
Yesu Kristi: Ɗan Ragon Allah
24/11/2025
‘Yancin Zaɓi: Me Wannan Ke Nufi?
01/12/2025Mene ne Muke Nufi Sa’adda Muke Magana Kan “Darajar Ran Ɗan Adam”
Bisa ga tsarin Littafi Mai Tsarki, darajar ran ɗan Adam ta kafu da tushin ta cikin aikin halitta. Ɗan Adam ba wai wani hatsari ne da ya faru kwatsam a duniya ba, amma halitta ne wanda cikin natsuwa da kulawa Allah madawwami ya yi shi. Martabar ɗan Adam na da tushen ta daga Allah. Mutum a matsayin wand ke da ƙarshe, mai dogaro ga wani, kuma mara tabbas, halitta ne da Allahn sa ya dora wa matuƙar daraja mai girma.
Labarin halitta cikin Farawa ya tanadar da tushen asali na martabar ɗan Adam:
“Sai Allah ya ce, ‘Bari mu yi mutum cikin siffar Mu, da kamannin Mu, su mallaki kifayen da ke cikin teku, da tsuntsayen sararin sama, da dabbobi, da dukan duniya, da kowane abu mai rarrafe bisa ƙasa.’ Haka nan fa Allah ya halicci mutum cikin siffar Sa, cikin siffar Allah, Allah ya halicci mutum, namiji da tamace ya halicce su.” (Farawa 1:26-27).
Halitta cikin siffar Allah, shi ne abin da ya bambanta ko keɓe ɗan Adam daga duka sauran halittu. Tambari na siffa da kamannin Allah ya danganta Allah da ɗan Adam ta wata hanya ta musamman. Ko dayake babu wani wuri a Littafi Mai Tsarki da ke cewa a dubi mutum kamar Allah, amma akwai babban martaba mai girma da ke ɗauke cikin wannan dangantaka ta musamman tare da Mahaliccin.
Ko da yake mutum ya rasa tsarkin sa, ammma har yanzu shi dan adam ne. Mundin muna nan a matsayin ‘yan Adam, muna ci-gaba da kasancewa cikin siffar Allah in muka lura sosai. Mu halittu ne masu matuƙar daraja. Duk da cewa ba mu kan matsayi mai dacewa, amma muna da daraja. Wannan shi ne saƙo da ake ta nanatawa sau da dama cikin Littafi Mai Tsarki, saƙon fansa. Waɗannan halittu da Allah ya halitta su ne dai halittun da Ya miƙe domin ya fansa.
Kalamai dayawa na cikin Tsohon Alkawari sun yi magana kan darajar ran mutum a yadda yake cikin halittar Allah, waɗannan sun haɗa da:
“Ruhun Allah ya yi ni;
Numfashin Mai-iko-duka ya ke ba ni rai” (Ayuba 33:4).
“Ku sani, Ubangiji Shi ne Allah!
Shi ne ya yi mu, mu kuwa nasa ne;
Mu mutanen Sa ne, tumakin makiyaya Tasa kuma.” (Zabura 100:3).
“Kaiton wannan da yake muhawara da mahaliccin sa!
Tukunyar da take daidai da sauran tukwane.
Yumɓu za ya ce da wanda ya kwaɓa shi, me ka ke yi?
Ko kuwa aikin ka, ba shi da hannuwa?
Kaiton wanda ya ce ma uban sa, me ka ke haifa?
Ya ce wa mace, me ki ke ɗauke a ciki?
Haka nan Ubangiji ya faɗa, Shi Mai Tsarki na Isra’ila,
Mahaliccin sa: tambaye ni kan al’amura masu zuwa; a kan ‘ya’ya Na,
A kan zancen aikin hannuwa Na, ko ku faɗa mani abin da ya kamata in yi!” (Ishaya 45:9-12)
Amma yanzu, Ya Ubangiji, kai Uban mu ne, mu yumɓu ne,
Kai ne mai yin tukwane da mu:
Mu dukan mu kuma aikin hannun Ka ne. (Ishaya 64:8).
Abun jan hankali shi ne, Yesu Kristi ya ba da bayani mafi muhimmanci na yadda Tsohon Alƙawari ya nuna darajar ran ɗan Adam;
“Kun ji an faɗa wa mutane a da, ‘Ba za ku yi kisan kai ba; da kuma ko wanene ya yi kisan kai ya shiga hatsarin hukunci.’ Amma ina ce maku, ko wanene ya yi fushi da ɗan’uwan sa, ya shiga hatsarin hukunci; kuma ko wanene ya ce wa ɗan’uwan sa ‘kai wofi’ ya shiga hatsarin Jihannama mai wuta.” (Matiyu 5:21-22).
