Gyaran Koyarwar Ceto a ƙarni na Sha Shida

19/05/2026

Gyaran Koyarwar Ceto a ƙarni na Sha Shida

19/05/2026

Mene ne Tabbacin Gafara?

Mutane dayawa a duniya, waɗanda ba su ɗauki addini da muhimmanci ba, amma har wa yau suna nan sane da daɗaɗɗen furcin nan na Roman Katolika mai cewa, “Ka albarkace ni Uba, domin na yi zunubi” furcin da ɗan ɗarikar kan furta sa’adda ya shiga keɓaɓɓen ɗakin furta laifofi tare da Firist. Kalmomi ne da suke matuƙar bayyana zahirin kasancewar zunubi da buƙata ta alheri. Me kan faru bayan wannan yanayi? Za a mayar da martani bayan furta jerin zunubai, sai firist ya ba da wasu matakan da za a bi na tuba, daga ƙarshe kuma ya furta yafewa. Aƙidar Masu Gyara (The Reformers) ita ma ta nanata muhimmancin furta zunubi da karɓan gafara, amma akwai wasu muhimman bambance-bambance.

Bambanci na farko shi ne, ga wa muke furta zunuban. Tun da yake Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa “matsakanci ɗaya ne tsakanin Allah da mutane, Mutumin nan, Kristi Yesu”(1Timoti 2:5), mun ba da gaskiya cewa wanda kaɗai zai iya magance irin saɓani da zunuban mu ya jawo shi ne Kristi, ba wani firist ɗan Adam ko kuma wani fasto ba. Muna furta zunuban mu kai-tsaye ga Allah, muna roƙo  cikin ikon cancanta na Babban Firist ɗin mu Mai-Girma, Kristi Yesu (Ibraniyawa 4:14-16).

Bambanci na biyu shi ne, ainihin wurin da muka gaskanta cewa, a nan ne ya kamata a furta zunubi. Masu koyarwar Reformed suna ɗauki abin da yakan faru a ɗakin sirri na furta zunubi, su kawo shi gaba-gaɗi a matsayin muhimmin ɓangare na lokacin sujada ta jama’a duka.

Cikin ƙarnoni da dama, wani tsayayyen tsarin sujada na Koyarwar Reformed shi ne ɓangare na”tsarkakewa.” Misalin wannan zai iya kasancewa kamar haka: Za a karanta Maganar Allah, mutane za su furta zunuban su a martanin abin da aka karanta, sannan mai bisharar zai furta gafara ga waɗanda suka gaskanta da Kristi Yesu.

Mene ne ya sa ake mai da wannan a matsayin wani ɓangare na sujaradar taron jama’a gaba-ɗaya? Furta zunubai yakan kasance abu da mutum zai yi a keɓe, kuma tsakanin shi da Allah. Mai yiwuwa ka taɓa jin wani iri a lokacin sujada na ikklisiya sa’adda aka buƙaci ka tashi kai-tsaye ka furta zunuban ka na makon da ya wuce. Ikklisiyoyi da dama sun yi watsi da duk wani abu da ya shafi karanta dokoki ko furta zunubi, musamman domin ba su so mutane su kasance cikin taƙura. Amma ikklisiya ta Reformed sun nace kan wata hanya, dalili kuwa ya shafi tsarin ibada.

Ibada matsayi ne na saduwa da Allah, kuma mutane masu zunubi ba za su iya shigowa gaban Allah Mai Tsarki ba. Furta zunubi da shaida adalcin da ke samuwa cikin Kristi Yesu babban tuni ne cewa, idan ba ta hanyar bishara ba, ibada ba za ta yiwuwa ba. Gaba da haka ma, ibada ta kasance ne domin ta ba da siffa da ƙarfafawa ga ɗabi’un Krista. A kasancewar mu Krista, mu masu zunubi ne, haka nan ma tsarkaka ne, kuma duka wadannan biyun suna da muhimmanci (1Yahaya1:8-9).

