
Mene ne Manufar Allah a cikin Giciyen?
24/11/2025
Yesu Kristi: Ɗan Ragon Allah
24/11/2025Matsayin Addu’a
Mene ne manufar rayuwa ta Krista? Tsattsarkar rayuwa tana samuwa ne ta hanyar biyayya ga Kristi. Biyayya tana buɗe albarku da ke cikin rayuwa ta Krista. Addu’a ita ce ke haifarwa da kuma raya biyayya, tana kuma saka zuciya cikin “matsayin tunani” mai dacewa yadda zai yi sha’awar biyayya.
Ƙwarai, ilimi shi ma yana da muhimmanci, domin in ba tare da shi ba, ba za mu iya sanin abin da Allah ke buƙata ba. Amma kuma idan ba mu yi zumunta da Allah cikin addu’a ba, to ilimi da kuma gaskiya za su kasance kawai cikin tunani amma ba abu na zahiri ba. Ruhu Mai Tsarki Shi ne yake koyarwa, da zuga zuciya, da kuma kawo hasken Kalmar Allah gare mu. Yana ɗaukan Kalmar Allah, sannan Ya taimaka mana mu amsa Uban ta hanyar addu’a.
Addu’a muhimmin abu ne a rayuwar Krista. Na farko, ainihin abu ne da ake buƙata domin ceto. Akwai mutane da ba su jin magana; duk da cewa kurame ne, suna iya samun ceto. Wasu ba su iya gani; amma duk da makantar su, suna iya samun ceto. Sanin Labari Mai Dadi – ceto ta wurin hadayar mutuwa da tashin Yesu Almasihu daga matatu – zai zo ne daga wata hanya ko wata, amma a ƙarshe zancen, dole ne mutum cikin ƙasƙancin ya roƙi ceto daga Allah. Addu’ar neman ceto ita ce kaɗai addu’ar mugu wadda Allah ya ce zai ji.
Mene ne abin da wadanda suke sama suna da shi iri daya?? Akwai abubuwa dayawa. Dukansu kuɓutattu ne, da yake sun sa bangaskiyar su cikin hadayar Kristi. Dukan su suna yabon Allah. Kuma dukan su sun yi addu’ar neman ceto. Kasancewa babu addu’a ya zama kenan kasancewa babu Allah, babu Kristi, da Ruhu Mai Tsarki, da kuma bege da tabbacin Sama.
Na biyu, ɗaya daga cikin tabbatacciyar alamar Krista ita ce rayuwar addu’ar sa. Mutum na iya yin addu’a amma kuma shi ba Krista bane, amma Krista ba zai iya rayuwa baya addu’a ba.. Romawa 8:15 ya gaya mana cewa karɓan mu da aka yi cikin ruhaniya wanda ya sa muka zama ‘ya’yan Allah ya ba mu dama muna iya kira muna furta cewa: “Ya Abba! Uba.” Ga Krista dai Addu’a ta kasance kamar yadda numfashi ya ke ga rai, sai dai kuma, babu wani ɓangare na ayukan rayuwar Krista da ake banza da shi kamar addu’a.
Zai zama da wuya mutum ya rudi kansa cikin addu’ar kadaici. Mutum na iya yin wa’azi da manufar rudi, kamar yadda yake kasancewa da annabawan ƙarya; mutum na iya yin hidima na Krista bisa dalilian ƙarya. Dayawa daga cikin ayuka na hidimomin Krista ana iya aiwatar da su bisa dalilan ƙarya, amma zai iya zama da wuya a ce mutum yana zumunta da Allah saboda dalilai marasa dacewa. Matiyu 7 ya gaya mana cewa a “ranar ƙarshe” dayawa za su tsaya a gaban shari’a suna gaya wa Yesu manya da kyawawan ayukan da suka aikata cikin sunan sa, amma amsar sa ita ce bai san su ba.
Domin haka ana gayyatar mu, har ma da umurtar mu, mu yi addu’a. Addu’a dama ce, kuma aiki ne da ya zama wajibi, haka kuwa fa duk wani aiki yana iya zama da wuya. Addu’a tana buƙatar aiki, kamar yadda ya ke ga kowane hanyar samun girma ga duk Krista. Kai har ma ta wani gefen addu’a ta zama abu baƙo a gare mu. Duk da yake an halicce mu domin zumunta da hira tare da Allah, sai dai sakamakon faɗuwa ya sa dayawan mu sun zama ragwaye, ba mu damu da abu mai muhimmanci kamar addu’a ba. Sake haihuwa yana farfaɗo da kuma sabonta sha’awa na zumunta da Allah, amma zunubi tana tsayayya da Ruhu.
