
Menene Mafi Girma Cikin Dukkan Bidi’oji na Furotesta.
23/12/2025
Dalilin Da Ya Sa Gyarar Ke Da Muhimmanci Har A Yau
30/12/2025Me ya sa Gyara ya zama Wajibi?
A koyaushe Ikkislisiya tana cikin buƙatar gyara. Har a cikin Sabon Alƙawari, mun ga Yesu ya tsauta wa Bitrus, mun kuma ga Bulus ya yi wa Korintiyawa gyara. Da yake a koyaushe Krista masu zunubi ne, a kullum ikkilisiya za ta buƙaci gyara. Amma, tambayar da take gaban mu ita ce, a wane lokaci ne wannan buƙatar take zama cikakkiyar wajibi?
Manyan Masu Gyara a ƙarni na goma-sha-shida sun zartar cewa gyara buƙata ce ta gaggawa da ta zama wajibi a kwanakin su. Ta dalilin aiwatar da gyara domin ikkilisiya, sun ƙaurace wasu ra’ayoyi biyu. A ɓangare ɗaya, sun ƙi amincewa da waɗanda suka nace cewa ikkilisiya kanta cikakkiya ce, ba ta da buƙatar muhimman canje-canje. A ɗaya ɓangaren kuma, sun guje ma waɗanda suka yi imanin cewa suna iya ƙirƙiro ikkilisiya da ta zama cikakkiya ta kammala a kowane fanni. Ikkilisiya ta buƙaci muhimmin gyara, amma kuma a koyaushe tana da buƙatar ta riƙa gyara kanta da kanta. Masu Gyaran sun kai ga wannan ƙarshe bisa ga nazarinsu na Littafi Mai Tsarki.
A shekarar 1543, wani Mai Gyara na Strasbourg, Martin Bucer, ya roki John Calvin ya rubuta muhawarar jaddada Gyara, Wadda za a gabatar wa Sarkin Charles na biyar a taron majalisar da za a yi a Speyer a shekara 1544. Bucer ya sani cewa sarki na ɗarikar Roman Catholic yana kewaye da mashawarta waɗanda Suna kin gyara a cikin ikkilisiya, kuma Martin ya yi imanin cewa Calvin shi ne mai hidimar bishara da ya fi cancanta wajen kare hakkin Protestant.
Calvin ya tunƙari ƙalubalen, ya rubuta ɗaya cikin mafi kyau na rubuce-rubucensa, “The Necessity of Reforming the Church.” Wannan isasshen rubutu bai canza ra’ayin sarkin ba, amma kuma mutane da yawa sun ɗauke shi a matsayin mafi kyau cikin takardun da aka taɓa rubutawa kan Gyara.
Calvin ya fara da yin la’akari cewa, kowa ya yarda da cewa ikkilisiya tana da “cututtuka da yawa da masu muni.” Calvin ya ce al’amura sun yi muni sosai wanda har Krista ba za su iya haƙura na “ƙara jure wani lokaci” don gyara, ko su jira “hanyoyin magancewa masu ɗaukan lokaci ba”. Ya ƙi amincewa da cewa Masu Gyaran suna da laifin “gaggawan biɗi’a mai muni”. Maimakon haka, ya jajirce cewa “Allah ya tayar da Luther da wasu mutane” domin su adana “ita gaskiyar addinin mu.” Calvin ya ga cewa tushen Kristanci na fuskantar barazana, kuma cewa gaskiyar Littafi Mai Tsarki ce kaɗai za ta sabunta ikkilisiya.
Calvin ya dubi muhimman fannoni huɗu cikin rayuwar ikkilisiya da ke buƙatar gyara. Waɗannan fannonin sun haɗa da abin da ya kira “rai da jiki na ikkilisiya”. Ran ikkilisiya ya ƙunshi “tsattsarka da ƙayyadaddiyar sujada ga Allah” da kuma “ceton mutane”. Jikin ikkilisiya kuma ya ƙunshi “amfani da Sacramenti” (amfani da kayan jibi ko al’adun baftisma) da “gudanarwar shugabanci na ikkilisiya.” Ga Calvin, waɗannan batutuwa suna a cibiyar muhawarar Gyara. Suna da matuƙar muhimmanci ga rayuwar ikkilisiya, kuma ana iya fahimtar su ne kaɗai bisa hasken koyarwar Nassi.
Za mu iya mamakin cewa Calvin ya sanya sujada ga Allah a farkon batutuwan Gyara, amma wannan ra’ayi ne da yake riƙe da shi a koyaushe. Tun baya, ya rubuta saƙo ga Kadinal Sadoleto: “Babu wani abin da ya fi hasari ga centonmu fiye da bautar Allah ta hanyar da ba ta dace ba”. Sujada wuri ne da muke saduwa da Allah, kuma wannan saduwar dole a gudanar da ita bisa ƙa’idar Allah. Sujadar mu tana nuna ko da gaske mun karɓi Kalmar Allah a matsayin ikon da ke kan mu, muna kuma biyayya da shi. Tsarin Sujada ta son zuci wata siga ce ta adalci-bisa-ayyuka, da kuma nuni na bautar gumaka.
Daga nan, Calvin ya juya ga abin da sau da yawa muke tunani a matsayin batu mafi girma na Gyara, mai suna, Koyarwa akan cikakken yafewa da daukar mutum a matsayi mai adalci a gaban Allah:
Mun tsaya a kan wannan, cewa ko da kan wane bayani ne aikin mutum ya kasance, ana ɗaukan sa adali a gaban Allah, Bisa ga rahamar wadda ba a cancanta da it aba, amma Allah ya bayar da ita kyauta; domin Allah, wanda ba ya daukaka ayyuka, ya maishe shi nasa cikin Kristi, ta wurin sanya adalci Kristi a cikin sa, kamar nasa ne. Muna kiran wannan adalci ta bangaskiya, wato, sa’adda mutum, wanda ba shi da sauran daman dogaro kan ayyuka, ya kai ga amince cewa, iyakar dalilin karɓuwarsa ga Allah shi ne, adalci wanda shi kansa ba shi da shi, kuma an samo ne daga Kristi. Abin da a koyaushe duniya take bijirewa a kai, (domin wannan kuskuren ya yaɗu cikin kusan dukkan tsara,) shi ne tunanin cewa mutum, komai ƙaƙancin kasawar sa, ta yiwu, yana iya samun cancantar tagomashin Allah ta wurin ayyuka.
Waɗannan muhimman batutuwa da suka zama ran ikkilisiya, suna da goyon baya daga jikin ikkilisiya: al’adun ikkilisiya da gudanarwar ikkilisiya. Dole a dawo da al’adun bisa tsattsarkar ma’anarsu mai sauƙi da kuma yadda ake morar su bisa ga tsarin Littafi Mai Tsarki. Dole gudanarwar ikkilisiya ta ƙi duk wani shugabancin danya, da ke ɗaure lamirin Krista ga abubuwan da suka saɓa wa Kalmar Allah.
Sa’adda muke duban ikkilisiyar zamanin mu, muna iya cewa ana buƙatar gyara–haƙiƙa, haka ya zama wajibi–a fannoni dayawa da Calvin ya nuna damuwa sosai. Kalma da Ruhun Allah ne kaɗai za su ainihin gyara ikkilisiya. Amma ya kamata mu yi addu’a, mu kuma yi aiki da aminci domin irin wannan gyara ya zo a lokacinmu.
An fara buga wannan tsararren rubutu ne a shafin ma’katar bishara ta Ligonier.