Kalaman Yesu suna da matuƙar muhimmanci ga fahimtar mu na darajar ran ɗan Adam.
A nan Yesu ya faɗaɗa tasirin dokokin Tsohon Alƙawari. Yana magana ne da shugabannin addini waɗanda fahimtar su ta dokoki goman nan ƙanƙanuwa ce kuma ba ta kai ko’ina ba. Masu tafiyar da rayuwa ta kiyaye dokoki a zamanin sa, sun ba da gaskiya cewa idan suka mai da hankali wajen kiyaye dokoki dalla-dalla, za su iya yaba wa kan su da kansu domin irin matuƙar nagartar su. Amma, sun kasa, domin ba su iya gane babban tasirin wannan ba. A cewar Yesu, abin da doka ba ta iya bayyanawa dalla-dalla ba, ya fito a fili cikin ma’anar ta mai faɗi.
Wannan nagarta na dokoki, ya bayyanu cikin yadda Yesu ya sake faɗaɗa hani da aka yi ga aikata zina:
“Kun ji ana faɗi, Ba za ka yi zina ba: amma ina ce ma ku, duk wanda ya dubi mace har ya yi sha’awar ta, ya riga ya yi zina da ita cikin zuciyar sa.” (Matiyu 5:27-28)
A nan Yesu ya bayyana cewa mutumin da ya guje daga aikata zina cikin jiki ba dole ne cewa ya kiyaye duka dokar ba ne. Dokar hana yin zina doka ce mai wuyar fahimta, ta haɗa da cewa, ba kawai ta shafi aikata zinar cikin jiki ba, amma har da duk wani abu da ke tsakanin muguwar sha’awa zuwa ga ita zinar kanta. Yesu ya bayyana muguwar sha’awa a matsayin yin zina cikin zuciya.
Ita dokar ba kawai ta hana wasu munanan halaye da ɗabi’u bane kaɗai, amma bisa ga tsarin ta tana buƙatar wasu halaye da ɗabi’u nagari. Wato, idan an yi hani ga zina, to ana buƙatar nagarta da tsarki.
Idan muka yi amfani da waɗannan tsare-tsare da Yesu ya kafa na hani ga kisan kai, za mu gane a fili cewa, a wani ɓangaren ana so mu guje daga aikata duk wasu abubuwa da suka danganci kisa idan har aka dubi ma’anar ta sosai, sannan kuma ta wani ɓangaren ana ba mu ƙwaƙƙwaran umurni na mu yi duk iyawar mu mu ceci rai, mu inganta ta, mu yi renon rai. Ana buƙata mu guje wa kisa, da duk abin da ke dangin ta, duk a lokaci ɗaya, kuma mu yi duk iyawar mu don inganta rayuwa.
Kamar dai yadda Yesu ya bayyana muguwar sha’awa a matsayin wani ɓangaren zina, haka ma ya nuna yin fushi babu dalili da kuma ɓatanci a matsayin wani ɓangaren kisa. Kamar yadda muguwar sha’awa ta kasance zina a zuciya, haka nan ma fushi da batanci sun zama kisa a zuciya.
Ta ƙara faɗaɗa iyaka na Dokoki Goma, ya kai ga sun haɗa da batutuwa kamar muguwar sha’awa da ɓatanci, ba wai Yesu yana cewa muguwar sha’awa tana matsayi iri ɗaya na shaiɗanci daidai da yin zina cikin jiki ba. Haka ma, Yesu bai ce ɓatanci yana matsayi ɗaya na shaiɗanci daidai da kisa ba. Abin da ya faɗa shi ne cewa, dokar da take hani kan kisa ta haɗa da hani ga duk wani abu da ya shafi raunana ɗan’uwan ka cikin rashin adalci.
Ya ya duk wannan ya shafi batun zubar da ciki? A koyarwar Yesu, mun ga wani ƙwaƙƙwaran nanatawa da ke nuna darajar ran ɗan Adam. Kisa na zuci, kamar yadda ɓatanci ma yake, za a iya saka shi a matsayin kisa da ke “iya faruwa.” Kisa ne da ke iya faruwa domin, alal misali, fushi da ɓatanci suna da yiwuwar kai wa ga ainihin aiwatar da kisa na jiki. Sai dai, ba kullum ne waɗannan ke kai wa ga faruwar haka ba.
