30/04/2026
Labarin ceto a cikin Littafi Mai Tsarki ya fara ne da zarar Adamu ya faɗa cikin zunubi. Maimakon ya bar Adamu da Hauwa'u cikin halin ƙiyayya na dindindin da kansa, Allah ya gaya wa macijin cewa zai "saka ƙiyayya tsakaninka da matar, da tsakanin zuriyarka da zuriyarta." Sai Allah ya ƙara wannan alkawari mai ban sha'awa: "Zai ƙuje kanka, kai kuma za ka ƙuje diddigensa" (Farawa 3:15). Wannan sanarwa ce ta yaƙi da Allah ya yi da macijin, kuma sanarwa ce ta alheri ga Adamu da Hauwa'u.








