Ta Yaya Martin Luther Ya Mutu?

17/12/2025

Menene Ma’anar Wanke Zunubi Da Kuma Kwantar da Fushin Allah?

17/12/2025

Ta Yaya Martin Luther Ya Mutu?

17/12/2025

Menene Ma’anar Wanke Zunubi Da Kuma Kwantar da Fushin Allah?

17/12/2025

Ya Ya Kammannin Tuba Yake?

Ɗaya daga cikin Zabura na tuba, Zabura 51 Dauda ne ya rubuta bayan da annabi Natan ya tunƙare shi. Natan ya bayyana cewa Dauda ya aikata mummunan zunubi a gaban Allah, da ya ɗauki Barsheba a matsayin matar sa, da kuma yadda ya kashe mijin ta, Yuriya.

Yana da muhimmanci mu fahimci irin halin taƙaici da na tuba daga zurfin zuciya wadda Dauda ya nuna, amma kuma dole ne mu gane cewa tuba daga zuciya aiki ne na Allah Ruhu Mai Tsarki. Dauda ya iya tuba ne domin tasirin Ruhu Mai Tsarki a kan sa. Bayan wannan ma, har kuma a sa’adda yake rubuta addu’ar sa, yana rubutawa ne cikin bishewar Ruhu Mai Tsarki. Ruhu Mai Tsarki ya nuna a cikin Zabura 51 yadda Yake haifar da tuba a cikin zukatan mu. Mu riƙe wannan a zuciya sa’adda muke binciken Zaburar.

Zabura 51 ya fara da, “Ka yi mani jinƙai, ya Allah, sabili da madawwamiyar ƙaunar ka. Ka shafe zunubai na, saboda jinƙan Ka mai girma” (Zabura 51:1). A nan mun ga wani abu mai matuƙar muhimmanci ga tuba. Yawancin lokaci, idan mutum ya gane da zunubin sa, ya juya ya bar wannan zunubi, ya miƙa kan sa ne ga rahamar Allah. ‘Ya’yan fari da ke bayyana tuban ƙwarai shi ne, fahimtar matuƙar buƙata da muke da ita na rahama. Dauda bai roƙi Allah ya yi shari’a ba. Ya san cewa idan Allah ya dube shi ta fuskar shari’a, nan take za a hallaka shi. Dalilin haka ne, Dauda ya fara furta laifin sa ta yin roƙo don rahama.

Sa’adda Dauda yake roƙon Allah Ya shafe laifofin sa, yana roƙon Allah ne ya cire tabo da ke zuciyar sa, Ya shafe rashin adalcin sa, Ya kuma wanke shi daga wannan zunubi da ya kasance tsayayye ya zama  wani ɓangare na rayuwar sa. Don haka ya ce, “Ka wanke ni matuƙa daga mugunta ta sarai, ka tsarkake ni daga zunubi na!” (Zabura 51:1).

Batutuwan gafara da tsarkakewa suna da dangantaka, amma sun bambanta. A cikin Sabon Alƙawari, Manzo Yahaya ya rubuta cewa, “Idan kuwa muka furta zunuban mu, to, Shi mai alƙawari ne, mai adalci kuma, zai kuwa gafarta mana zunuban mu, Ya tsarkake mu daga dukan rashin adalci” (1 John 1:9). A cikin ruhun tuba, muna zuwa wurin Allah mu furta zunuban mu, muna roƙo ba don Ya yafe mana kaɗai ba, amma har da neman iko na gujewa wannan zunubi, don kada mu sake aikatawa. Kamar yadda Dauda ya yi a zabura, muna roƙo bari sha’awar mu ta aikata mugunta ta mutu.

Dauda ya ci gaba da cewa, “Na san laifofi na, kullum ina sane da zunubai na” (Zabura 51:3). Wannan ba amsawa da furta yin laifi ne kaɗai ba. Shi mutum ne wanda nauyin abin da ya yi ke bin sa; ya ce, na san ni mai laifi ne.” Babu ƙoƙari sassauta laifin sa. Babu wani ƙoƙarin kawo hujja don fitar da kansa. Amma, a yawancin lokaci, mu ƙwararru ne wajen kawo hujjoji, da kuma saurin tsame kan mu ta hanyar da dalilai iri daban-daban na abin da ya sa muka aikata halin zunubi. Amma a wannan wuri, cikin ikon Ruhu Mai Tsarki, an kai Dauda ga matsayin da ya furta gaskiya a gaban Allah. Ya amsa laifin sa, ya kuma gane cewa a kullum zunubin sa na nan. Ba zai iya kawarwa ba, kuma ya kasance masa abu mai nauyi.