Hana yin Fushi da ɓatanci, ba wai domin abin da za su iya haifar wa bane kaɗai, amma domin ainihin illar da suke kawowa ga ingancin rayuwa.
Idan muka danganta muhawara na darajar ran ɗan Adam da batun zubar da ciki, muna kawo muhimmiyar dangantaka ne a kaikaice. Ko da ba za a iya tabbatar da cewa ɗan-tayi ya kasance ainihin mutum mai rai ba, amma babu shakka mutum ne da ke hanyar bayyanuwa. Ta wata hanyar, ana iya cewa ɗan-tayi mutum ne da ke kan ginuwa. Ba wai matsayin yiwuwa da ya tsaya cak bane. Ɗan-tayi mataki mai ci-gaba ne na musamman- ba tare da wata tangarɗa ko wata faruwar ba-zata-ba, zahiri zai kai ga zama cikakken halitta na mutum rayayye.
Yesu Kristi yana ganin dokar da ke kan kisa ba kawai ta shafi ainihin kisa bane kaɗai, amma har da duk wani abu da za a aiwatar wanda zai kai ga yiwuwar kisa. Yesu ya koyar cewa saɓa doka ne a aikata wani abu mai iya kawo yiwuwar kisan ainihin rai. Don haka, waɗanne sakamo ne ke zuwa idan a ainihi aka hallaka rai da ke hanyar zama mutum?
Ainihin hallaka rai da ke hanyar zamowa mutum, ba abu iri ɗaya ne da yiwuwar hallaka ainihin mutum mai rai ba. Waɗannan ba abu iri ɗaya bane, amma sun yi matuƙar kama da juna, ta yadda dole ne mu ɗan dakata, mu yi kyakkyawan tunani na ire-iren sakamako da kan iya faruwa, kafin mu je hallakar da ran da ke hanyar zamowa mutum. Idan wannan bangaren doka bai kunshe cikakke da kuma gaba daya batun zubar da ciki a cikin haramcin kissan kai ba, ya kamata bayani ta bangaren na biyu zai yi.
Sashen doka da ya yi hani ga miyagun abubuwa ta gefe ɗaya yana ƙarfafa ayuka da halayye nagari. Misali, dokar Littafi Mai Tsarki da ta hana zina, tana buƙatar a yi nagarta da tsarki. Haka kuma, idan aka nuna ɓangaren doka da ta ƙarfafa nagarta, to, ana haramta ɗaya ɓangaren da ke da akasin ta na mugunta kenan. Misali, idan Allah ya umurce mu da zama masu nagarta game da tafiyar da dukiyar mu, ya nuna a fili kenan bai kamata mu zama masu almubazzaranci ba. Nagarin umurni ko doka ga aiki cikin kwazo, yana ɗauke da nuna hani ga ragwanci a kan aiki.
Yin hani ga miyagun ayuka kamar kisa na ainihi, ko kisa da ke iya yiwuwa, duk a cikinsa ya ƙunshi umurni nagari, wato, yin aiki domin tabbatar da kariya da ci-gaba na rai. Yin tsayayya da kisa yana nufin inganta rayuwa. Ko ma mene ne zubar da ciki ya ƙunsa, ba ya dai kawo inganci ga rayuwar jaririn da ba a haifa ba. Ko dayake wasu za su yi gardamar cewa zubar da ciki yana inganta rayuwar waɗanda ba su son ‘ya’ya, to, amma kuwa bai inganta ran abin da ke cikin ba, wato, wannan jariri mai girma da ba a haifa ba.
Littafi Mai Tsarki a kullum yana ba da ƙwaƙƙwaran goyon baya ga matuƙar muhimmanci na ran dukan mutane, yadda ba a iya kwatantawa. Ko talakawa ne, ko waɗanda ake zalunta, ko mata da mazan su suka mutu, ko naƙasassu-duk suna da matuƙar muhimmanci gaba da misali a cikin Littafi Mai Tsarki. Don haka, tabbas ne duk wata muhawara kan batun zubar da ciki, dole sai ta yi kokawa da wannan muhimmin jigo na cikin Littafi Mai Tsarki. Sa’adda hallaka rai ko kuma zubar da rai da kan iya zamowa mutum, ya kasance abu na haka kawai, ba wahala an aikata, to kuwa, duhu yana yaɗuwa kan shimfida na darajar rai, da kuma martabar mutum.
An tsakuro wannan bayani daga rubutun R.C. Sproul na Abortion: A Rational Look at an Emotional Issue.
An fara buga wannan tsararren rubutu ne a shafin ma’katar bishara ta Ligonier.


