Shin Mutum a asali nagari ne ko kuwa gaba daya mai zunubi ne?

25/06/2026

Magance Laifin Zubar da Ciki

02/07/2026

Shin Mutum a asali nagari ne ko kuwa gaba daya mai zunubi ne?

25/06/2026

Magance Laifin Zubar da Ciki

02/07/2026

Menene Fushin Allah?

Fushin Allah shi ne martanin Allah mai tsarki da adalci ga zunubi da kuma masu zunubi wadanda ba a rufe su da kafarr Allahnmu ba Ko da yake mutane da yawa ba sa son tunanin Allah a matsayin mai fushi, Littafi Mai Tsarki ya sha nanata magana a kan fushin Ubangiji da ake zartarwa a kan mugunta. Tsohon Alkawari da Sabon Alkawari duka sun  tabbatar sosai cewa Allah yana zartar da fushi a kan rashin adalci (duba K. Shari’a 9:8; 2 Sarakuna 23:26; Zab. 21:9; 90:11; Isha. 13:9; Mik. 5:15; Zaf. 1:18; Yohanna 3:36; Rom. 1:18; Afis. 5:6; Ruy. 16:1).

Fushin Allah da Halayen Allah

Allah yana zartar da fushinsa a kan rashin adalci domin halinsa. Nassi ya shaida cewa Allah mai adalci ne kuma mai gaskiya (K. Shari’a 32:4; Dan. 9:14; Rom. 1:17; Ruy. 15:3). Ba zai zama mai adalci da gaskiya ba idan bai hukunta mugunta da masu aikata mugunta ba, saboda haka zubar da fushinsa a kan zunubi ya yi daidai sarai da halinsa na adalci. Dole ne masu zunubi su biya sakamakon laifofinsu, kuma Allah ba zai kuɓutar da mai laifi ba tare da ya zartar da fushinsa na adalci ba, don kada ya kasance marar adalci (Fit. 34:6–9). Allah ƙauna ne (1 Yohanna 4:7–8), kuma ɗaya daga cikin abubuwan da yake ƙauna shi ne adalci (Zab. 33:5). Tun da Allah cikakke ne, ƙaunarsa ga adalci dole ta zama cikakkiya; saboda haka, dole ne ya ƙi “hanyar mugaye” (K. Magana 15:9; duba kuma K. Shari’a 32:4).

Ubangiji ba zai iya nuna fushi ba sai dai idan akwai zunubi, kuma ba za a iya samun zunubi ba sai dai idan akwai halittu da suke yin zunubi. Don haka, ba za a iya bayyana fushin Allah ba sai da halitta da kuma faɗuwarta cikin zunubi. Saboda wannan dalili, masana tauhidi da yawa sun rarraba fushi a matsayin halayen Allah na dangantaka ba halayen Allah tabbatattu. Halin Allah tabbatacce shi ne halin Allah wanda zai kasance a bayyane ko a zartar da shi ko da Ubangiji bai taɓa halittar komai ba. Halayen Allah tabbatattu sun haɗa da abubuwa kamar dawama da sanin komai da kowa. Ko Allah ya halicci sararin samaniya ko bai halitta ba, shi madawwami ne kuma mai sanin komai.

Halayen Allah na dangantaka ba sa bayyana sai dai idan akwai wani abu a wajen Allah da zai yi alaƙa da shi. Kamar yadda aka lura a sama, fushi halin Allah ne na dangantaka domin idan babu masu zunubi, ba za a bayyana fushin Allah ba. Duk da haka, ba wai fushi (ko wani halin Allah na dangantaka) wani abu ne da Allah yake samu ta dalilin halitta ba. Allah yana mayar da martani ga zunubi da fushi ta dabi’ar halinsa na asali—nagari kuma mai adalci. Ana bayyana fushin Allah ne saboda halitta ta canja, ta zama mai zunubi, ba wai domin Allah kansa ya canja ba. Masu zunubi suna fuskantar fushi lokacin da suka zo gaban Allah wanda asalin yanayinsa mai adalci ne, ba wai domin Ubangiji ya ɗauki sabon hali a lokacin faɗuwar ɗan adam ba. Domin kuwa, Allah ba ya canjawa (Mal. 3:6).

