
Kafofin Da Aka Samo Asalin Tsarin Tauhidi
08/12/2025
Mene ne Ma’anar Bishara?
12/12/2025John Calvin Akan Wajabcin Gyara Ikilisiya
Fiye da shekaru 450 da suka wuce, kira ya zo ga John Calvin na ya rubuta game da halayyar ikklisiya da kuma buƙatar gyara a cikin ta. Yanayin ya bambanta sosai daga sauran wasu yanayi da suka ƙarfafa wadansu rubuce-rubucen Calvin, kuma sun taimaka mana wajen fahimtar bangarori na kariya da yake da ita ga Gyarawan. Babban sarkin Charles V ya yi kira ga majalisar masu fada a ji na Daular Roma Mai Tsarki don su hadu a birnin Speyer a shekara ta 1544. Martin Bucer, babban mai kawo sauyi na Strassburg, ya roƙi Calvin ya rubuta furci na koyarwar gyara da wajibcin yin gyara. Sakamakon ya kasance mai ban mamaki. Theodore Beza, abokin Calvin, kuma magajinsa a Geneva, wanda ake kira “Wajibcin Gyara Ikilisiya” a matsayin aiki babba mafi matukar tasiri a lokacin sa.
Calvin ya tsara aikin zuwa manyan sassa uku. Sashe na farko ya mai da hankali ne kan muguntar da ke cikin ikilisiyar, wanda ke buƙatar a yi gyara. Na biyu ya ba da bayanin dalla-dalla kan ainihin maganin wadancan mugunta, da masu gyara suka dauka. Na uku ya nuna abin da ya sa ba za a iya jinkirta gyaran ba, sai dai yadda lamarin ya bukaci “gyara nan take.”
A kowanne cikin waɗannan sassa uku, Calvin ya mai da hankali kan batutuwa huɗu, waɗanda ya kira ruhu da kuma jikin ikklisiya. Ruhin ikkilisiya shi ne bauta, da ceto. Jiki shi ne wadannan tsarkakan al’adun ibada ikklisiya da shugabancin ikklisiya. Ga Calvin, babban dalilin gyara yana da tushe ne cikin waɗannan batutuwa. Muguntar, maganin, da kuma bukatar a gaggauta yin sa, duk sun danganci bauta, ceto, tsarkakan al’adun ibada da shugabancin ikklisiya.
Ga Calvin, babban dalilin gyara yana da tushen cikin waɗannan batutuwa. Muhimmancin waɗannan batutuwa ga Calvin, shi ne, idan muka tuna cewa ba yana mayar da martani ga kalubale a waɗannan bangarori huɗu bane, amma shi da kansa ne ya zaɓe su da kansa a matsayin manya kuma muhimman ɓangare na Gyaran. Ibada mai dacewa, ita ce abu na farko da Calvin ya damu da shi.
Ibada
Calvin ya nanata mahimmancin ibada domin ‘yan Adam suna saurin yin ibada bisa ga irin nasu hikimar maimakon na Allah. Ya nace cewa dole ne a daidaita ibada da Kalmar Allah kaɗai: “Na san yadda yake da wuya a shawo kan duniya ga cewa, Allah bai yarda da duk wani nau’in ibada wanda ba Maganar Sa ce ta bayyana ba. Saɓanin ra’ayin da ya manne masu, ya sami zama, kamar dai har cikin ƙashin su yake, shi ne, cewa duk abin da suke aikatawa yana da hukunci mai gamsarwa na kansa, idan har ya iya nuna wasu irin himma ga ɗaukakar Allah. Amma da yake ba wai kaɗai Allah yana ganin irin wannan a matsayin ibada marar amfani ba, amma har ma a fili ya nuna ƙyama. Duk wata hidimar da za mu yi cikin himmar mu ta yi masa ibada, idan har hidimar tana saɓani da umarnin Sa, to wace riba za mu samu cikin aikata abin da ya zama akasin nufin Sa? Maganar Allah na bayyanawa a sarari, kuma cikin sauƙin fahimta cewa, ‘biyayya ta fi miƙa hadaya.’ “Wannan sakankancewa tana ɗaya daga cikin dalilan da suka kawo buƙatar gyara:”. . . tun da. . . Allah, cikin nassoshi dayawa ya hana duk wata irin sabuwar ibada wadda Maganar Sa bata amince da ita ba. Tun da ya bayyana cewa, duk wani zato da ke ƙirƙiro irin wannan ibada, ya kasance aikata matuƙar babban laifi ne a gare Shi, kuma ya bayyana yin hukunci mai tsanani. Ya nuna a fili cewa gyara, wanda muka riga muka gabatar, buƙata ce mai matuƙar muhimmanci. Ga Calvin, a bisa ga ka’idar maganar Allah, ya amince game da ikklisiyar Roman Katolika cewa “duk irin siffar ibadar bauta ga Allah da ake aiwatarwa gaba ɗaya a zamanin yau, ba komai bane sai lalaci kawai
A ra’ayin Calvin, ibadar ikklisiya a zamani na tsakiya ya zama “tsananin bautar gumaka.” A gare shi batun bautar gumaka ya kasance yanayi mai tsananin muni matuƙa, kamar yadda yanayi na ayukan adalcin-kai yake in aka zo maganar barata. Dukan su biyun, suna wakiltar hikimar ɗan Adam ne a maimakon so ga faranta wa Allah rai, da kuma yi masa biyayya. Calvin ya nace cewa babu wani haɗin-kai da zai iya faruwa cikin yin ibada tare da masu bautar gumaka: “Amma za a riƙa cewa, ko dayake annabawa da manzanni sun sami rashin yarda da firistoci miyagu a ɓangaren koyarwa, amma duk da haka, har yanzu suna yin tarayya da su a cikin hadayu da addu’o’i. Na yarda sun yi, idan har ba tilasta masu aka yi ga bautar gumaka ba. Amma wane ne daga cikin annabawa muka karanta cewa ya taɓa yin hadaya a Bethel?”
Kamar yadda ya kasance da annabawa na da can, masu Gyara sun buƙaci su tsauta wa bautar gumaka da kuma “bautar ganin ido” na irin ibadar zamanin su. Hanyar magance wannan mai kamar wasan kwaikwayo na ikklisiya ta zamanin Calvin, shi ne kawai ibada cikin sauƙi da ke dauƙaƙa Allah – kamar yadda aka nuna a cikin tsarin hidima sujada a ikklisiyar Geneva. Irin wannan sassauƙar ibada na ƙarfafa masu bauta su ba da tunanin su, duk tare da jikunan su don ibada: “Duk da cewa ya zama wajibi masu ibada ta gaskiya su ba da zuciya da tunani, amma a kullum mutane suna sha’awar ƙirƙirar salon bautar Allah wanda kwata-kwata yake da tsari daban, abin da suka saka a gaba shi ne, su aikata masa wasu ayuka na jiki, amma kuma su riƙe tunani da zuciya wa kansu.”
Baratawa
Abu na gaba da Calvin ya fuskanta shi ne batun barata. A nan ya bayyana cewa saɓani ra’ayi shi ne abu mafi ƙarfi: “Babu wani batu da aka fi jayayya a kai, kuma babu wani batu da maƙiyan mu suka fi nuna ra’ayin riƙau kan matsayin su, dangane da batun barata, cewa, ko mun samu ta wurin bangaskiya ne ko kuma ta wurin ayyuka.” “Lafiyar ikklisiya” ta dogara ne kan wannan koyaswa, amma saboda yawan kurakurai a kan ita koyaswar, Ikilisiya ta jawo wa kanta “mummunan rauni mai tsanani, kuma har ta kai dab da rushewa.”
Calvin ya nace cewa, baratarwa ta wurin bangaskiya ne kaɗai: “… mun yarda cewa, ko da wane irin sifar ibada ayukan mutum ke dauke da ita, abin da kaɗai ke mai da shi adali a gaban Allah, shi ne, alherin jinƙan Allah kadai; domin Allah, ba tare da duban ayuka a matsayin wani abu ba, ya karbe shi a matsayin ɗa ko ‘ya kyauta, cikin Almasihu, ta hanyar lissafta adalcin Kristi a gare ta ko gare shi, kamar nasa ne.”
