan, “Me ya sa nake nan a duniya a zahiri?”
Kamar yadda ɗaya daga cikin tsofaffin fassarori ya bayyana shi,
Duk abin da nake buri shi ne in san Almasihu da ikon tashinsa daga mattatu, in yi tarayya cikin wahalolinsa, in kuma zama kamarsa, domin wata rana in kai ga tashin mattatu. (Filibiyawa 3:10–14).
Wani babban ƙudurin Sabuwar Shekara ne wannan! Abu guda ɗayan nan nake yi: Ina so in san Almasihu.
Asali, an wallafa wannan talifi ne a Shafin Yanar Gizo na Ligonier Ministries. [Blog ɗin Ministirin Ligonier]