Sai ya yi kuka, “Na yi maka zunubi, gare Ka kaɗai na yi laifi, na kuwa aikata mugunta a gare Ka” (Zabura 51:3). Ta wani ɓangaren, Dauda yana matuƙar nanatawa ne. Ya aikata mummunan laifi ga Yuriya, ga ‘yan’uwa da abokan Yuriya, ga Barsheba, da kuma ga dukan tarayya ta al’umar Allah. Kuma, Dauda ya fahimci cewa, zunubi ainihin ta laifi ne ga Allah, domin Allah shi ne kaɗai cikkakke a rayuwa gaba ɗaya. Da yake Allah shi ne alƙalin Sama da duniya, ana bayyana duk wani zunubi a matsayin laifi ne ga dokokin Allah, haka kuma laifi ne ga tsarkin Sa. Dauda ya san hakan, kuma ya amince da hakan. Bai yi ƙoƙarin rage nauyin laifin da ya aikata ga mutane ba, amma ya gane matuƙar girman zunubin sa ga Allah.

Bayan haka, ya furta wasu kalamai da a yawancin lokaci ba a kula da su. Ana samun kalaman a sashe na biyu a aya ta 4, kuma suna ɗaya daga cikin furuci na ainihin tuban ƙwarai wanda muke samu cikin Littafi Mai Tsarki: “Daidai ne shari’ar da Ka yi mani, kuma daidai ne Ka hukunta ni” (Zabura 51:4). Dauda a nan yana ainihin cewa, “Ya Allah, kana da duk wani iko na hukunta ni, kuma a bayyane yake cewa, ban cancanci kome ba sai dai hukuncin Ka da fushin Ka mai ƙuna.” Dauda ya amince cewa Allah ba Shi da aibu, kuma Yana da dukan dama na hukunta shi. Babu neman rangwame ko yin ciniki a gaban Allah.

“Duba cikin zunubi aka haife ni, kuma cikin zunubi uwa ta ta yi ciki na. Amintacciyar zuciya ita Kake so, kuma Ka koya mani hikima cikin zurfin zuciya ta” (Zabura 51:5-6). Ba gaskiya kaɗai Allah ke buƙata daga gare mu ba, har ma Yana so ta fito daga zurfin cikin mu. Dauda ya amsa cewan ya kasa aikata abin da Allah ya umurta, da kuma cewa yawancin lokaci biyayyar sa ta ganin ido ce kawai maimakon ayuka da ke ɓulɓulowa daga zufin zuciyar sa.

Sai kuma Dauda ya sake kuka domin neman tsarkakewa: “Ka kawar da zunubi na, zan kuwa tsarkaka, ka wanke ni, zan kuwa fi auduga fari” (Zabura 51:7). Za mu iya jin matuƙar rashin ƙarfi cikin muryar Dauda. Dauda bai ce, “Allah, dakata tukuna. Kafin in ci gaba da wannan tattaunawa a cikin addu’a, ina so in tsaftace hannuwa na, in kuma wanke jiki na ba.” Dauda ya sani cewa ba shi da wani halin da zai iya cire tabo na laifin sa daga kansa. Ba zai iya biya ba. Muma sai mu haɗu da Dauda mu amince cewa ba za mu iya kaffara domin zunuban mu ba.

Ta hannun annabi Ishaya, a can gaba, Allah ya ba da alƙawari “Zo mu daidai ta al’amura tare. Ko dayake zunuban ku sun yi ja wur, za su zama kamar dusan ƙanƙara, ko dayake sun yi matuƙar ja fiye ma da jini, za su zama kamar auduga. (Ishaya 1:18). Allah yana jin daɗin ya tsaftace mu idan Ya tarar da mu cikin datti.   

