
Me ya sa Gyara ya zama Wajibi?
25/12/2025
Aƙidu da Furucin Imani na Furotestan
01/01/2026Dalilin Da Ya Sa Gyarar Ke Da Muhimmanci Har A Yau
A ranar 31 na Oktoba, 2016, Paparoma Francis ya yi sanarwa cewa, bayan shekaru ɗari biyar, Furotestan da Katolika a yanzu “suna da damar gyara wani muhimmin lokaci na tarihin mu, ta hanyar ci-gaba, a yi nesa da yanayi na jayayya da irin saɓani wanda yawanci yake hana mu fahimtar juna.” Daga wannan maganar, ya zama kamar Gyaran ɓata lokaci ne, kuma damuwa ne kan abubuwan da ba su taka kara sun karya ba, kamar irin rikicin da ƙananan yara sukan yi, wanda amma, yanzu da kowa ya girma za mu iya mantawa da shi.
Amma ba za a iya gaya wa Martin Luther wannan ba, wanda ya karɓi zuwan ‘yanci da murna sa’adda ya sake gano cewa samun barata ta gaskantawa ne kaɗai, yadda har ya rubuta cewa, “Sai gaba ɗaya na ji kamar an sake haihuwa ta, kuma na shiga aljanna ita kanta ta ƙofa buɗaɗɗiya.” Haka ma ba za a iya gaya wa William Tyndale da ya ce ya, ji annashuwa, da murna, da farin ciki, wadda ya sa shi “raira waƙa, da tsalle cikin murna.” Shi kuma Thomas Bilney da ya sami ganewar, ya kasance cikin, salama mai armashi, da kwanciyar hankali, yadda har raunannun ƙasusuwa na suna tsalle-tsallen murna.” Ya nuna a bayyane cewa waɗannan Masu-Gyara na farko ba su kasance da tunanin wai rigima za su tayar ba, domin kamar yadda suka gani, sun samo albishir na farin ciki mai yawa ne.
Labari Mai Daɗi a 1517
A farkon ƙarni na goma sha shida, lokacin Turai sun kasance ba su da Littafi Mai Tsarki wanda mutane za su iya karantawa, har na tsawon kusan shekaru dubu ɗaya. Saboda haka, Thomas Bilney bai taɓa karo da kalamai kamar “Kristi Yesu ya zo duniya domin ya ceci masu zunubi.” (1 Timoti 1:15). A maimakon Maganar Allah, an bar su kawai da bayani na cewa, Allah, Allah ne da ke barin mutane su samo wa kansu ceto. Kamar yadda wani daga cikin malaman wancan zamanin ya faɗa cewa, “Allah ba zai hana alherin Sa ba, ga waɗanda suka dage cikin ƙoƙarin su.” Sai dai kuma waɗannan kalmomi da suke ganin wai na ƙarfafawa ne, sun bar kowa da jin nauyin zuciya ga duk wanda ya ɗauke su da muhimmanci. Ya ya ma za ka iya sanin ko ka yi iyakacin ƙoƙarin ka da duk ƙarfin da iyawar ka za ta iya yi? Ya ya za ka iya sani ko ka kai matsayi na mutum wanda ya cancanci ceto?
Zahiri, Martin Luther ya yi ƙoƙari. Ya rubuta cewa, “Ni ainihin ɗan ƙungiyar maza mabiya addinni ne, da ke ɗaukar niya ta rayuwa cikin talauci, da tsarki, da kuma biyayya. Kuma na kiyaye umurni dalla-dalla har ya kai ga zan iya cewa, idan akwai irin ɗan wannan ƙungiya da zai shiga aljanna domin tafiyar da wannan rayuwa ta keɓancewa don aikata sassauƙar rayuwar tare da bin dokoki, lallai da na shiga.” Amma duk da haka, ya gane:
Lamirina ba zai ba ni tabbaci ba, amma kullum ina shakka in cewa, “ba ka yi abin da ya dace ba. Nadamar ka ba ta isa ba. Ba ka sa wannan a furucin ka na tuba ba.” A duk ƙoƙarin da nake yi don magance rashin sanin tabbas, da rashin ƙarfi, da damuwa da muraɗi na kan kasance a ciki dangane da al’adun ‘yan Adam, sai kuma a kullum na ci gaba ganin rashin tabbas, da rashin karfi, da yawan damuwa a cikin yanayin.
