
Mene Ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce Game Da Auren Mata Fiye Da Guda Ɗaya?
03/09/2026
Me ya sa muke waƙa a lokacin Kirsimeti?
10/09/2026Ya Kamata In Je Kwalejin Tauhidi?
Yawancin ɗalibai masu neman gurbin karatu da nake haɗuwa da su suna fama da tambayar nan, “Ya kamata in je kwalejin tauhidi?” Wasunsu suna kallon wannan tambayar ne ta fuskar neman jagora. Suna ƙoƙarin fahimtar ko Allah yana son su tafi kwalejin tauhidi ko kuma su yi wani abu dabam. Wasu kuma, suna mamakin ko hakan ya dace da albarkatun da za a buƙata don kammala karatu. Suna kallon wannan tambayar ne ta fuskar ribar da za a samu daga abin da aka zuba, kuma yawanci suna yin tambayar ne ta wannan hanyar: Menene kwalejin tauhidi za ta yi mini? Mene ne zan samu daga cikinta?
A cikin wannan makalar, zan tattauna ne game da rukunin farko na ɗalibai masu neman gurbin karatu—waɗanda ke fadi-tashi wajen gane abin da Allah yake so su yi. Zan tattauna rukuni na biyu a cikin makala ta gaba. Manufata a cikin wannan makalar ita ce in yi magana kai tsaye ga waɗanda suke tambayar ko ya kamata su tafi kwalejin tauhidi. Idan da za mu iya haɗuwa da kai ido-da-ido, ga shawarar da zan ba ka.
Na farko, zan ƙarfafa ka ka yi tunani sosai akan abin da zuciyarka take marmari. Shin kana son zuwa kwalejin tauhidi? Kana da sha’awar yin karatu da kuma girma a cikin saninka na Littafi Mai Tsarki, tauhidi, da tarihin ikilisiya? Shin kana da sha’awar ra’ayin ciyar da sauran rayuwarka kana koyarwa ko rubutu game da abubuwan bangaskiya? Shin kana ɗokin samun damar yin kiwon mutanen Allah ta cikin hawan-da-saukan na rayuwar Kirista da kuma tafiya tare da su sa’ad da suke wucewa ta “kwarin inuwar mutuwa” (Zab. 23:4)?
Waɗannan kaɗan ne daga cikin tambayoyin da nake yi wa kaina shekaru da yawa da suka wuce yayin da nake kokawa da abin da Allah yake so a gare ni. Ina iya tunawa ina karanta Littafi Mai Tsarki na wata safiya kuma na fahimci cewa ina so in shafe sauran rayuwata ina nazarin Maganar Allah kuma ina koyar da ita ga mutanen Allah. Idan kana jin irin waɗannan marmari a cikin kanka, to ya kamata ka yi la’akari da zuwa kwalejin tauhidi. Samun irin waɗannan sha’awoyi matakin farko ne na dole wajen tantance abin da Allah yake so ka aikata.
Amma idan ba ka da tabbacin yadda kake ji fa? To zan ƙarfafa ka ka ɗauki wani darasi ɗaya a kwalejin tauhidi don ka gani ko za ka so shi. Halarci darasin ɗin kai-tsaye kuma don samun kiredit idan za ka iya. Wannan zai ba ka cikakken hoto gwargwadon iko na yadda zama ɗalibi yake da kuma abin da ake buƙata don kammala digiri. Shin kana jin daɗin karatun da aka bayar da kuma bincike? Shin kana ɗokin jiran lokacin karatu? Shin kana jin Kwarin gwiwa da farin ciki sa’ad da kake tattauna darasin da abokan ajinka ko abokanka da iyalinka? Kuma, wataƙila mafi mahimmanci, shin darasin ɗin yana sa ka so ka ƙara ɗaukar wani?
Na biyu, zan ƙarfafa ka ka yi magana da waɗanda suka fi saninka. Tambaye su abin da suke gani a tare da kai. Shin suna ganin sha’awar nazarin Littafi Mai Tsarki da koyar da shi a cikin ka? Shin sun lura da wata baiwa da ba a saba gani ba a cikinka na fahimta, amfani da ita, da kuma isar da Maganar Allah? Shin suna ganin baiwar sanya ayoyin Littafi Mai Tsarki masu wuya su zama da sauƙin fahimta? Shin sun shaidi tausayi a cikinka ga mutanen Allah?
Wannan ya kasance ɗaya daga cikin abubuwa mafi taimako a gare ni a nawa tafiyar. Matata da aminai na kusa duk sun gaya mini cewa ya kamata in je kwalejin tauhidi. A duk lokacin da na koyar a makarantar Lahadi ko na jagoranci nazarin Littafi Mai Tsarki, mutane kan zo gare ni bayan an gama su kuma ƙarfafa ni in je. Fastona ya taka muhimmiyar rawa a wannan tsarin ma. Shaidar gama-gari daga dukkan waɗannan hanyoyin ta zama tabbacin abin da nake ji a cikin raina tun farko. Ya taimake ni in ga cewa ba hauka nake yi ba don yin tunanin barin aiki mai albashi mai tsoka da kyakkyawar makoma domin in koma makaranta.
Idan kana jin sha’awar zuwa kwalejin tauhidi kuma wadanda suka fi kusa da kai suna karfafa ka a wannan turba, to ina ganin ya kamata ka je. Ba lallai ne sai ka fahimci komai ba kafin ka dauki mataki. Allah zai amsa dukkan tambayoyinka a lokacin da ya dace, kuma zai yi amfani da darasoshinka, da daliban ajinka, da malaman kwalejin don yin hakan. Haka kuma ba lallai ne ka shirya kowane daki-daki ba kafin ka fara. Allah zai tanada maka yayin da kake ci gaba. Yi addu’a, kuma ka fita da bangaskiya. Yi roko mai girma ko kuma, a cikin kalaman mai zabura, “ka bude bakinka fadi,” domin Ubangiji ya yi alkawarin cewa “zai cika shi” (Zabura 81:10). Amince da maganarsa. Yi tafiya ta wurin bangaskiya ba ta wurin gani ba. Kuma, yayin da kake yin haka, addu’ata ita ce Allah namu mai girma da Sarki zai yi amfani da kai matuka na shekaru masu zuwa, duka domin yabon alherinsa mai daraja.
An fara wallafa wannan talifi ne a shafin Blog na Ministirin Ligonier. [Blog ɗin Ministirin Ligonier]