Sai kuma Dauda ya ce, “Bari in ji sowa ta farin ciki da murna” (Zabura 51:8a). Tuba abu ne mai zafi. Wane ne yake jin daɗi a yanayin furta zunubi, da amsa cewa ya yi laifi? Jin laifi yanayi ne mai matuƙar tsanani wajen ɓata farin ciki da mutum ke da shi. Ga shi Dauda ba ya yanayin murna , haka nan ya roƙi Allah ya sabunta ruhun sa, ya sa shi sake jin farin ciki da murna. Ya yi nuni ga wannan sa’adda ya ce, “ Bari waɗannan ƙasusuwa da ka kakkarya su yi murna” (Zabura 51:8b). Ko kalaman nan basu kasance da sha’awa ba? Yana cewa, Allah, ya rugurguza ni. Ƙasusuwa na sun kakkarye; Ba Shaitan ko Natan ne suka karya ƙasusuwa na ba, amma Ka karya ƙasusuwa na sa’adda da ka yanke mani hukuncin laifi na. Don haka na tsaya a gaban Ka mutum karyayye, kuma hanya kaɗai da zan iya ci-gaba da rayuwa ita ce idan ka warkar da ni, ka maido mani da murna ta, da farin ciki na gare ni.

Bayan haka ya ce, “Ka kawar da fuskarka daga zunubai na, ka shafe duk mugunta ta. Ka halitta tsarkakakkiyar zuciya a ciki na, Ya Allah, ka sa sabon halin biyayya a ciki na” (Zabura 51:9-10).

Hanya kaɗai da za a sami tsarkakakkiyar zuciya ita ce ta ikon Allah mai sake sabontawa. Ba ni da ikon iya sabonta kai na haka kawai. Allah ne kaɗai ke iya halittar tsarkakakkiyar zuciya, kuma yana halittar tsarkakakkun zukata ta hanyar shafe zunuban mu.

Dauda ya yi kuka cewa, “Kada ka kore ni daga gaban Ka, kada Ka ɗauke mani Ruhun Ka Mai Tsarki” (Zabura 51:11). Dauda ya gane cewa wannan shi ne abu mafi muni da zai iya faruwa ga duka wani mai zunubi. Ya sani lallai, Allah zai, kore mu daga gaban Sa idan muka ci-gaba cikin ƙin guje wa zunubi. Yesu ya yi gargaɗi cewa waɗanda suka ƙi Shi, za a kawar da su daga gaban Allah har abada. Amma addu’ar tuba mafaƙa ce ga wanda ya gaskanta. Wannan shi ne martani mai dacewa ga duk wanda ya san ya aikata zunubi. Ya kamata irin wannan martani ya zama karɓaɓɓe cikin rayuwar duk wanda ya tuba.

Dauda ya ci gaba, “Ka sake mayar mani da farin ciki na ceton Ka, Ka ƙarfafa ni da zuciya ta tarbiya, sa’annan zan koya wa masu zunubi umarnan Ka, za su kuwa komo wurin Ka” (Zabura 51:12-13). Sau dayawa mukan ji cewa, mutane ba su son kasancewa a wurin da Kristoci suke, domin Kristoci suna nuna faɗin rai, da adalci irin na su kansu, ko wani hali na na-fi-ka-tsarki. Amma, ba haka ya kamata ya kasance ba. Krista ba su da wani abin da za su yi faɗin rai a kai; mu ba wasu mutane masu adalci ne da ke ƙoƙarin kawo gyara ga marasa adalci ba. Kamar yadda wani mai wa’azi ya ce, “Aikin bishara shi ne, mabaraci ne yake ƙoƙarin gaya ma wani mabaracin wurin da zai sami burodi.” Muhimmin bambanci tsakanin mai-bi da mara-bi shi ne gafara. Abin da kaɗai ke ba mutum cantanta na kasancewa mai aikin bishara cikin sunan Kristi shi ne cewa, wannan mutumin ya ɗanɗana gafara, kuma yana so ya bayyana wannan yanayi ga wasu.

