
Mene ne Tabbacin Gafara?
21/05/2026
Ko Allah Yana Kula Da Gaske?
28/05/2026Mene ne Furcin Zunubi?
Yayin da kake halartar ibadar wata ikklisiya ta tsarin Reformed, fasto zai iya jagorantar ku zuwa furcin zunubi. Yana iya karanta dokokin Allah tun da fari, sannan ya yi addu’a, ko ya bayyana gafara ta dalilin jinin Kristi. Mene ne wannan furcin zunubi yake nufi? Daga ina wannan al’ada ta samo asali? Ta yaya za ka iya shiga cikinta da aminci fiye da da?
Ma’anar Furcin Zunubi
Yahaya na Farko 1:9 ya ce, “Idan muka furta zunuban mu, to, Shi Mai-Alƙawari ne, Mai-Adalci kuma, zai kuwa gafarta mana zunuban mu, Ya tsarkake mu daga dukan rashin adalci.” Yahaya ya yi amfani da wata kalma wajen nuna “furci” a nan, wadda ke nufin “a faɗi abu daidai Yadda ya ke.” Furtar zunuban mu yana nufin mu yarda da yadda Ubangiji ya bayyana zunuban mu, kamar yadda yake a cikin Littafi Mai Tsarki.
A lokacin sujada na taron jama’a gaba-ɗaya, furtar zunubi wani keɓaɓɓen lokaci ne, wanda sa’adda ake sujada fasto zai jagoranci jama’ar Kristi su amsa su kuma furta zunuban su. Bayan haka zai yi addu’a domin su sami rahamar Ubangiji da aka tanada cikin Kristi.
Asalin Tushe na Furcin Zunubi
A alfarwa da haikali na zamanin Tsohon Alƙawari, Ubangiji ya umurta cewa ƙofar tsakar-gidan za ta fuskanci wajajen gabas (Fitowa 27:13). An zaɓi wannan kusurwa domin an kori Adamu da Hauwa’u wajen lambun Aiden ta gabashin ne, a bayan da suka faɗi cikin zunubi (Farawa 3:24). Wannan ƙofar ta kasance kira ne na alheri ga Isra’ila su koma ga Allah.
Abu na farko da masu yin ibada suke gani idan sun shigo shi ne bagadi. Sa’adda suka shiga, masu ibada kan tsaya, su dafa hannuwan su akan dabbar hadaya, sannan su furta zunuban su a lokacin ɗaya firist yana miƙa hadayar ga Allah Mai Tsarki. Wannan hidima tana tuna masu cewa, “ in ba da zubar da jini ba kuwa, to, babu gafara na zunubi” (Ibraniyawa9:22; dubi kuma Littafin Firstoci 17:11).
Ibraniyawa 9:10-22 ya haskaka waɗannan baye-baye don nuna cewa su dabbobin nan ba su da ainihin ikon tsarkakewa na gaskiya. Makamancin haka kuwa mun karanta cewa, “Balle fa jinin Kristi, wanda ya miƙa Kansa marar aibu ga Allah ta wurin madawwamin Ruhu, za ya tsarkake lamirin mu daga matattun ayuka, zuwa ga bauta ma Allah Rayayye” (Ibraniyawa 9:14).
Domin a nuna buƙata na jinin Kristi don zuwa wurin Allah, yawancin tsarin ibadar Reformed suna Sanya furcin zunubi a farkon ibadar taro. John Calvin ya sa taron masu sujada a Geneva da Strasbourg suna fara ibada da furta shaida cewa:
Taimakon mu na cikin sunan UBANGIJI,
Wanda ya yi Sama da duniya, Amin. (Zabura 124:8)
Abin da kan biyo baya shi ne furcin zunubi da jama’a duka za su yi. Kamar yadda Calvin ya ce,
Tabbas , a ikklisiyar da ke da kyakkyawar tsari, na tabbatar da kyawawan ɗabi’u, a kowace ranar sujada, shi fasto yana tsara hanya ta furtar zunubi na shi kansa da kuma na jama’a, a yadda zai furta zunubi, da yin neman gafara daga wurin Ubangiji. (Daga Institude 3.4.11)
Ta dalilin tasirin Calvin da wasu, wannan ɗabi’a ta sami yaɗuwa. Littafin Westminister Directory Of Public Worship na cewa, ya kamata ibada ta fara da “amincewa da girman Allah da ɗaukakar Sa wadda ta wuce misali, ( wanda a gaban sa ne suke bayyana cikin tsari na musamman) da yarda da nasu muni, da rashin daraja na kusantar Shi.” Wannan littafi ya ci gaba da bayyana takamamme irin hanyoyi da dama da za a amsa, a kuma furta zunubi. A matsiyin magada na ruhaniya, Wannan aƙida ta Masu-Gyara ta kai har zuwa gare mu.