Bisa ga ra’ayin Roman Katolika, daidai da Luther ya kasance cikin rashin tabbaci na aljanna. Suna ganin cewa, kasancewa da tabbaci na samun wuri a aljanna, ya zama zato cikin kuskure, kuma yana daya daga cikin laifofin da aka tuhumi Joan din Arc a lokacin yi mata shari’a a 1431. A lokacin, alkali ya furta cewa,
Wannan matar ta aikata zunubi sa’adda ta ce, tabbacin da ta ke da shi na za a karbe ta cikin Aljanna yana da matukar karfi har tana ji kamar ta riga ta sami…. daukaka, ganin cewa a wannan rayuwar tafiya ta bakonci a duniya, babu matafiyi da ya san ko ya cancanci daukaka ko kuma hukunci, wadda alkali mai iko duka ne kadai ne zai iya fada.
Wannan hukunci da aka yanke ya kasance da ma’ana ga irin tunanin na tsarin. Idan har za mu shiga Sama domin mun (ta wurin alherin Allah) sami cancanta ta iyawar kanmu ne, to, lallai babu wanda zai iya kasancewa da tabbaci. Bisa ga wannan tsarin tunani, zai zama cewa tabbacin na na shiga Sama ya dogara ne ga tabbacida na ke da shi kan rashin zunubi na kaina.
Ainihin dalili kenan da ya sa matashin nan Martin Luther sa’adda ya ke dalibi, ya yi ihu saboda tsoro a lokacin da walkiya ya kusa ya fado masa ana ruwan sama. Ya razana matuka, domin idan babu fahimta ta isasshiya da kuma alherin ceto na Kristi -idan babu fahimta ta barata a ta hanyar gaskantawa kadai- a she kenan ba shi da begen Sama.
Abin da ya sa kenan sake gano wannan Nassi a kan barata ta hanyar gaskantawa kadai, ya zama kamar shiga Aljanna ta budaddiyar kofa. Yana nufin cewa, a maimakon dukan fushin sa da matukar tsoron sa, yanzu za iya rubuta cewa:
Idan shaidan ya wurgo mana zunuban mu, yana cewa mun cancanci mutuwa da jahannama, ya kamata mu furta cewa: Na yarda cewa na cancanci mutuwa da jihannama. Sai me kenan? Ko yana nufin za a yanke mani hukuncin shiga la’ana na har abada? Sam wannan ba haka bane. Domin na san Wani wanda ya sha wahala ya kuma gamsar domin. Sunan sa Yesu Kristi, Dan Allah. Wurin da yake, a nan zan kasance.
Dalili kenan da Gyaran ya sa mutane suka zama da marmarin bishara da karatun Littafi Mai Tsarki. Domin samu a karanta Maganar Allah, Sannan daga cikin ta aka kuma gano irin wannan labari mai dadi, na cewa, Allah yana ceton masu zunubi, ba domin yadda suka tuba bane, amma cewa komai gaba daya ya dogara ne kan alherin Sa (Allah), zancen ya zama kamar tasowar hasken rana daga babban teku, yana haskakawa cikin duhu na duniyar mai zargi da ka’idojin addini.
