21/05/2026
Tun da yake Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa “matsakanci ɗaya ne tsakanin Allah da mutane, Mutumin nan, Kristi Yesu”(1Timoti 2:5), mun ba da gaskiya cewa wanda kaɗai zai iya magance irin saɓani da zunuban mu ya jawo shi ne Kristi, ba wani firist ɗan Adam ko kuma wani fasto ba. Muna furta zunuban mu kai-tsaye ga Allah, muna roƙo cikin ikon cancanta na Babban Firist ɗin mu Mai-Girma, Kristi Yesu (Ibraniyawa 4:14-16).
