26/05/2026
Furtar zunuban mu yana nufin mu yarda da yadda Ubangiji ya bayyana zunuban mu, kamar yadda yake a cikin Littafi Mai Tsarki. A lokacin sujada na taron jama’a gaba-ɗaya, furtar zunubi wani keɓaɓɓen lokaci ne, wanda sa’adda ake sujada fasto zai jagoranci jama’ar Kristi su amsa su kuma furta zunuban su. Bayan haka zai yi addu’a domin su sami rahamar Ubangiji da aka tanada cikin Kristi.
