
Mene ne Ma’anar Bishara?
12/12/2025
Ta Yaya Martin Luther Ya Mutu?
17/12/2025Me Ya Sa Kuke Aiki?
Me ya sa muke aiki? Na taɓa jin wata amsa mai sa damuwa, wadda aka bayar kamar haka; “Mukan sami aiki domin mu saya wa ‘ya’yan mu takalma, domin su je makaranta, domin su sami aiki wata rana, saboda su saya wa ‘ya’yan su takalma, domin su ma su….” Wato kenan, aiki ya zama ba ma’ana. A gaskiya ma, ta wannan fuskar, rayuwa ita kanta ta zama banza -ana ta zagaye ne a wuri ɗaya.
Haka kuma na taɓa jin cewa, muna aiki ne domin mu taimaka wa ministiris ɗin da suke ainihin aiki- aiki na mulkin. Ku fahimce ni fa, ba wai ina adawa da yin bayaswa ga ministiris bane. A gaskiya ina jin za a iya samun ƙwararan wurare a Littafi Mai Tsarki da suka nuna wajibi ne mu yi hakan. Sai dai ina tunani ko waɗannan zance da ake yi sun ƙunshi ainihin kyakkyawan ma’anar aiki.
Ina sake tambaya, me ya sa kuke aiki? Na sami farkon amsar a cikin Zabura ta 104. Zabura ta 104 na tunani ne game da halitta, kuma watakila ma zurfin tunani ne game da ambaliyar da ta faru a Farawa ta 6-8. Mawakin ya bayyana halittar duniya da dukan halittu cikin salo na waka, ba wai halittar Allah kadai ba, har ma da yadda Allah ke ci gaba da kula da halittunsa da dukan abin da Ya halitta (aya 1 -13).
A sura ta 14, mun karanta cewa Allah ya yi tanadi wa dabbobi da kuma wa mutane. Amma kuwa mun karanta cewa, mutane suna da rawar da za su taka. Za su nome duk tsiron da Allah ya halitta. Abin da ke faruwa a nan shi ne, aikata abin da kasancewa cikin-kamannin ke kunshe da shi. A matsayin waɗanda aka halitta cikin kamannin Allah, ya kamata mu yi iko a kan, mu kuma mallaki duniyar. Ya kamata mu faɗaɗa wannan ainihin lambun nan da Allah ya ba mu. A nan mun ga aiwatar da umurni na tsarin rayuwa na ƙwarai da ke a Farawa 1:26-28.
Mun sake ganin wannan a ayoyi ta 21-23 na Zabura 104. Kamar yadda zakuna suke fita farautar abincin su -suna aiwatar da haka ne bisa zahirin tsarin halittar su -haka nan ma mutum yakan tafi “ya fita ya je aikin sa, ya kuma yi aiki matuƙa har yamma” (aya 23). Akwai daidaituwa a nan wadda bai kamata ta ɓace wa tunanin mu ba. Dukan halittun Allah, babba da ƙarami, sun bayyana a matsayi na aiki cikin daidaituwa da ainihin, zahirin tsarin da Allah ya yi su. An halicci zakuna su yi “aiki” kamar zakuna. An halice mu mu yi aiki kamar wadanda ke dauke da kamanin Allah. Ainihi ma mai Zabura ya bi dalla-dalla, ba kawai daga hallitta zuwa halitta kaɗai ba, amma har daga halitta zuwa Allah, Mahaliccin. A ayar da ta biyo baya, wato aya 24, mai Zabura ya furta, “Ya Ubangiji, ka halicci abubuwa masu yawa! Da hikima Ka yi su duka; duniya cike take da taliƙan Ka.”
Mai Zabura yana so mu iya dangantawa tsakanin aikin mu, da batutuwa masu muhimmancin ma’ana. A sa’adda muke aiki, muna juyayi kan aikin Allah, Mahaliccin. Cikin aikin mu na yin iko da mallaka, cikin aikin mu na nomewa, muna ganin wani abu kuma. Aikin mu yana ba da shaida, da kuma yin nuni ga Shi wanda cikin Kamannin Sa ne aka halicce mu. Aikin mu shaida ne, manuni ne, ga Allah Mahalicci. C.S Lewis ya taɓa cewa, babu wani mutum da za mu haɗu da shi, da za a ce ba shi da amfanin sa. Ko kuma mu sake yadda muka faɗi maganar: Babu aiki da muke yi da ya kasance na haka kawai, aiki ba abin haka kawai bane, ko na wasa, ko marar kan gaba, ko marar kan gado, ko kuma marar ma’ana ba. Za mu fi fahimtar aikin mu a matsayin abin da ke ambaliya da ma’ana da matuƙar muhimmanci.
Amma, dakata, har ma ya wuce haka.
A ayoyi 25-26, mun karanta cewa:
Ga tekun babbar kuma mai faɗi,
Inda taliƙai da ba su ƙidayuwa suke zaune,
Halittu masu rai, manya da ƙanana,
Can jirage suke tafiya
Can Lebiyatan ya ke, wanda Ka halitta domin ya yi wasa a ciki.