Aiwatar da Furcin Zunubi
Ga wasu hanyoyi uku na yadda za a sami aiwatar da furcin zunubi cikin ainihin gaskiya.
- Mu yarda da girman zunubin mu.
Yawancin lokaci mukan fi mai da hankali ne kan zunubin da aka aikata. Amma kuma babban abu muhimmi shi ne, Shi wanda muka yi wa zunubin.
Idan ka zana gashin-baki a kan wani zanen mutum da na riga na yi, laifi ba zai zama babba ba. Don me? Domin da ma ni ban iya zane ba. Amma idan ka je Louvre, sannan ka sami yin zanen wannan gashin-baki a kan Mona Lisa ɗin Da Vinci (wani shahararren mai zane) za ka shiga babban matsala. Sakamako ko hukuncin wannan abu babba ne, ya zama ka lalata shahararren aikin gwaninta.
Makamancin haka shi ne, aikata zunubi ga Shugaban dukan halitta, babban laifi ne sosai. A lokacin da Dauda ya furta zunubin sa na aikata zina da Barsheba da kuma kashe mijin ta―mutum biyu da aka halitta cikin sifar Allah―ya ce, “Kai, Kai kadai na yi maka zunubi”(Zabura 51:4).
- Yi matuƙar bakƙin ciki kan yadda zunubin mu takan shafi jama’a.
CIkin addu’ar Ubangiji, mukan ce, Ka gafarta mana laifofin mu” (Matiyu 6:12). Ruhun Kristi ya haɗa mu cikin tarayya da sauran jama’a na ikklisiya. Zunubin mu yakan yi tasiri kan ikklisiya, don haka dole ne mu furta zunuban mu tare.
Bulus ya ce, “Ba ku sani ba ku haikali ne na Allah, kuma Ruhun Allah yana zaune a cikin ku?” (1Korintiyawa 3:16). Kalmar da aka mora a wannan aya “ku” tana nuna jam’i. Zunubai a jikin Kristi (ikklisiya) abin ƙyama ne, domin Allah mai tsarki yana zama a wurin. Ita ikklisiya tana nan kamar ɗaki kyawawan zane da Allah ya yi ne, sannan kuma “fentin” da ke sa mu zama masu kyau shi ne jinin Kristi (Ibraniyawa 10:28-31). Kamar yadda Thomas Watson ya ce: “ Zunubin miyagu yana tayar da fushin Allah. Zunubin mutanen sa yana baƙanta mashi rai.”
- Mu nuna cikakkiyar bakin ciki kan zunuban mu zunubin mu
Tarihi na Littafi Mai Tsarki ya ƙunshi misalai da yawa na yanayi daban-daban wanda Isra’ilawa suka furta zunuban su, misali, a lokacin da Ubangiji ya aika mugayen macizai bayan da Isra’ila suka yi gunaguni a cikin jeji ( Littafin Kidaya 21:7), ko a lokacin da jama’a suka dawo daga bauta domin su sake gina ganuwar Urshalima (Nahemiya 9:1-3). Sa’adda kake karanta waɗannan bayanai, za ka ji nadamar mutanen Allah. Mai yiwuwa ikklisiyar ku ba ta faɗi ta kai wannan matsayi na ƙasƙanci ba, amma duk wani irin zunubi da aka aikata ga Allah, dole ne ya jawo baƙin ciki. Zabura da yawa wanda akan karanta ko a raira domin furtar zunubi, yakan nuna makoki daga zuciya saboda laifofin mu. Ya kamata waɗannan kalamai na furtar zunubi su zama abu na kullum, wanda ya kasance lallai ikklisiya tana aiwatarwa. Kamar yadda Martin Luther ya ce, “Saboda haka, sa’adda na ƙarfafa ku ga furtar zunubi, Ina ƙarfafa ku ne da ku kasance Krista.”
An fara buga wannan labarin a shafin yanar gizon Ministirin Ligonier. [Blog ɗin Ministirin Ligonier]


