
John Calvin Akan Wajabcin Gyara Ikilisiya
10/12/2025
Me Ya Sa Kuke Aiki?
15/12/2025Mene ne Ma’anar Bishara?
Kristoci dayawa, da ikklisiyoyi dayawa, da ƙungiyoyi dayawa, a kullum suna amfani da kalmar bishara domin bayyana abubuwan da suka yi aminci da su. An taɓa samun saɓani na irin wannanTauhidin, ana kuma samu har yanzu game da ma’anar bishara da kuma ko wa ke wa’azin ta cikin gaskiya da aminci.Mene ne wannan sananniyar kalma bishara ke nufi? Hanya mafi dacewa domin amsa wannan tambaya ita ce mu koma ga Littafi Mai Tsarki.
A Sabon Alƙawari na Girkanci, Kalmar euangelion(“bishara”) ta bayyanu kusan sau saba’in.Tun da yake, ta wani ɓangare za mu zaci cewa kalmar za ta fito fiye da haka, ganin cewa gaba ɗayan Sabon Alƙawari yana a kan bisharar ne. Wani abin mamaki kuma shi ne cewa, yadda marubuta Sabon Alƙawarin sun yi amfani da ita ta hanyoyi da suka matuƙar bambanta. Bulus ya yi amfani da kalmar sau kusan ninki uku fiye da duk sauran marubutan idan aka haɗa duk nasu. Ana samun sauran wuraren da aka yi amfani da kalmar a cikin Matiyu da Markus, da kuma ɗan kaɗan, in ma akwai kenan, a cikin Luka, da Bitrus, da kuma Yakub.
A sauƙaƙe, Ita kalmar bishara tana nufin “labari mai daɗi.” wannan kalma ba keɓaɓɓiya ce ga saƙon Krista kaɗai ba, amma an yi amfani da ita a duniyar arna wajen bayyana sanarwa mai daɗi. A cikin Sabon Alƙawari, tana nufin labari mai daɗi na Yesu Mai-ceto. Yawancin lokaci, ana amfani da kalmar da tunanin cewa makaranci ya san abin da kalmar take nufi.
A sa’adda muka yi kyakkyawan lura ga hanyoyin da aka yi amfani da kalmar bishara cikin Sabon Alƙawari, wasu ƙwararan batutuwa suna bayyanuwa matuƙa. Da farko, muna yawan ganin furuci na “bisharar Allah.” Wannan furuci yana nanata asalin tushen bishara a matsayin kyauta ce daga Allah. Asalin bishara daga Allah take, ba daga mutum ba. Na biyu, An ƙayyade halayyar bishara ta hanyoyi daban-daban: ita bisharar, gaskiya ce (Galatiyawa 2:5,14; Kolosiyawa 1:5), alheri ce (Ayyukan Manzanni 20:24), daukaka ce (2 Korintiyawa 4:4; 1 Timoti 1:11). Na uku, muna ganin martani iri biyu ga bisharar. Muhimmin martani shi ne gaskantawa (Ayukan Manzanni 15: 7; Afisawa 1:13). Sannan kuma biyayya ma martani ne(1 Bitrus 4:7; Romawa 1:5; 10:16; 16:26; 2 Tasalonikawa1:8).
(Yadda Bulus ya yi amfani da batun biyayya na gaskantawa a cikin Romawa, yana kusan kawo saɓani ga tunanin mutum, a lokacin da yake mai da martani ga waɗanda suke zargin sa, wai ya ce Krista ba su da hakkin aikata ayukan nagarta in har sun riga sun ba da gaskiya, hakan kuwa ya saɓa wa shari’a). Na huɗu, mun ga sakamakon bishara da yawa. Lallai, bisharar tana kawo ceto (Romawa 1:16; Afisawa 1:13). Tana kuma kawo mulkin (Matiyu 4:23; 9:35; 24: 14). tana haifar da bege a cikin mutanen Allah (Kolosiyawa 1:23). Haka kuma bisharar tana zuga mutum zuwa ga tsarkakewa (Markus 8:35; 10:29; 2 Korintiyawa 9:13; Afisawa 6:15; Filibiyawa 1:27).