A fili ya nuna cewa, tekun da halittun cikin tekun suna yin shaida ga girma, da ɗaukaka, da kuma kyaun Allah. Amma lura sosai da aya 26. Mai Zabura ya kawo abubuwa biyu amma sun kasance cikin akasi da juna: Jaragen ruwa da kuma Lebiyatan. Litattafan nan da ke a tsarin waƙa, kamar Zabura da Ayuba, har ma da wasu a cikin litattafan annabawa, sun ambaci wannan halitta, Lebiyatan. An yi zace-zace masu yawa game da ko wane irin halitta ne wannan Lebiyatan ɗin. Ko wani babban kifin ruwa ne? Ko dabba ne da ya ninka girman giwa? Ko dai wani dodon ruwa mai matuƙar girma? Abun da muka sani na tabbas shi ne cewa, wannan Lebiyatan ɗin halitta ne mai jan hankali. Za mu iya amfani da kalmar matuƙar-ban-mamaki, ko da yake ana yawan amfani da kalmar yadda har ya rage ƙarfin ma’anar ta, amma lallai Lebiyatan hallitta ne mai matuƙar-ban-mamaki.
Haka kuma Lebiyatan yana son wasa. Wannan ya bayyanu a fili. Jonathan Edwards, cikin rubutun sa na Flying Spider (gizo mai firiya), ya nuna cewa sa’adda wannan spider ɗin yake firiya za a ga murmushi a fuskar sa.Wannan ya sa Edwards ya kai ga tunanin cewa, Allah ya yi tanadi na “jin daɗi da nishaɗi ga kowane irin halitta, har ma da ƙwari.” Har da Lebiyatan. Wannan gabjejen dabba mai matuƙar-ban-mamaki yana wasa. Sannan kuma ga wannan dabba da ke a aya 26. Wannan dabba halittar-mutum ce: Can ga jirage tafe.” Yanzu sai mu yi tunanin sosai kan wannan. Halittar Allah da halittar mu suna haɗe kafaɗa da kafaɗa, dab kusa da juna a jere. Mai Zabura ya yi mamakin Lebiyatan, haka kuma mai Zabura ya yi mamakin jiragen. Yi tunanin wannan, mai yiwuwa ke ma ko kai da kanka ma ka faɗi haka: “Dubi, ka ga jiragen can suna tafiya. “Abin matuƙar mamaki.”
Me ake amfani da su wajen ƙera jirgin ruwa? Lissafi, da wani ɓangaren kimiya, da aikin kafinta cikin gwaninta, da ƙwarewa, wannan ƙwarewa ta samu ne daga tarin hikima na tsararraki da dama, ta hanyar gwaje-gwaje, da aiki cikin naciya- wannan duk domin ƙoƙarin ƙera jirgin ruwan ne. Mene ne tafiyar jirgin ruwa a kan ruwa ke kunsa? Hikimar jujjuya jirgin, da ƙwarewa, amfani da jijiyoyin jiki, ƙarfin ƙashin baya, hannuwa masu ƙarfi, juriya, da naciya, tarin hikimomi na tsawon tsararraki dayawa -duk wannan na ƙunshe cikin iya tuƙa jirgin ruwa.
Mai Zaburan mu ya yi matuƙar mamaki sa’adda ya ga jirgin ruwa na tafiya bisa faɗin teku. Mai Zaburan mu yana matuƙar mamaki da ya ga Lebiyatan na wasa yana kekkewayawa cikin faƙin teku. Waɗannan yanayi ne da ke da matuƙar ban mamaki ƙwarai.
Sa’adda muka ci-gaba da karanta wannan Zabura, za mu ga cewa akwai abin da ya wuce gaban babban hallitar Allah da gabjejen halittar mutum suna ƙetare teku, da yin wasa da igiyoyin ruwa. Aya 27 ta bayyana mana cewa: “Duka waɗannan” ma’ana dukan halittar Allah, “A gare Ka suke dogara, don Ka ba su abinci sa’adda suke buƙata . . .Kakan buɗe hannun ka, sukan ƙoshi da alheri.” Mu kan sami nishaɗi, mukan sami cika kuma muna samun ma’ana a cikin aikin mu. Muna amincewa da irin baiwa da Allah ya ba mu, da albarku na abubuwa daban-daban da Allah ya ba mu, sa’annan mu je mu yi aiki. Sannan mu sami gamsuwa. Ruwan inabi yana faranta mana zukata (aya 15). Halittar mu tana ba mu matuƙar mamaki,
Duka waɗannan sakamako ne na aikin mu. Amma a cikin su duka babu wanda yake babba mai kammala dukan abubuwa, ko kuma cikakken sakamako na aikin mu. Cikakken kammalawar aikin mu yana nan a aya ta 31: “Bari darajar Ubangiji ta dauwama har abada; bari Ubangiji Ya yi murna bisa ayukan Sa.” Aikin mu na da ma’ana. Aikin mu na yin nuni ga Shi Wanda cikin kamannin Sa ne aka halicce mu. A sa’adda muke aiki, muna kawo ɗaukaka ga Allah. A sa’adda muke aiki, Allah yana farin ciki da mu. Yanzu mun ci karo da amsar mu ga tambayar mene ne ya sa muke aiki.
Ko ka lura da abin da ba a ambata ba a Zabura 104? Babu ko nuni guda ɗaya da aka yi game da haikali, ko mawaƙan cikin haikali, ko firist da irin hidimomin su. An yi nuni ga noma. An yi nuni ga lura da shuke-shuke, an yi nuni ga aiki da hannuwan mutum. An yi nuni ga aiki.
An yi nuni ga ƙera jiragen ruwa.
“Ga jiragen can suna tafiya.” Ɗaukaka ga Ubangiji.
An fara buga wannan tsararren rubutu ne a shafin ma’katar bishara ta Ligonier.