Labari mai dadi a 2017
Babu wani abu ko kadan da ya bata, daga cikin albarku ko tasiri wanda Gyaran ya kawo fahimtar su a cikin shekaru dari biyar da suka wuce. Amsoshin na duk muhimman tambayoyin nan suna nuna kyakkyawan bambanci tsakanin yanayin dan Adam na kasancewa da bege ko kuma murna. Me zai faru da ni bayan na mutu? Ya ya zan iya sani? Ko barata kyauta ne ga kasancewa a matsayin tsattsarka(kamar yadda Masu-Gyara suka yi muhawara), ko tafiya ce ta kai wa ga zama da ƙarin tsarki(kamar yadda Roma ke faɗa)? Zan iya zama da tabbaci kan dogara ga Kristi kaɗai domin ceto na, ko kuma ceto na ya dogara ga ƙoƙarin da zan yi zuwa tsarki, ko nasara wajen kai wa ga tsarki?
Kusan zahiri ne cewa, abin da yake ruɗar da mutane har su ɗauki Gyaran a matsayin tarihi ne wanda lokacin sa ya wuce, kuma sai a ci gaba da rayuwa kawai, shi ne tunanin cewa, martani ne kawai aka yi saboda matsalar da ta taso a zamanin can. Amma muddin an mai da hankali an lura sosai, za a sami kyakkyawar fahimta. Gyaran ba wai ainihin ra’ayi mara kyau bane da suka yi don neman janyewa daga Roma da halin ta na rashin gaskiya; yunƙuri ne mai kyau, da ya shafi ƙara bunƙasa bishara, ta ci-gaba. Kuma lallai abin da kenan ya kare amincin Gyaran har zuwa yau. Da a ce Gyaran ya kasance wata faruwa ta haka kawai ce game da wani yanayi na tarihi a shekaru ɗari biyar da suka wuce, ai ya kamata da batun ya mutu. Amma da yake tsari ne da ya haifar da matsowa kusa da bisharar, to, ba zai iya ƙarewa ba.
Wani abu kuma da ke haifar da jayayya shi ne, a ɗabi’u na wannan zamani na tsarin kyakkyawan tunani game da yadda mutane ke kimanta darajar kansu, ya kawar da buƙata da ya kamata mai zunubi ya kasance da ita na neman barata. A yanzu ba mutane dayawa ne ke yafa tufafin tuba, da kiyaye yin addu’o’in dukan dare ba, a cikin tsananin sanya, wai don neman samun gata a wurin Allah. Gaba ɗaya dai, matsalar Luther na yadda tsananin tunanin ji shi mai laifi ne a gaban Allah, wanda Shi ne alkali, ya zama an yi watsi da shi, ana gani sa a matsayin matsala ne na ƙarni na goma sha shida, haka kuma an yi watsi da yadda aka magance batun, wato, barata ta dalilin gaskantawa, ya zama kenan babu buƙatar shi a yau.
Amma kuma, saboda daidai irin wannan yanayin ne, hanyar Luther na magance matsalar ya yi ƙarfi a matsayin labari mai daɗi, mai tasiri kuma. Domin tun da an yi watsi da tunanin cewa, za mu iya kasancewa masu laifi a gaban Allah, wanda ya sa muke buƙatar barata Tasa, al’adar mu ta mika wuya, ta koma ga tsohuwar matsala a jin kai mai laifi ne, tare da rashin hanyar samun maganin yanayin. Yanzu duk an cika mu da saƙonni da ke cewa, za a fi ƙaunar mu sosai idan mun gyaran kanmu sosai. Mai yiwuwa abin da muke yi bai ma shafi hidima ga Allah ba, amma duk ya da haka ya zama addini ne na aikata ayuka yake sarƙaƙe a ciki matuƙa.
Dangane da batun ne, Gyaran yana ɗauke da labari mai daɗi mafi haske. Kamar tsananin hasken rana da ke cike da ɗaukaka, haka nan ne kalaman Luther da ya furta suke rushe duk wani duhu.
Ƙaunar Allah ba takan nemo a kawo mata bane, tana halittar abin da ke mata daɗi ne . . . maimakon nema wa kanta abubuwa masu kyau, ƙaunar Allah tana ƙwarara gaba, tana ba da abubuwa masu kyau. Saboda haka masu zunubi sukan zama da sha’awa domin ana ƙaunar su: Ba wai ana ƙaunar su domin su abin sha’awa bane.