Muna iya samun ƙarfafawa daga gaskiyar cewa Allah ya san zukatan mu, kuma yana jin kukan mu na zuci wadda ba mu iya furtawa ba, fiye ma da kalmomin da ke fitowa daga bakunan mu. A duk lokacin da muka kasa iya bayyana zurfafan tunani da muraɗin zukatan mu, ko sa’adda gaba daya ma muka kasa fahimtar abin da ya kamata mu yi addu’a a kai, Ruhu Mai Tsarki yakan yi a madadin mu. Romawa 8:26-27 ya ce,
Ruhu yana yi mana taimako cikin kasawar mu, domin ba mu san abin da ya kamata mu roƙa ba, amma Ruhu da kan sa yana yi mana roƙo da nishe-nishen da ba su furtuwa. Kuma shi mai fayyace zukatan mu ya san abin da Ruhu yake niyya, domin bisa ga nufin Allah ne Ruhu yake yi wa tsarkaka roƙo. Sa’adda ba mu san yadda za mu yi addu’a ba, ko abin da za mu yi addu’a a kai ba cikin wani yanayi, Ruhu Mai Tsarki yana taimaka mana. Daga wannan nassi, akwai nunin cewa ta yiwu ma idan ba mu yi addu’a yadda ya kamata ba, Ruhu Mai Tsarki yana gyara kurakuran da ke cikin addu’o’in mu kafin ya kai su ga Uban, domin aya ta 27 ta gaya mana cewa “bisa ga nufin Allah ne Ruhu yake yi wa tsarkaka roƙo.”
Addu’a ita ce sirrin rayuwar tsarki– wato idan har rayuwar tsarki tana da wani sirri. Idan muka binciki rayuwar manyan tsarkaka na Ikklisiya, za mu ga cewa su manyan mutane ne ta ɓangaren addu’a. John Wesley ya taɓa cewa, bai ɗauki masu aikin bishara, waɗanda ba su addu’a na aƙalla sa’o’i hudu kowace rana da wani muhimmanci ba. Luther kuma ya ce, yana addua’a na aƙalla sa’a ɗaya kowace rana, sai dai idan har wasu hidimomi sun cunkushe masa a ranar. In ba haka, yakan yi addu’a na sa’o’i biyu.
Yin watsi da addu’a ya kasance babban dalili na rashin ci gaba a rayuwar Krista. Dubi misalin Bitrus a Luka 22:39-62. Yesu ya tafi yin addu’a a Dutsen Zaitun kamar yadda ya saba, ya gaya wa almajiran sa, “Ku yi addu’a kada ku faɗa ga gwaji.” Maimakon haka sai almajiran suka yi barci. Abin da Bitrus ya yi ƙoƙarin yi daga nan shi ne ya tunƙari sojojin Romawa da takobi; sannan kuma ya yi musun sanin Kristi. Bitrus bai yi addu’a ba, dalilin haka ne ya faɗa cikin jaraba. Gaskiyar wannan yanayi na Bitrus ya kasance gaskiyar yanayi a gare mu a yau. Mukan faɗi a ɓoye kafin mu zo ga faɗuwa a fili.
Ko akwai wani lokaci mai dacewa ko marar dacewa domin yin addu’a? Ishaya 50:4 ya yi magana akan safiya a matsayin lokacin da Allah yake ɗora nauyin yin addu’a a kullayomin, da kuma sabonta aminci ga Allah. Amma akwai wasu nassoshi da ke nuna dukan lokaci cikin wuni a matsayin lokacin addu’a. Babu wani lokaci cikin wuni wanda aka keɓe na musamman cewa ya fi tsarki fiye da wani domin yin addu’a. Yesu ya yi addu’a da safe, da rana, wani lokacin ma har na tsawon dare. Akwai shaidar cewa yana da lokaci da ya keɓe don yin addu’a; amma duk da haka, ganin irin dangantakar da Yesu ke da ita tare da Uban, mun sani cewa zumunta tsakanin su ba ta taɓa yankewa.
1 Tasalonikawa ta5:17 ya umurce mu da mu yi addu’a ba fasawa. Ma’ana kenan ya kamata a kullayomi mu kasance cikin halin zumunta da Uban mu.
An taɓa bugawa cikin Does Prayer Change Things daga R.C. Sproul.
An fara buga wannan tsararren rubutu ne a shafin ma’katar bishara ta Ligonier.


