
Matsayin Addu’a
24/11/2025
Mene ne Muke Nufi Sa’adda Muke Magana Kan “Darajar Ran Ɗan Adam”
28/11/2025Yesu Kristi: Ɗan Ragon Allah
Wannan ra’ayi na Ɗan Ragon Allah ya zama kamar igiya ne da ya ratsa duk cikin tarihin fansa. Za a iya gano shi idan aka yi waiwaye baya zuwa Farawa 22, lokacin da Allah ya kira Ibrahim ya je Dutsen Moreya, ya ba da ɗan sa Ishaku a matsayin hadaya. Ibrahim kuwa, cikin biyayya ga Allah, ya shirya aikata hakan, amma da ya kai lokacin aiwatarwa, bayan Ibrahim ya ɗaure Ishaku bisa itacen bagadi, yana shirin ɗora ma shi wuƙa a zuciyar sa, Allah ya hana shi, yana ce masa “Kada ka sa hannun ka a kan saurayin, kada kuwa ka yi masa wani abu, gama yanzu na sani kai mai tsoron Allah ne, da yake ba ka ƙi ba da ɗan ka, tilon ka, gare ni ba” (aya ta 12). Sai ga wata hayaniya a bayan Ibrahim, ya juya sai ya ga rago da ƙahonsa ya sarƙaƙe cikin kurmin daji. Allah ya tanadar da ɗan rago na hadaya a maimakon ɗan Ibrahim. Tabbas ba a bayyana a Farawa 22 cewa wannan rago da Ibrahim ya kama, ya yi hadaya a maimakon Ishaku ya zama hadayar kaffara ba. Amma duk da haka, ya kasance hadayar ta musaya, kuma wannan shi ne ra’ayin da ke dunƙule cikin kaffarar Kristi. Yesu ya kasance musaya, kuma ta dalilin zunuban mu, Allah ya zuba fushin sa mai ƙuna a kan Sa, a maimakon mu. Haka nan Allah ya tanadar da Ɗan Rago Nasa, kuma ya karɓi ran wannan da aka yi musaya.
Haka nan kuma, An yi nuni na wannan Ɗan Ragon Allah a lokacin Ƙetarewa. Sa’adda Allah ya yi shirin sauko da annoba kan Masarawa, na mutuwar kowane ɗan farin Masarawa namiji, har da ɗan Fir’auna yarima, Ya umurci mutanen Sa su yanka ‘yan raguna marasa tabo, sannan su shafa jinin a dogaran ƙofofin su. Allah ya yi alƙawarin zai tsallake duka gidajen da ya ga jinin ‘yan raguna a bisa kofofin (Fitowa 12:3-13). Kamar yadda jinin waɗancan ‘yan raguna ya sa Allah ya jiƙan ‘ya’yan Isra’ila daga fushin sa, haka nan Ɗan Ragon Allah ya Fanshi Mutanen sa daga hukuncin da ya daidaici zunubin su.
Ganin waɗannan hotuna daga Farawa 22, da Fitowa 12, da wasu nassoshi duk cikin Tsohon Alƙawari, zai kasance wauta a ce manzo Yahaya ne ya ƙirƙiro wannan suna na “Ɗan Ragon Allah.” Kalaman Yahaya mai Baftisma sun samu ne ta dalilin ilimin sa na Tsohon Alƙawari da Nassoshi masu tsarki na Yahudawa a zamanin Kristi.
