
Menene Ma’anar Wanke Zunubi Da Kuma Kwantar da Fushin Allah?
17/12/2025
Me ya sa Gyara ya zama Wajibi?
25/12/2025Menene Mafi Girma Cikin Dukkan Bidi’oji na Furotesta.
Bari mu fara da tambaya ta jarrabawar tarihin ikklisiya. Kadinal Robert Bellarmine (ya yi rayuwa daga 1542 zuwa 1621) babban mutum ne da aka ɗauke shi da matuƙar muhimmanci. Shi ne malamin tauhidi na Paparoma Clement na takwas, kuma shi ɗaya ne daga cikin mutanen da suka yi tsayayya da batutuwan da suka danganci Gyara a Roman Katolika cikin ƙarni na goma sha shida. A wani lokaci, ya rubuta cewa: Mafi girma cikin ire-iren koyarwar ƙarya na Furotestan shi ne_____.” Cika, bayyana, ka kuma tattatuna furucin Bellarmine.
Ya ya za ku amsa? Wannene mafi gawurta cikin ire-iren koyarwar ƙarya na Furotestan? Mai yiwuwa barata ta hanyar bangaskiya? Ko ta Maganar Allah kaɗai, ko kuma ɗaya daga cikin sauran batutuwan da Gyaran ya mai da hankali a kai?
Duka waɗannan amsosi sun iya ba da ma’ana. Amma babu ko ɗayan su da ya cika wannan jimla ta Bellarmine daidai. Abin da ya rubuta shi ne: “Mafi gawurta cikin ire-iren koyarwar ƙarya na Furotestan shi ne tabbaci.”
Idan aka yi juyayi na lokaci kaɗan za a gane abinda ya sa. Idan barata ba ta bangaskiya kaɗai bane, ko a cikin Kristi kaɗai ba, ko ba ta alheri kaɗai ba – idan bangaskiya na buƙatar ayuka domin ta sami dacewa; idan ya zamana sai an maimaita aikin da Kristi ya yi, ko idan alheri ba kyautabane da kuma bai kasance bisa komai ba, to kenan, dole a kullum akwai buƙatar aikata wani abu, da za a “ƙara” domin barata ta gaba-daya ta zama namu. Wannan shi ne matsalar. Idan barata ta gaba-daya tana dogaro ga wani abin da muka kammala ne, to ba zai yiwu mu mori tabbacin ceto ba. Domin zai kasance kenan, barata ta gaba-daya tana dogara kan wani abu ne, kuma ba ta da tabbas, kuma zai zama da wuya ga duk wani mutum(in an ware muhimman wahayi da Roman suka amince) ya kasance da tabbacin ceto. Amma idan Kristi ya riga ya yi komai, kuma idan barata ta wurin alheri ne, ba tare da wani taimako na ayuka ba; An karɓa da hannuwan da ba su riƙe da komai ciki sai bangaskiya -lallai ya zama kenan tabbaci, wato, “cikakken tabbaci “ yana samuwa ga kowane mai gaskantawa.
Shi ya sa bai zama abin mamaki ba da Bellarmine ya yi tunanin cewa cikakke, kuma kyautar alheri marar iyaka hatsari ne! Ashe kuwa bai zama da mamaki ba yadda Masu-Gyara suka so wasiƙa zuwa ga Ibraniyawa!
Wannan ne ya sa, a lokacin da marubucin Ibraniyawa ya ɗan dakata don ya numfasa, sa’adda ya kai ƙolin bayanin aikin Kristi (Ibraniyawa 10:18), ya ci-gaba da bayyana hujjojin sa ta yin amfani da kalamai irin na Bulus cewa, “saboda haka” (Ibraniyawa 10:19). Yana ƙarfafa mu, mu “matsa kusa … cikin bangaskiya cikakkiya tabbatacciya” (Ibraniyawa 10:22) Ba mu buƙatar sake karanta dukan wasiƙar kafin mu ga ikon ma’anar “saboda haka” da ya yi amfani da ita.” Kristi Shi ne babban Firist ɗin mu mafi girma; an wanke zukatan mu an tsaftace su, daga duk wani mugun lamiri, kamar dai yadda aka wanke jikunan mu da tsarkakakken ruwa (sura 22).