Duk waɗannan hanyoyi da aka yi amfani da kalmar bishara na yin nuni ga abin da ta ƙunsa, amma akwai nassoshi a cikin Sabon Alƙawari da musamman ke keɓanta abin da ta ƙunsa. A lokacin nazarin waɗannan nassoshi, mun gane cewa wani lokaci kalmar bishara bisa ga faffaɗar ma’ana tana nufin dukanin ɓangarorin bishara da sabon rai wanda Yesu yake ba mutanen Sa, wani lokaci kuma akan ƙayyade ma’anar zuwa ga nuna abin da Yesu yake yi mana daga waje da mu. Ta wata hanyar kuma, wani lokaci kalmar bishara tana nuni idan aka faɗaɗa bayanin, ga aikin Yesu na baratarwa da tsarkakewa domin, da kuma cikin Mutanen Sa, wani lokaci kuma in aka ƙayyade, tana nuni ga aikin Yesu na baratarwa. Wata hanyar nuna wannan bambanci ita ce cewan, wani lokaci kalmar bisharar in an faɗaɗa bayanin ta, tana nufin dukan cikawar Alƙawura a Sabon Alƙawari, wato, alƙawuran nan da aka yi a cikin Tsohon Alƙawari, sannan wani lokaci kuma bishara a ƙayyde tana nufin yadda Yesu ya aiwatar da doka ta hanya daban da yadda mu muke yi.
Misali faffaɗan bayani na kalmar bishara na bayyanuwa a Markus 1:1, “Farkon bishara ta Yesu Kristi, Ɗan Allah.” Wannan amfani da kalmar bishara kamar tana nufin dukan abin da Markus ya gaya mana game da koyaswa da ayukan Yesu. Haka ma mun ga wani faffaɗan ma’ana a Wahayin Yahaya 14:6-7.
Na ga wani mala’ika kuma yana firiya a tsakiyar sararin Sama, yana da bishara ta har abada, wadda zai yi shelar ta ga mazauna duniya, ga kowane iri, da ƙabila, da harshe, da al’umma. Da babbar murya kuwa sai ya ce, “Ku ji tsoron Allah, ku ba shi daraja, gama sa’ar hukuncin sa ta zo: ku yi sujada ga wanda ya yi Sama da duniya, da teku da maɓulɓulan ruwaye.”
A nan bisharar kira ce ga tuba da yi wa Allah sujada.
Yawanci kuma, akan ba da ƙayyadadden ma’ana na kalmar bishara, kuma a kayyade abin da take dauke da shi, za mu iya ganin haka a 1 Korintiyawa 15:1-4
Yanzu ‘yan’uwa, ina tuna maku da bishara wadda na yi maku wa’azin ta, wadda kuka karɓa, wadda kuke bi, wadda kuma ake ceton ku da ita, muddin kun riƙe maganar da na sanar da ku da kyau, in ba sama-sama ne kuka gaskanta ba. Gama jawabi mafi muhimmanci da na sanar da ku, wanda ni na karɓa, cewa, Almasihu ya mutu domin zunuban mu, kamar yadda litattafai suka faɗa, cewa an binne shi, an ta da shi a rana ta uku, kamar yadda litattafai suka faɗa.
A nan, bishara na magana a kan ceto wadda mutuwa da tashin Yesu ya bayar.
A wani sashe kuma, Bulus ya rubuta game da “Maɗaukakiyar bishara, ta Allahn mu Mai Albarka, wadda aka danƙa mani amanar ta,” kuma ya nuna takamaimai mene ne wannan bisharar:
Maganar nan amintacciya ce, ta kuma cancanci a karɓe ta dungum cewa, Almasihu ya shigo duniya ne domin ceton masu zunubi,” ni ne kuwa babban su. Duk da haka an yi mani jinƙai, musamman don ta wuri na, ni da ke babba, Yesu Kristi zai bayyana cikakken haƙurin Sa duka, domin in zama gurbi ga waɗanda za su ba da gaskiya gare Shi nan gaba su sami rai madauwami (1 Timoti1:11, 15-16).
A nan, bishara ita ce aikin Kristi na ceto domin masu zunubi.
Bulus ya sake rubuta makamancin haka a Timoti ta 2:
Saboda haka, kada ka ji kunyar ba da shaidar Ubangijin Mu, da kuma tawa, ni da nake ɗan sarka saboda Shi, sai dai mu jure wa shan wuya tare, saboda bishara, bisa ga ikon Allah, wanda ya cece mu, ya kuma kira mu da kira mai tsarki, ba don wani aikin lada da muka yi ba, sai dai domin nufin Sa, da alherin Sa, da aka yi mana baiwa tun fil’azal, a cikin Almasihu Yesu, wadda yanzu aka bayyana ta bayyanar Mai-ceton mu Almasihu Yesu, wanda ya shafe mutuwa, ya kuma bayyana rai da rashin mutuwa, ta wurin bishara . . . Tuna Yesu Almasihu fa, Shi da aka tashe shi daga matattu, na zuriyar Dauda bisa ga bishara ta. (2 Timoti 1:8-10; 2:8)
Yin amfani da kalmar bishara a ƙayyade abu ne mai sauƙi a cikin rubuce-rubuce na Masu-Gyara na ƙarni na goma sha shida. Za mu iya ganin haka a rubutun John Calvin, da ya ce:
Kalmar gaskantawa ta musanya (ta maye gurbin kalmar da take da dangantaka da ita) kalmar alkawari, wato na Bisharar ita kanta, tun da tana da dangantaka da gaskantawa. Ya kamata a fahimci bambanci tsakanin shari’a da bishara, kuma daga fahimtar wannan bambanci mun fahimci cewa, kamar dai yadda shari’a ke buƙatar ayuka, ita bishara tana buƙatar mutane su zo cikin gaskantawa domin su karɓi alherin Allah.