Duk da yawan muhimman sunaye da aka yi amfani wa Yesu cikin sura ta farko na littafin Yahaya-“Ɗan Ragon Allah,” “Ɗan Allah,” “Almasihu,” “Ɗan Mutum,” da dai sauran su- ban yarda cewa Yahaya Mai Baftisma, da Andirawus, da, Nataniyel, ko wani daga cikin almajiran ya kasance da cikakkiyar fahimta na ma’anonin waɗannan sunaye ba. Yahaya Mai Baftisma , wanda ya ce, “Kun ga! ga Ɗan Ragon Allah wanda zai ɗauke zunuban duniya!” daga baya an zo an jefa shi cikin kurkuku, har ya aika ‘yan saƙo wurin Yesu, yana tambaya, “Kai Ne Mai Zuwa, ko kuwa mu sa ido ga wani?” (Luka 7:20). Wannan tambaya ta nuna cewa Yahaya bai kasance da cikakkiyar fahimta na asalin Yesu ba, duk da gagarumin shaida na asalin Yesu. Matsalar ita ce, shi ma ya kasance da irin nasa tunanin. Yana tunanin cewa Ɗan Ragon Allah zai zo ya kawar da Romawa, kamar yadda wasu suka yi a baya. Da ya ga Yesu tafiya yana yin wa’azi ne kaɗai, sai ya zama a rikice.
Yesu ya gaya wa ‘yan saƙon Yahaya cewa, “ ku je ku gaya wa Yahaya abin da kuka ji da abin da kuka gani. Makafi na samun gani, guragu na tafiya, ana tsarkake kutare, kurame na ji, ana ta da matattatu, ana kuma yi wa matalauta bishara” (Luka 7:22). Yesu ya yi nuni ga ayukan Sa na alajibi domin tabbatar da asalin sa ga Yahaya wanda ke shakka. Ya kuma yi nuni ga annabcin da ya bayyana shi Almasihu ne cikin Ishaya 61:1-2a, wadda ke cewa:
Ubangiji ya saukar mani da ikon Sa.
Ya zaɓe ni, ya aike ni
Domin in kawo albishir mai daɗi ga talakawa,
In warkar da waɗanda suka karai a zuci,
In yi shelar kwance ɗaurarru, da kuma ‘yanci
ga waɗanda suke cikin kurkuku. Ya aike ni In yi shela,
Cewa lokaci ya yi da Ubangiji zai ceci mutanen Sa.”
Ya zama kamar Yesu yana cewa: “Yahaya, da ka yi kyakkyawan bincike na Littafi Mai Tsarki, da ba za ka yi tambayoyi na ko nine shi wanda ya zo ba. Ba sai ka sa ido jiran wani ba kuma. Ka faɗi daidai tun can da farko, Ni ne Ɗan Ragon Allah.”
Haka nan ma Bitrus ya kasance cikin ruɗani, duk kuwa da cewa ya bayar da babban shaida a Kaisariya Filibi. Da yake amsa tambayar Yesu na ko wa almajiran Sa suke tunani yake, Bitrus ya ce “Kai ne Almasihu, Ɗan Allah Rayayye” (Matiyu 16:16). Yesu ya tabbatar da cewa wannan ikirari zahiri ne, kuma ya furta “albarka” a kan Bitrus, domin ya gane ko wanene Shi. Amma ba da daɗewa ba bayan wannan lokacin, da Yesu ya gaya wa almajiran sa cewa, lallai ne ya tafi Urshalima ya sha wuya ya mutu, sai Bitrus ya tsawata Masa, ya ce “ Wannan ba zai same ka ba!” (16:22b). Cikin minti ɗaya Bitrus ya tabbatar cewa Yesu Shi ne Almasihu, amma cikin mitin da ya biyo baya kuma ya nuna cewa bai ainihin fahimci mene ne ma’anar Yesu ne Almasihu ba.
Mu ma muna da saurin shiga irin wannan yanayi na ruɗani. Abin da kaɗai zai taimake mu mu iya ganin zurfin hikima da wadata na saƙon da Allah yake shela ta hannun manzon Sa, wanda ya ce, “Kun ga! Ga Ɗan Ragon Allah, wanda zai ɗauke zunubin duniya!” shi ne idan muka dubi hoton yanayin gaba ɗayan sa, muna la’akari da giciyen, da tashin sa daga matattu, da komawar sa Sama, da kuma saukowar Ruhu Mai Tsarki a ranar Fentakos
An tsakuro wannan rubutu ne daga sharhin da R.C. Sproul ya yi kan Littafin Yahaya.
An fara buga wannan tsararren rubutu ne a shafin ma’katar bishara ta Ligonier.


