
Ya Ya Kammannin Tuba Yake?
17/12/2025
Menene Mafi Girma Cikin Dukkan Bidi’oji na Furotesta.
23/12/2025Menene Ma’anar Wanke Zunubi Da Kuma Kwantar da Fushin Allah?
Idan muna Magana game da bangaren sauya wa wani hukunci a cikin aikin fansar zunubi (atonement), kalmomi guda biyu masu zurfin man’ana suna yawan fitowa: kafara da gamsar da fushin Allah. Wadannan kalmomi suna haifar da muhawara iri-iri game da wacce daga cikinsu ya kamata a yi amfani da ita wajen fassara wata Kalmar Helenanci, kuma wasu Fassarorin Littafi Mai Tsarki sukan yi amfani da kalma na farko, wasu kuma sukan yi amfani da na biyun. Ana yawan tambayata in bayyana bambanci tsakanin kwantar da fushin Allah (propitiation) da kuma wanke zunubi (expiation). Matsalar it ace, ko da yake wadannan kalmomi suna cikin Littafin Mai Tsarki, ba mu saba amfani da su a cikin magana ta yau da kullum ba, don haka ba mu da tabbas abin da suke nufi a cikin Nassi. Ba mu da wasu wuraren da za mu tuntuɓa don neman ƙarin sani dangane da waɗannan kalamai.
Wanke Zunubi da Kuma Kwantar da Fushin Allah
Bari mu yi tunani akan abin da wadannan kalmomi ke nufi, fara da furuci na Wanke Zunubi. Kalma mai ja-gaba ‘wanke’ tana nufin “fitar” ko “kawar daga.” Don haka, Wanke Zunubi yana nufin fitar da wani abu ko kawar da wani abu nesa. Daga bayani na Littafi Mai Tsarki, yana nufin ɗauke zunubi ta biyan hukunci ko hadaya na kaffara. Akasin wannan shi ne Kawar Daga Fushin Allah Mai Ƙuna, wanda shi ne Hukuncin Da Ya Dace Da Zunubin Mu, ta dalilin Hadayar Yesu A Kan Giciye, ya shafi wanda aka dauke zunuban sa aka kuma kawar masa da jin laifin zunubi. Kalmomin “kawar daga” wadda ke ja-gaba a wadannan kalamai yana nufin “domin,” saboda haka Kawar Daga Fushin Allah Mai Kuna, wanda shi ne Hukuncin Da Ya Dace Da Zunubin Mu, yana kawo canji a halayyar Allah, domin ya tashi daga kasancewa cikin gaba da mu, zuwa kasancewa domin mu. Ta hanyar Kawar Da Fushin Allah Mai Ƙuna, da shi ne Hukuncin Da Ya Dace Da Zunubin Mu, an mayar da zumunta da tagomashin mu a tare da Shi.
Ta wani ɓangaren Kawar Da Fushin Allah Mai Ƙuna, da shi ne Hukuncin Da Ya Dace Da Zunubin Mu, ya danganci gamsar da Allah. Mun san yadda wannan kalma ta gamsarwa ta ke aiki a lokacin saɓani na fagen soja ko siyasa. Idan muka yi tunanin siyasar gamsarwa, wadda ra’ayin tunani ne wanda idan aka sami wani mai ƙarfin yaƙi da ke borin karɓe iko na garuruwa ya mallake su, to, a maimakon a yarda a yi arangama da shi, to gara a sakar masa wani ɓangare ko wani yanki na ƙasar. Za ka yi ƙoƙarin sanyaya fushin sa ta ba shi wani abu da zai gamsar da shi domin kada ya zo ƙasar ka ya murƙushi ku. Irin wannan ba hanyar gamsarwa ta nagarta ba ce. Amma idan kana fushi, ko an yi maka ƙeta, sai na yi abin da zai sanyaya fushin ko na gamsar da kai, to zan maido da tagomashi na a wurin ka, kuma matsalar ta sami kawarwa.
Kalmar Girkanci guda ɗaya tana ɗaukan fassara na waɗannan kalamai biyu na Wanke Zunubi da Kuma Kawar Daga Fushin Allah Mai Ƙuna. Amma akwai ɗan bambanci kaɗan a matsayin aikin su, Wanke Zunubi da Kawar Da Jin Laifin Zunubi shi ne abin da ya kawo canji a matsayin da Allah ke da shi a gare mu. Shi ne abin da Kristi Ya yi a kan giciye, kuma sakamakon wannan aikin Kristi na Wanke Zunubi da Kawar Da Jin Laifin Zunubi shi ne Kawar Da Fushin Allah Mai Kuna, wanda shi ne Hukuncin Da Ya Dace Da Zunubin Mu- Fushin Allah ya sami kawarwa. Bambancin kenan, yanayin abin da aka biya fansa da kuma halayyar shi wanda ya karɓi fansar.
Aikin Almasihu ne aikin sulhunta Allah da mutane.
