Mene ne Furcin Zunubi?

26/05/2026

Mene ne Furcin Zunubi?

26/05/2026

Ko Allah Yana Kula Da Gaske?

Cikin tsananin damuwa da matuƙar fargaba, masu bi suna yawan tunani―ko da kuwa a cikin zukatan su ne kawai―cewa ko Allah ya damu da su. Idan kana da irin tunanin nan, ina da labari mai daɗi.

Tambayar da ake yawan yi

Da farko, ba ke/kai kaɗai ba ne. Cikin tsawon tarihi masu bi suna wannan tambayar. Annabi Habakuk ya dubi halin da mutanen Allah ke ciki― marasa adalci sun Tattake su, sun zaluntar su – sai ya yi kuka, y ace,

Ya Ubangiji, har yaushe zan yi kira, kai kuwa ba ka yarda ka ji ba?

(Habakuk. 1:2; dubi kuma 1:3, 13).

Mai-Zabura yana yawan roƙon Allah cewa Ya “taso” da Kansa, yana tambayar kulawar Allah sa’adda  bai sami amsa ga ɓacin ran sa ba (Zabura 35:23; 44:23). Duk da cewa sun sani Allah ba ya taɓa yin barci (Zabura 121:4), da kuma yadda tunanin yakan nuna kamar bai yi komai ba a lokacin tsananin su, ya sa suna tunani ko a gaskiya ya damu da su.

Wannan gwagwarmaya ba ta keɓu ga Tsohon Alƙawari kaɗai ba. A lokacin tsananin damuwa almajirai sun yi kuka ga Yesu, “Malam, ba ka damu ba za mu halaka?” (Markus 4:38). Ko ma a kan abin da bai taka kara ya karya ba , masu bi suna kokawa da wannan tambaya. Sa’adda Marta ta gaji da yawan aiki, ta tambayi Yesu ko bai damu ba cewa tana hidima ita kaɗai (Luka 10:40). Cikin ire-iren yanayi, a lokuta daban-daban, sa’adda ya zama kamar Allah bai yi wani abu game da tsananin da muke ciki ba, ko kuma ta yadda muke so a gaggauce ba (ko kuma da ya hana faruwar wannan matsalar tun farko), masu-bi cikin shekaru aru-aru suna yi tambaya game da kulawar Sa.

Amsa Mai Burgewa  

Na biyu, Allah ba ya barin ka, kai kaɗai haka nan, ka yi ta tunanin ko ya damu da kai, ko da ke. Ya bayyana ƙauna ko kulawar Sa gare ka/ki ta wata gagarumar hanya da ta wuce tunanin mutum: da ya aiko ƙaunataccen Ɗan Sa. Yahaya ya nuna mana wannan sosai sa’adda ya rubuta cewa: “Gama Allah Ya yi ƙaunar duniya,har Ya ba da Ɗan Sa haifaffe shi kaɗai” (Yahaya 3:16). Wannan yana nuna cewa Kristi na ainihin fahimci irin yanayin takaici nan, da tsanani, da tsoro da ke ƙunshe cikin rayuwa a duniyar da ta ɓace kuma cike da zunubi, dalilin haka yana iya tausaya maka ko maki (Ibraniyawa 4:15).

Gaba da haka ma, kulawar Allah na kasancewa ta ayyukan Ruhu Mai Tsarki. Sa’adda Yesu ya yi alƙawari na Ruhun, Ya bayyana Shi a matsayin “wani Mai-Taimako kuma” wanda ba zai taɓa barin mu ba (Yahaya 14:16). Ba kamar yadda yakan kasance da abokai mutane waɗanda kan iya gajiya, ko wani abu ya ɗauke masu hankali ba, Shi Ruhu Mai-Tsarki Yana tare da kai a kullum. Ba ya zuwa hutu, ko ya sulale ya gudu, kuma ba zai taɓa yashe ka/ki ba. Wannan bayyanannen aikin alƙawarin Allah ne na ainihi gare ka/ki: “Har abada ba zan bar ka ba. Har abada kuma ba zan yashe ka ba.” (Maimaitawar Shari’a 31:8; Ibraniyawa 13:5). Wannan Zahiri ne ko da kuwa muraɗin ka/ki ya gaya maka cewa kina ko kana kai kaɗai, ko kuwa an yashe ka, ko kana can waje nesa da kulawar Allah.

Wahala tana nuna kulawar Allah

A ƙarshe, yana da muhimmanci ku gane cewa kulawar Allah ba wai yana nufin za ka kauce wa tsanani da taƙaici bane. Maimakon haka, kulawar Sa na nufin za ka jure cikin yanayin har ka girma ka yi nasara bisa wannan yanayin. Hakan yana da wuyan fahimta ga tunanin mu. Amma Allah yana gaya mana cewa wahala, maimako ta hallaka mu, yana haifar da himma, da inganta hali, da kuma bege (Romawa 5:3-5).

Wani shan wahalan yana zuwa a matsayin horo cikin ƙaunar Allah, domin alheri gare mu (Ibraniyawa12:7-11), wannan na nufin cewa shan wahalar mu―ko da kuwa ta kasance horo ne―ba alama ne wai Allah ya yashe mu ba, amma alama ne na kulawar Sa.

Wani shan wahalan kuma yana ba mu damar tarayya cikin rayuwar Kristi. Bulus cikin ƙarfin hali ya bayyana cewa mu “magada ne tare da Kristi, in dai har muna shan wuya tare da Shi, za a kuwa ɗaukaka mu tare da Shi” (Romawa 8:17). Ko shi Kristi da Kansa ya koyi biyayya ta wurin wuyan da Ya sha (Ibranyawa 5:8). Idan har za mu zama kamar Shi, dole ne mu yi koyi ta irin hanyar. Wannan ya yi nesa da kasancewa nauyin kaya, wannan kyauta ce― dama ce ta yin tarayya cikin abubuwan da Mai-Ceto mu ya fuskanta.

Kammalawa.

Lokacin da aka jarabce ka ka yi shakka ko Allah yan kula, ka duba giciye. A nan ne aka nuna kaunar Allah cikakke. Ba zai― Hakika ba zai iya – barin mutanensa ba bayan ya biya irin wannan babban farashi. Kuma da bay a kula da mutanensa – da kai – tun farko, da bai biya irin wannan babban farashi ba. Wahalarka ba lallai  alama ba ne cewa Allah ya janye yardarsa; a maimako haka, tana iya zama shaida  ce ta aikin da yake ci gaba da yi a cikinka.

Ka yi karfi hali. A lokacin da shaka ya zo kuma bangaskiyar ka tana kasawa, Shi ba zai bar ka ba. Wata rana, idan ka waiwaya ka dubi waɗanna jarabobi bayan ka kai wurin salama, za ka gane cewa ba ƙarfin hannun ka da ke riƙe da giciyen ne ya ba ka nasara ba, amma ƙarfin hannayen Sa masu tabon kusoshi ne suka dauke ka, suka kiyaye ka, suka karfafa ka, ba tare da barin ka ko yashe ka ba.


An fara buga wannan labarin a shafin yanar gizon Ministirin Ligonier. [Blog ɗin Ministirin Ligonier]

Josh Squires

Josh Squires

Reverend Joshua A. Squires mataimakin fasto ne na sashen bayar da shawarwari a Presbyterian Church a garin Columbia, S. C.