A sujada ta taron jama’a duka, akan kai wani lokaci na murna da farin ciki, wanda mai wa,azi zai furta gafara da muke da ita cikin Kristi Yesu, tare da nanata mana matsayin mu na masu zunubi da aka ceto ta dalilin alheri―waɗanda aka zaɓa kuma masu daraja a gaban Allah.

Wannan ya kai mu ga bambanci na uku da ke tsakanin Roman Katolika da ta Reformed game da gafara: Me ke faruwa sa’adda mai wa’azi ya sanar da gafara. Ba wai mai wa’azi yana kafa doka na wani abu bane sa’adda ya yi haka, amma kawai yana shaida abin da dama can ya ke tabbataccen gaskiya bisa ga Littafi Mai Tsarki.  Akasin wannan “yantarwa” (daga Kalmar Latin na absolvere, mai nufin “a ‘yantar”) shi ne yanayin da firist a fili zai ‘yantar da mutum daga hakkin zunuban su. Sai dai kuma ɗan Adam ba shi da ikon gafarta zunubi (Markus 2:7), ko dayake akwai iko na yin wa’azin cewa ana gafarta zunubai (Ayukan Manzanni 13:38). A wannan muhimmin lokacin sujada na Koyarwar Reformed, mai wa’azi yana tsaye ne a madadin Allah―ba a matsayin Allah ba―kuma daga bakin shi ne muke jin maganar gafara da rahamar Allah gare mu: “Saboda haka a yanzu, babu sauran kayarwa ga waɗanda suke na Kristi Yesu” (Romawa 8:1).

Wannan shi ne dalilin da ya sa furcin yafewa a ikklisiyoyin Reformed da dama kan ƙunshi karanta wani nassi na Littafi Mai Tsarki da a fili yake bayyana gafara da bege da ke cikin bishara. A cikin Maganar Allah da alƙawarin Sa ne muke samun tabbaci na gafarar mu.

Ɗauke da wannan a zuci, furta gafara yana ɗaya daga cikin muhimman batutuwa na lokacin sujadar Reformed. Zunubi yana kayar da mu, amma bishara tana ɗaga mu sama (dubi Zabura 32:3-5). Shi ne abin da ke zuga begen mu, da kuma ƙarfin biyayyar mu. Ibada lokaci ne na saduwa da “Allahn dukkan alheri” (1Bitrus 5:10) ―Allah wanda ke nuna ƙauna ga ‘yan tawaye da basu cancanci kulawar Sa ba, Shi ne wanda ya zama, kamar yadda Dauda ya faɗa, ‘Mai- daka kaina” (Zabura 3:3). Shi ne Allah wanda ke da “jinkirin fushi, Mai yalwar ƙauna da gaskiya” (Fitowa 34:6). A sujada ta taron jama’a, zuciyar Sa tana nan bayyane a fili, haka yake musamman ma a lokacin furci na gafara.

An riga an gafarta ma waɗanda suka riga suka gaskanta da Kristi kafin ma mai wa’azi ya furta hakan. Ba wai akwai wani taƙamammen abu da ke canzawa a cikin mu, ko a tsakanin mu da Allah a wannan lokacin ba. Duk da cewa an gafarta mana, amma muna yawan mantawa, wannan kan kai mu ga yin shakka da rashin biyayya. Saboda haka, Tabbacin Gafara, tuni ne da muke buƙata na ko su wane ne mu a matsayin mutanen Allah: “Da ku ba jama’a ta bane, amma yanzu ku jama’ar Allah ne; da ba ku sami jinƙai ba, amma yanzu kun sami jinƙai” (1Bitrus 2:10).


An fara buga wannan labarin a shafin yanar gizon Ministirin Ligonier. [Blog ɗin Ministirin Ligonier]

Jonathan Landry Cruse

Jonathan Landry Cruse

Reverend Jonathan Landry Cruse fasto ne na Community Presbyterian Church a garin Kalamazoo, a Michigan, wurin da yake zama da matar sa da kuma ‘ya’yan sa. Ya rubuta waƙoƙi sama da hamsin, da kuma litattafai da dama, waɗanda suka haɗa da Hymns of Devotion, The Christian’s True Identity da kuma The Character of Christ.