Wannan koyarwar tana da matuƙar tasiri a rayuwa da takun Krista: “… ta wurin shawo kan mutum ya amince da talaucin sa, da rashin ƙarfin sa, muna horar da shi na kwarai zuwa ga tawali’u na gaskiya, muna jagorantar sa ga musunta duk wani hali na mutum ya sa-aminci ga-kansa, sannan ya sa dogaron sa duka ga Allah gaba ɗaya; a haka nan kuma, mu horar da shi matuƙa zuwa ga yin godiya, ta hanyar jagorantar sa zuwa ga nunawa cikin gaskiya kamar yadda ya dace cewa, duk wani abu mai kyau da yake da shi, ya samu ne ta dalilin alherin Allah”
Sakaramenti (Sacrament)
Batu na uku da Calvin ya duba shi ne sakaramenti wanda ya yi bincike na dalla-dalla. Ya yi kukan cewa “… an ɗora ayukan ibada waɗanda mutane suka tsara, a daidai matsayi ɗaya da ire-iren abubuwan sirri da Kristi ya kafa” kuma an mai da Jibin Ubangiji musamman ya zama kusan kamar “wani wasan kwaikwayo.” Irin wannan wulaƙanci ga sakaramenti na Allah abu ne da ba zai karɓu ko kuma a jure da shi ba. “Abu na farko da muke kokawa da shi a nan shi ne, ana shagaltar da mutane da bukukuwan nuna burgewa, alhalin ba a bayyana komai game da muhimmancin su, da kuma gaskiyar su. Domin babu wani amfani a cikin hidimomi na sakarmenti, sai dai idan aka bayyana abin da alamar ta ke wakilta bisa ga Maganar Allah.”
Calvin ya yi kuka cewa sauƙin koyaswa na sakaramenti, da ayyuka da suka yi tasiri a cikin Ikklisiya ta farko sun ɓata. An fi ganin wannan a fili a cin Jibin Ubangiji, da Hadaya ta Yukaris, cewa jibin yana ainihin canzawa zuwa jini da jikin Kristi, tare da yi ma waɗannan keɓaɓɓun gurasa da ruwan inabi sujada, ba koyaswar Littafi Mai Tsarki ba ce, kuma suna ɓata ainihin ma’anar sakarment. “Yayin da ya kamata sakarmenti ya kasance hanyar daga zukatan masu bege zuwa Sama, sai gaba ɗaya aka ɓatar da maƙasudi na wannan tsattsarkan hidima ta Jibin zuwa wasu manufa dabam-dabam, kuma ‘yan Adam sun gamsu da kafa idanu a kansu, da yi musu ibada, ba tare da tunanin Almasihu ba ko kadan.” An lalatar da aikin Kristi, kamar yadda ake gani a cikin hidimar hadayar yukaris inda “…Kristi ana yanka shi hadaya sau dubu a rana, kamar dai abin da ya yi a lokacin da ya mutu sau daya domin mu bai isa ba.”
Calvin ya taƙaita ainihin ma’anar jibin cikin sauƙi: “. . . muna ƙarfafa duka su zo cikin bangaskiya . . . . muna. . . wa’azin cewa, da jikin da jinin Kristi duka Ubangiji ne ya ba mu a cikin cin Jibin; muka kuma karɓa. Haka nan kuma, da muke koyar da cewa gurasa da ruwan inabi alamu ne, mukan ƙara da bayyana cewa akwai gaskiyar abin da ke dangane da su, kuma suke wakilta.” Zahiri, Kristi yana ba da kansa, da dukan fa’idodin ceton Sa zuwa ga waɗanda suka aiwatar da cin jibin ta wurin bangaskiya.
Wannan taƙaitaccen bayani na tattaunawar Calvin game da sakaramentin ya ba mu ɗanɗano ne kaɗan game da yadda ya ɗauki wannan muhimmin batu. Ya mai da hankali sosai ga baftisma tare da musanta matsayin Romawa na cewa akwai wasu ƙarin sakaramenti guda biyar.
Gwamnatin Ikilisiya
A ƙarshe Calvin ya juya ga batun gwamnatin ikklisiya. Ya lura cewa wannan batu ne mai matuƙar girma: “Idan da na ce zan yi bayani dalla-dalla kan kurakuran gwamnatin ikklisiyoyi, da ban kammala ba.” Ya mai da hankali kan mahimmancin matsayin fasto. Cewa alhakin koyaswa da hakkin koyaswa suna tushen wannan matsayi: “… babu wani mutum da yake faston ikklisiya, na ƙwarai da za a ce wai ba ya yin koyaswa.” Ɗaya daga cikin manyan nasarori da Gyaran ya yi shi ne, maido da wa’azi bisa matsayin da ya dace cikin rayuwar mutanen Allah.”…Ba za a iya ganin ko ɗaya daga cikin ikklisiyoyin mu ba, sai dai idan tana ainihin wa’azin Kalmar. Dole daga matsayin fasto ne za a danganta tsarki da kuma koyarwa: “… . . . ya kamata waɗanda suke shugabantar Ikilisiya su fi bunƙasa gaba da wasu, su kuma haskaka ta wurin kasancewa misali na rayuwa mafi tsarki. . . .”