Ya Ubangiji, Ka buɗe laɓɓa na, baki na zai furta yabon Ka. Ba Ka son sadakoki, ai da na ba Ka; ba Ka jin daɗin hadayun ƙonawa. Hadaya da Allah ke so ita ce, ruhun da ya karaya, da zuciya wadda ta karaya tana nadama, Ya Allah ba za ka ƙi ba. (Zabura 51:15-16). A nan ne muka sami ainihin zuciya da ruhin tuba bisa ga anabci na waɗannan kalamai, “ruhun da ya karaya, da zuciya wadda ta karaya tana nadama, Ya Allah ba za ka ƙi ba.” Dauda yana cewa da zai iya yin kaffara domin zunuban sa, da ya yi; amma bisa ga yanayin da ke na zahiri, begen sa kaɗai shi ne cewa, Allah zai karɓe shi bisa ga rahamar Sa.

Littafi Mai Tsarki ya nuna mana a fili da kuma ta kowace hanya cewa, Allah yana gaba da masu girman kai, amma yana yi wa masu tawali’u alheri. Dauda ya sani wannan gaskiya ce. Duk da zurfin karaya tasa, ya san Allah, ya kuma san yadda Allah yake yi da mutane masu nadama. Ya fahimci cewa Allah bai tsana ko ya kori zuciya da ta karaya take nadama ba. Wannan shi ne abin da Allah ke buƙata daga gare mu. Abin da ke a zuciyar Yesu kenan a lokacin wa’azi a kan dutse, da ya ce, “Albarka ta tabbata ga masu nadama, “domin za a sanyaya masu rai” (Matiyu 5:4). Wannan nassi ba kawai yana magana a kan yin makoki na rashin ƙaunatacce namu ba, amma har da irin makoki da muke kasancewa a ciki sa’adda aka nuna mana laifin mu. Yesu ya tabbatar mana cewa sa’adda muke makoki saboda zunuban mu, Allah ta wurin Ruhun Sa Mai Tsarki zai ta’azantar da mu.

Zan ba da shawara cewa dukan Krista su haddace Zabura ta 51. Kyakkyawan misali ne mai dacewa da za ayi koyi da shi na tuba ta gaskiya. Lokuta da dama a rayuwa ta, na zo gaban Allah na ce, “Ka halitta tsarkakakkiyar zuciya a ciki na, Ya Allah,” ko kuma, “Ka shafe laifofi na. Ka kawar da zunubi na. Ka wanke ni zan kuwa tsarkaka.” sau dayawa na yi wannan addu’a, “Ya Allah, Ka sake mayar mani da farin cikin ceton Ka,” na yi roƙo na ce, “gare Ka, gare Ka kaɗai na yi zunubi.” Sa’adda ainihin halin jin laifi ya mamaye mu, kalmomi sukan kasa mana a ƙoƙarin mu na bayyana kan mu cikin nadama a gaban Allah. A gaskiya albarka ne babba cewa, muna da nassoshi na musamman, su kansu, a bakunan mu cikin irin waɗannan yanayin.

An tsakuro wannan daga dan littafin Crucial Questions What is Repentence? Na R.C. Sproul.


An fara buga wannan tsararren rubutu ne a shafin ma’katar bishara ta Ligonier.

R.C. Sproul

R.C. Sproul

Dr. R. C. Sproul shi ne ya kafa Ministirin Ligonier, shi ne kuma mai bishara da koyarwa na farko a masujadar Saint Andrew’s da ke a Sanford, Fla., Shugaba na farko na Reformation Bible College, kuma Babban darekta na mujallar Tabletalk. Har yau, ana yaɗa shirin sa na Renewing The mind (sabonta tunani) a dubban tashoshin radiyo a kewayen duniya, haka kuma ana iya sauraro a yanar gizo. Ya wallafa litattafai fiye da dubu, sun haɗa da, The Holiness of God (TSarkin Allah), Chosen by God (zaɓin Allah), da kuma Everyone’s a Theologian (Kowa Dalibin Tauhidi ne). Ya zama sananne a kewayen duniya domin kalaman sa na kishin kare Littafi Mai Tsarki a matsayin babu kuskure a ciki, da kuma buƙatar mutanen Allah su tsaya daram bisa amincin su a kan Kalmar Sa (Allah).