Kristi Ya miƙa hadaya guda-ɗaya-tak na gaba-ɗaya domin zunuban mu, kuma an tashe Shi daga matattu, an kuma wanke shi daga tuhuma, cikin ikon rai da ba a iya hallakarwa a matsayin Sa na firist da ya wakilce mu. Ta hanyar gaskantawa da Shi, mun zama adilai a gaban kursiyan Allah, kamar yadda Shi yake adali. Gama mun sami barata a cikin adalcin Sa, baratar tasa kaɗai ce tamu! Kuma babu wani abu da zai iya sa mu rasa wannan barata, ko ma mene ne. Saboda haka, babu buƙatar wani abu da zai cika baratarwar mu, wanda ya wuce cikawar Kristi!
Riƙe da wannan fahimta, marubucin ya ce, “ta hadaya guda kawai ya kammala na har abada duk waɗanda suka zo ga Allah ta wurin Sa” (Ibraniyawa 10:14). Dalilin da ya sa muke iya tsayawa a gaban Allah da cikakkiyar tabbaci shi ne, don yanzu mun samu an “tsarkake zukatan mu daga mugun lamiri, jikunan mu kuma wankakku da tsarkakakken ruwa” (Ibraniyawa 10:22).
“Ah,” in ji Roman Kadinal Bellarmine, in ka koyar da wannan, to waɗanda suka gaskanta hakan za su yi rayuwa cikin samun sarari da ƙin kiyaye dokoki da sauran ayukan addini.” Amma saurari kyakkyawan bayani da ke a Ibraniyawa. Morar wannan tabbaci yana kai wa ga abubuwa huɗu: Na farko, aminci marar kasawa bisa ga bayyana imanin mu ga Yesu Kristi kaɗai, a matsayin begen mu (aya 23); na biyu, yadda za mu lura, mu sa hankali wajen ƙarfafa juna ga “ƙauna da ayukan nagarta” (aya 4); na uku, cin-jibi kullayomi babu yankewa, tare da sauran Kristoci cikin ibada, da aiwatar da duk wani ɓangaren zumuntar mu (aya 25). Na huɗu, za mu mori, rayuwa wadda muke ƙarfafa juna ga zuba idanun mu ga Kristi, mu kuma kasance da aminci a gare Shi, domin ranar dawowar Sa tana kusatowa (aya 25b).
Itacen kirki ne yakan haifi kyawawan ‘ya’ya, ba akasin haka ba. Ba a cece mu ta ayuka ba; an cece mu domin yin kyawawan ayuka. A ainihin , mu kayan aikin Allah ne da ke aikata ayuka (Afisawa 2:9-10)!
Domin haka, wannan aikin Yesu Kristi da ya yi sau-ɗaya-tak na gaba ɗaya da cikakkiyar tabbacin bangaskiya da take kawowa, tana tanadar wa mai bangasakiya da ƙarfin iko don yin rayuwa domin ɗaukaka ga Allah, da jin daɗin Sa. Bayan haka ma, wannan cikakkiyar tabbaci tana da tushen ta cikin gaskiyar cewa Allah da Kansa, Shi ya yi duka wannan domin mu. Ya bayyana zuciyar Sa gare mu a cikin Kristi. Uban bai buƙaci mutuwar Kristi ta kasance abin da ya zuga Shi ga ƙaunar mu ba. Kristi ya mutu domin Uban yana ƙaunar mu (Yahaya 3:16). Ba wai yana ɓuya a bayan Ɗan Sa, yana fatan samun damar yi mana mugunta ba- kamar da ba don hadayar da Ɗan Sa ya yi ba! Sam-sam, ko fiye da sau dubu ne, sam! -Uban Shi Kansa yana ƙaunar mu cikin ƙauna ta Ɗan, da kuma ƙauna ta Ruhun.
Waɗanda suke morar wannan tabbacin, ba su zuwa ga tsarkaka ko ga Maryamu. Waɗannan da suke zuba idanu ga Yesu kaɗai ba su buƙatar kafa ido a wani wuri kuma. A cikin Sa muke morar cikakken tabbacin ceto. Mafi gawurta cikin koyarwar ƙarya? Idan dai koyarwar ƙarya ce, to bari in mori mafi albarka cikin “koyarwan ƙaryar”! Domin wannan dai gaskiya ce ta Allah da alherin Sa!
An fara buga wannan tsararren rubutu ne a shafin ma’katar bishara ta Ligonier.