Yanzu Kuma, Lokacin Ya Yi
Har yanzu, shekaru ɗari biyar bayan faruwar, ikklisiyar Roman Katolika ba ta sami gyara ba. Duk da irin yarda da aka samu na kalamai tsakanin ‘yan Furotestan da na Roman Katolika, har yanzu Roma ta ki amincewa da barata ta gaskantawa kaɗai. Tana ganin za ta iya nuna na ki, domin a gare ta, ba ta ɗauki Maganar Allah a matsayin iko mafi girma duka ba, wanda paparoma, da majilasa, da duk koyarwa za ta biye ma ba. Kuma da yake an mai da Maganar Allah can baya, sai ba a ƙarfafa ilimin Littafi Mai Tsarki ba, dalilin haka ne miliyoyin talakawa na Roman Katolika suna nesa da samun hasken Maganar Allah.
Ko a wajen Roman Katolika ma, koyarwar barata ta hanyar gaskantawa kaɗai, sau dayawa ana guje ma koyarwar a matsayin ba wani muhimmin abu bane, ko karkatacciyar tunani, ko kuma a ce abu mai rikitarwa ne. Wasu sabobbin ra’ayi game da ko mene ne Manzo Bulus yake nufi da barata ta hanyar gaskantawa, musamman idan sun yin ƙoƙarin kawar da muhimmancin daga duk wata buƙata ta mutum na tuba don kansa, ya kasance da matuƙar ruɗani wa mutane, suna barin rubutun da Luther ya yi, wanda ya ce, ba za a iya watsi da shi ba, ko a sirka shi ba -sai ga shi ana watsi da shi, ana kuma sirka shi.
Yanzu ba lokaci ne da za a riƙa sanyin jiki game da batun barata, ko game da matuƙar girman ikon Maganar Allah da ya bayyana cikin furucin ba. Barata ta hanyar gaskantawa kaɗai ba batu ne da ke cikin aƙidar litattafan tarihi ba; amma har yau yana nan a matsayin saƙo mai ainihin ‘yantarwa, saƙo da ke da matuƙar ikon sa ‘yan Adam su wartsake, su kuma bunƙasa. Yana ba da tabbaci a gaban Allahn mu Mai Tsarki, yana kuma canza masu zunubi da suka so su manta da Allah, amma suka zama tsarkaka da ke ƙaunar Sa da kuma tsoron Sa.
Kuma wai, annan irin dama da muke da ita a yau na yin shelar wannan labari mai daɗi! Shekaru ɗari biyar da suka wuce, sai rubuce-rubucen Gutenberg, ta dalilin kirkira na sabon kamfanin buga litattafai, ya sa hasken bishara na yaɗuwa cikin ɗan ƙanƙanin lokaci da ba a taɓa tsammani ko gani ba. Da yawan Littafi Mai Tsarki bugun Tyndale, da ƙananan takardu na Luther, masu ɗauke da saƙon bishara suna samun yaɗuwa a dubban su. A yanzu, ci-gaba na kimiya da aka samu ya tanada mana wani sabon yanayi na Gutenberg, haka kuma daidai irin saƙon da Luther ya yi a lokacin, yanzu yana iya yaɗuwa cikin saurin da ba a taɓa tunani ba.
Da buƙatu, da kuma dama iri daban-daban suna nan da matuƙar yawa a yau, kamar yadda suke a shekaru ɗari biyar da suka wuce -a gaskiya ma sun fi na da. Bari mu sami ƙarfafawa cikin aminci na masu Gyara, mu kuma riƙe ita wannan bisharar da matuƙar muhimmanci, domin bata rasa ko kaɗan daga cikin ɗaukakar ta, ko ikon ta na kawar da duhun mu ba.
An fara buga wannan tsararren rubutu ne a shafin ma’katar bishara ta Ligonier.


