Matsayin Addu’a

24/11/2025

Matsayin Addu’a

24/11/2025

Mene ne Manufar Allah a cikin Giciyen?

Ka’idar fansar da aka takaita ko kaffara mai iyaka (wanda ake kira kuma fansar na musamman) tana koyar cewa fansar da Almasihu ya yi an takaita ta (a cikin manufarta da iyakarta) ga wadanda Allah ya zaba tun fil azal; wato Yesu bai yi fansa domin zunuban dukkan mutane a duniya gaba daya ba. A ɗarikar mu, mukan yi zama na tattaunawa da matasa maza da suke son shiga aikin bishara, kuma a kullum wani yakan yi wannan tambaya “ko ka yarda da kaffara mai iyaka?” Sai ɗalibin ya amsa da cewa, “E, na ba da gaskiya cewa kaffarar Kristi wadatacciya ce ga kowa, kuma mai dacewa ga wasu, “ma’anar ita ce, darajar mutuwar Yesu a kan giciye ta kasance da girma matuƙa yadda take rufe dukanin zunubai na duk wani mutum da ya taɓa rayuwa a duniyar nan, amma ya kasance da amfani ne kaɗai ga duk waɗanda suka sa bangaskiyar su ga Kristi. Kodayake wannan maganar ba ta tunƙari ainihin tushen wannan jayayyar ba, wadda ta shafi mene ne maƙasudin Allah game da giciyen.

Akwai muhimman hanyoyi biyu da za a fahimci madawwamiyar nufin Allah. Hanya ta  ɗaya ita ce, tun fil’azal, Allah ya kasance da ƙauna ta ceton mutane masu matuƙar yawa daga wannan lalatacciyar duniya ta ɗan Adam, domin haka ya tsara shirin fansa wadda a ta haka ne zai aiko Ɗan Sa cikin duniya a matsayin mai ɗaukan zunubi na mutane da suka faɗi. Yesu zai je giciye, kuma ya mutu domin dukan waɗanda a wani lokaci suka sa bangaskiyar su a gare shi. Saboda haka wannan shiri ne da aka tanada-Allah ya tanada kaffara ga duk waɗanda suka yarda su mori wannan dama, ga duk waɗanda suka ba da gaskiya. Ma’ana, an yi tanadi na mutuwar Yesu domin kowa da kowa, amma tana iya yiwuwa wannan tanadi ba zai zama da wani tasiri ba, domin wataƙila kowane mutum a duniya zai ƙi karɓan aikin da Yesu ya yi, su zauna matattu cikin laifofin su da zunubansu. Don haka ta yiwu a katse aikin Allah, domin mai yiwuwa babu wani da ya amince ya mori wannan dama. Wannan shi ne ra’ayin da ke rinjaye cikin ikklisiya a yau- cewan a tanadin, Yesu ya mutu domin kowa. A tantancewa ta ƙarshe kuwa, idan aka sami ceto, to, zai dogara ne ga kowane mutum da kansa shi kaɗai.

Ra’ayi na Gyara, wato Reformed, kuma sun fahimci shirin Allah ta wata fuska daban. Suna cewa tun fil’azal, Allah ya yi shiri wanda ba wani tanadi bane. Shiri daya tak ba tare da wata shiri na biyu ba, kila idan shiri na farko bai yi nasara ba. A wannan shirin, Allah ya tsara cewa zai ceci wata lambar mutane daga wannan duniyar mutum da ta faɗi, mutane waɗanda Littafi Mai Tsarki ya kira zaɓaɓɓu. Kuma domin wannan shiri na zaɓaɓɓu ya sami yin nasara cikin tarihi, Ya aiko Ɗan Sa cikin duniya da manufa da kuma fasali ta musamman don kammala fansa domin zaɓaɓɓun. Wannan ya sami cikakkiyar kammaluwa, ba tare da wani ɗigo na jinin Yesu ya zama a banza ba. Duk wanda Uban ya zaɓa ga ceto, zai sami ceto ta hanyar kaffarar.