Fuskantar Fushin Allah

Nassi ya bayyana sarai cewa fushin Allah mai ban tsoro ne. Littafi Mai Tsarki yakan yi magana akai-akai game da zafin fushin Allah mai ƙonawa (Fit. 32:11; Mak. 4:11), har ma ya bayyana wurin fushin Allah na har abada a kan masu zunubi waɗanda ba su taɓa juyowa daga zunubinsu zuwa ga Kristi ba a matsayin “tafkin wuta” (W.Yah. 20:10). Da yake ɗauko magana daga Ishaya 66:24, Yesu ya ce a cikin jahannama, “tsutsarsu ba ta mutuwa” (Markus 9:42–49). Da wannan hoton, Mai Cetonmu ya kwatanta shari’ar Allah a matsayin cinyewa mai zunubi da ba ya ƙarewa kuma mai halakarwa. Annabawa da Manzanni suna magana game da babban halaka da kuncin “ranar Ubangiji,” wadda za ta iya nufin zubar da shari’ar Allah a takamaiman lokuta a tarihi da kuma shari’arsa ta ƙarshe a ƙarshen zamani (Isha. 13:6; Ezek. 30:3; Joel 1:15; 2 Bitrus 3:10).

Saboda kwatancin da aka ambata a baya, mutane da yawa wataƙila suna tunanin fushin Allah ya ƙunshi bayyanuwar shari’a mai ban mamaki kuma mai wuta kawai. Duk da haka, yana da mahimmanci cewa irin waɗannan bayyanuwar shari’ar a haƙiƙa su ne cikar fushin da aka fara zubarwa tun da wuri. Nassosi irin su Romawa 1:18-32 suna nuna cewa Allah sau da yawa ba ya sauke fushinsa lokaci ɗaya, maimakon haka yana yin hakan ne a hankali a tsawon lokaci. Bulus ya gaya mana cewa fushinsa ya ƙunshi mika mutane ga zunubinsu da barinsu su ƙara nitsewa a ciki. Sau da yawa Allah yana barin masu zunubi marasa tuba su de fada cikin zunubin da suke so tun kafin ya murkushe shi a cikin shari’a mai wuta. Allah a cikin fushinsa zai mika marasa tuba ga zunubinsu.

Bege ga Waɗanda Suke Ƙarƙashin Fushin Allah

Akwai ranar fushi ta ƙarshe da take zuwa kan masu zunubi. Abin godiya ne cewa Allah mai jin ƙai ne, kuma ya samar da Yesu Kristi don ya cece mu daga fushi mai zuwa (1 Tas. 1:10). Yesu Kristi shi ne Allah Ɗa, wanda ya zama mutum domin ya ɗauki hukuncin da Allah mai adalci ya tanada domin zunubi. A cikin Yesu Kristi, Allah ya zubar da fushinsa, yana ɗaukar fushin a kan kansa. Ta haka ya nuna kansa mai adalci, domin an hukunta zunubi a cikin Kristi, kuma yana cike da jin ƙai, domin kafarar Kristi tana nufin cewa yanzu zai iya zama mai sulhu, ko mai nuna alheri, ga masu zunubi waɗanda suka juyo daga zunubinsu kuma suka dogara ga Yesu (Rom. 3:21–31). Ubangiji yana jin daɗin nuna madawwamiyar ƙauna da jin ƙai (Mik. 7:18), kuma dukan waɗanda suka dogara ga Yesu kaɗai domin ceto za a cece su sarai daga fushin Allah na har abada (Ibran. 7:25).


An wallafa wannan talifi ne asali a dandalin Ministirin Ligonier Blog. [Blog ɗin Ministirin Ligonier]

Robert Rothwell

Robert Rothwell

Rev. Robert Rothwell babban marubuci ne na Ligonier Ministries, mataimakin edita na mujallar Tabletalk, kuma malami mai ziyara dake zaune a harabar makarantar a Reformation Bible College da ke Sanford, Fl.