Idan aka haɗa su tare, Wanke Zunubi, Da kuma Kawar Daga Fushin Allah Mai Kuna, Ya kasance sulhuntarwa dan adam ga Allah. Kristi Ya yi aikin Sa kan giciye domin ya sanyaya zuciyar Allah kan fushin sa mai ƙuna. Wannan ra’ayi na sanyaya fushin Allah mai ƙuna bai sanyaya fushin masana Tauhidi ba. Ainihi ma sun kasance da fushi mai ƙuna saboda tunanin cewa an sanyaya fushin Allah. Suna tunanin cewa wannan ya zama nuna rashin girmamawa ga Allah a ce an sanyaya fushin, cewan dole ne mu yi wani abu don mu daɗaɗa ma Sa, ko mu rarrashe Shi. Akwai buƙatar mu mai da hankali sosai game da yadda muke fahimtar fushin Allah mai ƙuna, kuma bari in tuna maku cewa batun sanyaya fushin Allah mai ƙuna a nan ba zance ne na sama-sama a fagen tauhidi ba, amma yana ɗauke da ainihin zuciyar ceto.
Mene Ne Ceto?
Bari in yi wata muhimmiyar tambaya: mene ne wannan batu ceto ke nufi? Ƙoƙarin ba da bayani cikin hanzari yana iya kawo ciwon kai, domin an yi amfani da kalmar ceto ta hanyoyin daban-daban kusan saba’in a cikin Littafi Mai Tsarki. Idan aka kuɓutar da wani daga wani yaƙin da aka ci shi, sai a ce ya sami ceto. Idan wani ya warke daga wata cuta da ta kusa ɗaukan ran sa, mutumin ya sami ceto. Idan amfanin gonar mutum suka farfaɗo suka rayu bayan barazanar bushewa don rashin ruwa, to sun sami ceto. Wannan shi ne harshen Littafi Mai Tsarki, kuma ba shi da wani bambanci cikin irin namu harshen. Muna ceto kuɗi. Ɗan wasan kokawa yana samun ceto sa’adda aka buga ƙararrawan su, ma’ana an ceto shi daga rasa kanbin nasara wanda da mugun bugu zai iya kawowa, ba ana nufin an ɗauke shi an kai shi zuwa madawwamiyar mulkin Allah bane. A taƙaice dai, duk wani hali na kuɓuta daga yanayi wanda a fili hatsari ne ya zo, za a iya cewa hali ne na ceto.
Idan muna maganar ceto kamar yadda yake cikin Littafi Mai Tsarki, dole mu mai da hankali don fayyace irin ma’anar, wadda cikin ta ne aka ainihin cetonmu. Manzo Bulus ya yi mana irin wannan kyakkyawan bayani a 1 Tasalonikawa 1:10, wurin da ya ce, Yesu ya “kuɓutar da mu daga fushin nan mai zuwa.” Mafi girma shi ne, Yesu ya mutu domin ya cice mu daga fushin Allah mai ƙuna. A haka nan dai ba za mu iya fahimtar koyarwa da wa’azin Yesu Banazare ba haka kawai, domin a kullum ya yi wa mutane gargaɗi cewa duniyar gaba ɗayanta wata rana za ta kasance a ƙarƙashin shari’ar Allah. Ga kaɗan daga cikin irin waɗannan gargaɗi Nasa da suka shafi shari’ar: “Ina gaya ma ku, kowa ya yi fushi da ɗan’uwan sa ma babu dalili, za a hukunta shi (Matiyu 5:22); “Ina gaya maku, a Ranar Shari’a duk hululun da mutum ya yi za a bincike shi” (Matiyu 12:36), da kuma “A Ranar Shari’a mutanen Nineba za su tashi tare da mutanen zamanin nan, su ka da su, don su sun tuba saboda wa’azin Yunusa. Ga kuma wanda ya fi Yunusa nan” (Matiyu 12:41). Tauhidin Yesu Tauhidi ne mai ruɗani. A Girkanci kalmar ruɗani tana nufin “shari’a.” Ruɗanin da Yesu ya yi wa’azi a kai shi ne ruɗani na shari’ar da ke zuwa ga duniya, wanda a lokacin Allah zai zubo fushin Sa mai ƙuna a kan marasa fansa, marasa kiyaye tsarki, marasa zuciyar tuba daga laifofi. Bege kaɗai na samun tsira daga wannan fushi mai ƙuna da zai zubo shi ne a kasance lulluɓe cikin kaffarar Kristi.
Saboda haka, babbar nasara mafi girma na Kristi a kan giciye shi ne cewa ya sanyaya fushin Allah mai ƙuna, wanda da zai sauka a kan mu in ba don muna lulluɓe cikin kaffarar Kristi ba. Don haka, idan wani ya yi gardamar game da sanyayawar fushin Allah, ko ga cewa Kristi ya gamsar da fushin Allah, yi hattara, domin bishara tana fuskantar ƙalubale. Wannan shi ne kusan a ce zuciyar ceto -cewa a matsayin mu na mutane da aka lulluɓe ta kaffara, an fanshe mu daga babban hatsari mafi girma da duk wani mutum zai taɓa fuskanta. Abu ne mai matuƙar ban tsoro a faɗa a cikin hukuncin Allah Rayayye da ke da fushi mai ƙuna. Amma babu fushi mai ƙuna ga waɗanda aka riga aka biya zunuban su. Wannan shi ne gaba ɗaya abin da ceto ke nufi.
An tsakuro wannan bayani daga The Truth of the Cross na R.C. Sproul.
An fara buga wannan tsararren rubutu ne a shafin ma’katar bishara ta Ligonier.