Zacharias Ursinus shi ma ya bayyana a fili. Daga farko-farkon sharhin sa game da Catechism na Heidelberg, Ursinus ya raba duk koyaswar zuwa shari’a da bishara:
Koyaswar ikklisiya ta ƙunshi ɓangarori biyu: Shari’ar, da kuma Bisharar; wanda a cikin ta mun sami fahimtar ta sosai na maƙasudin tsarkakakkun nassoshi. Ana kiran shari’ar dokoki goma, sannan bishara kuma ita ce koyaswa dangane da Kristi mai shiga tsakanin mu da Allah, da kyauta ta gafarar zunubai, ta hanyar gaskantawa.
Irin wannan nazari a kan bishara ya zama abu mai sauƙi cikin Tauhidin Masu-Gyara, kamar yadda yake a wannan dogon bayani da aka tsakuro daga rubutun shahararren masanin tauhidi na garin Dutch, mai suna Herman Bavinck:
Amma maganar Allah, wanda kasancewar ta daga ɓangaren shari’a ne da kuma bishara, ya kasance wahayi da ke bayyana nufin Allah, shela ne na alƙawari na shari’a, da kuma alƙawari na alheri…. ko dayake daga faffaɗan ma’ana na waɗannan kalmomi na shari’a, da kuma bishara, za mu iya amfani da su wajen yin nuni ga lokacin bayar da sabo da tsohon alƙawari na alheri, dangane da ainihin muhimmancin kowannen su, tabbas suna bayyana wahayi biyu daban-daban daga Allah (a nan Bavinck ya yi amfani da misalai na nassoshi dayawa da za su tabbatar da wannan) . . . A waɗannan nasssoshi an kamanta bambanci da ke tsakanin shari’a da bishara a matsayin ‘buƙata da kyauta,’ da kuma ‘umurni da alƙawari,’ ko kuma kamar ‘zunubi da alheri,’ ko ciwo da warkaswa, ko kuwa ma kamar ‘rai da mutuwa’ . . . Sharia’a ta samu ne daga tsarkin Allah, bishara kuma daga alherin Allah; ana sane da shari’a tun a farkon halitta, bishara kuma daga wahayi na musamman kaɗai, shari’a ta buƙaci cikakkiyar tsarki, amma alheri tana bayar da ita; shari’a tana jagorantar mutane ga madauwamiyar rai ta hanyar ayuka, amma bishara na haifar da kyawawan ayuka ta wurin arzikin da ke a madauwaminyar rai da aka bayar cikin gaskantawa. Yanzu shari’a tana yanke hukunci kan mutane, bishara kuma tana wanke su daga tuhuma; shari’a tana nuna kanta ga dukan mutane, bishara kuma ga waɗanda suke rayuwar sauraron ta kaɗai.
Wannan gabatarwa ta bishara ta kasance, a bayyane da kuma sauƙin fahimta, tana na musamman, da bisa tsarin Littafi Mai Tsarki, kuma mai daraja.
Ikklisiya tana bukatar ta yi wa’azin bishara a ma’anarta mai fadi da kuma ma’anarta mai tataituwa. Kalmar Girkanci ta bishara ita ta ba duniyar harshen Turanci kalmar nan Evangelism. Evangelism na gaskiya, kamar yadda Babban Umurnin da Yesu ya bayar a Matiyu 28:18-20, ya ƙunshi almajirantarwa: da farko, a ƙayadadden ma’ana shi ne, a kira maza da mata su gaskanta da Yesu, sannan na biyu, a faffaɗar ma’ana kuma, a koyar da su, su kiyaye dukan abubuwa da Yesu ya koya wa mutanen Sa. Saboda bishara, sai mu ƙarfafa evangelism na gaskiya.
An fara buga wannan tsararren rubutu ne a shafin ma’katar bishara ta Ligonier.