Ra’ayi na Mara-Gyara, wato waddanda ba Reformed bashi ne cewa Allah ba shi da riga-sani na ko wanene zai sami ceto. Domin wannan dalilin ne, a yau akwai malaman Tauhidi da ke cewa, “Allah Yana ceton mutane dayawa da zai iya.” Mutum nawa ne Allah zai iya ceto? Mutum nawa ne yake da ƙarfin ya ceto? Idan Shi Allah ne, Yana da ikon ceton dukan su. Mutum nawa ne yake da ikon cetowa? Ko Allah ba zai iya yin wani abu cikin rayuwar kowane mutum ba, kamar yadda ya yi a rayuwar Musa, rayuwar Ibrahim, ko rayuwar manzo Bulus ba, na yadda ya kawo su ga dangantaka ta ceto tare da shi? Tabbas yana da ikon yin hakan.

 Ba za mu iya musunta cewa Littafi Mai Tsarki ya yi magana game da Yesu ya mutu domin “duniyar.” Yahaya 3:16 shi ne misali na aya da ke kan-gaba da ta yi amfani da waɗannan kalamai. Amma akwai ra’ayi mai akasin wannan a cikin Sabon Alƙawari, haɗe da Bishara Ta Yahaya, da ya gaya mana cewa, Yesu ya ba da ran Sa ba don kowa ba, amma sai tumakin Sa. A nan cikin Bishara Ta Yahaya, Yesu ya yi maganar tumakin sa a matsayin waɗanda Uban Ya ba Shi.

A cikin Yahaya 6, mun ga Yesu ya ce, “Ba wanda ke zuwa wuri Na sai dai in Uba wanda ya aiko Ni ne ya jawo shi” (aya ta 14a), kuma kalmar da aka fassara “jawo” tana ainihin nufin “tilasta.” A wannan aya Yesu ya sake cewa, “Duk waɗanda Uba Ya ba Ni za su zo gare Ni” (aya 37a). Abin da yake nunawa shi ne, dukan wanda Uba ya shirya su zo ga Ɗan Sa za su zo, ban da ko wani dabam. Don haka, ceton ka/ki, daga farkon har ƙarshe, ya dogara ne ga tsari na ikon Allah, ya shirya ne, cikin alherin Sa, ya nuna maka jinƙai, ba don Ya ga wani abu a wurin ka da ya cancanci yin hakan ba, amma kawai don ƙauna ta Ɗan ne. Dalilin kaɗai da zan iya bayarwa a duniyar nan, na me ya sa na kasance Krista shi ne cewa, ni kyauta ne ta Uban zuwa ga Ɗan, ba don wani abu da na taɓa aikatawa, ko zan aikata ba.   

An tsakuro wannan rubutu ne daga sharhin da R.C. Sproul ya yi kan Littafin Yahaya.


An fara buga wannan tsararren rubutu ne a shafin ma’katar bishara ta Ligonier.

R.C. Sproul

R.C. Sproul

Dr. R. C. Sproul shi ne ya kafa Ministirin Ligonier, shi ne kuma mai bishara da koyarwa na farko a masujadar Saint Andrew’s da ke a Sanford, Fla., Shugaba na farko na Reformation Bible College, kuma Babban darekta na mujallar Tabletalk. Har yau, ana yaɗa shirin sa na Renewing The mind (sabonta tunani) a dubban tashoshin radiyo a kewayen duniya, haka kuma ana iya sauraro a yanar gizo. Ya wallafa litattafai fiye da dubu, sun haɗa da, The Holiness of God (TSarkin Allah), Chosen by God (zaɓin Allah), da kuma Everyone’s a Theologian (Kowa Dalibin Tauhidi ne). Ya zama sananne a kewayen duniya domin kalaman sa na kishin kare Littafi Mai Tsarki a matsayin babu kuskure a ciki, da kuma buƙatar mutanen Allah su tsaya daram bisa amincin su a kan Kalmar Sa (Allah).