Calvin ya koka cewa, maimakon koyarwa da biɗan tsarki, shugabanci ta ikklisiyar Roman tana yin “zalunci mai matuƙar muni” akan rayukan mutanen Allah, suna da’awa akan ƙarfi da ikon da Allah bai ba su ba. Gyaran ya kawo ’yanci mai ɗaukaka daga al’adu waɗanda ba al’adu daga Littafi Mai Tsarki ba ne, waɗanda kuma suka ɗaure ikklisiya. “Kamar yadda dama ya kasance, aikin mu ne mu kuɓutar da lamiri na amintattu daga mummunan bautar da bai kamata ba, wanda kuwa aka damƙe su a ciki,, saboda haka mun koyar da cewa sun zama ‘yantattu, kuma sun tsira daga dokokin ’yan Adam, kuma wannan ’yanci, wanda jinin Kristi ne ya saya, ba za a iya lalata shi ba.
Ikilisiyar Roman tana ɗauka zaɓen manzanni da matuƙar muhimmanci, musamman ma wajen naɗa wannan matsayi. Calvin ya nace cewa gyara da aka yi game da naɗa wannan matsayi yana bin ainihin koyarwa da ayukan Kristi, da na manzanni, da kuma ikklisiya ta da. Ya lura ya ce, “Saboda haka, babu wanda zai iya yin da’awar hakki na ikon naɗa wani, idan har wai yana kare haɗin-kan ikklisiya ta hanyar koyarwar tsarkakakkiya ba.”
Gyarawa
Calvin ya kammala wannan bayani tare da yin tunani kan tafarkin gyarawa. Ya alaƙanta farkon ga Luther wanda cikin “sannu a hankali” ya yi kira ga gyara. Amsa daga Roma ya zama wani ƙoƙari ne “don murƙushe gaskiya tare ta yin tashin hankali da mugunta.” Wannan yaƙin bai zama da mamaki ba wa Calvin domin “… Ƙaddarar bishara iri ɗaya ce, tun farkon farkon ta, ta kasance, kuma har abada tana nan, har zuwa ƙarshe, za a yi wa’azinta a duniya cikin tsananin jayayya.”
Calvin ya ba da dalilin yiwuwar wannan matsala a rayuwar ikklisiya, cewa saboda muhimmancin batutuwan da ake jayayya a kai ne. Ba ya yarda a sassauta gaskiyar cewa “dukan abin da ke zahiri game da addinin Krista” yana cikin fuskantar barazana. Tun da yake masu gyara sun yi aiki ne cikin biyayya ga Littafi Mai Tsarki, sai ya yi watsi da duk ra’ayin da cewa sun kasance masu kawo tsattsaguwa: “… Abu na farko da ya kamata a mai da hankali a kai shi ne, a yi hattara kada a raba Ikilisiya daga Kristi, wanda shi ne Kan ta. Idan na ce Almasihu, ina haɗawa ne da koyaswar bisharar Sa, wanda Ya hatimce da jinin Sa ….domin haka, bari ya zama tsayayyen matsayi da muka amince da shi cewa, akwai haɗin kai tsarkakakke tsakanin mu, a lokacin da muka yarda cikin koyaswa tsattsarka, muna tare cikin Kristi kaɗai.” Ba sunan ikklisiya shi ke tanadar da haɗin-kai ba, amma gaskiyar aƙidar ikkilisiya ta ƙwarai, wadda ke rayuwa cikin Maganar Allah.
Calvin ya juyo ga tambaya mai amfani na wanene zai iya jagorancin hanya ga gyara cikin ikklisiya, a yadda ya kamata. Ya ƙi yarda da ra’ayin cewa Paparoma zai iya jagorantar ikklisiya, ko kuma gyaran, cikin harshe mafi ƙarfi: “Ina musun cewa wannan kuiera ta Manzanni, wadda ba a gani kome a cikinta sai mummunar ridda – ina musun shi ya zama wakilin Kristi, domin a cikin tsananin tsananta wa bishara yana nuna da ayyukansa cewa shi ne Makiyi Kristi – na ƙi yarda da shi ya zama wanda zai gaji Bitrus, shi da yake duk iyakacin ƙoƙarin sa ya rusa duk wani tsayayyen abu da Bitrus ya gina, kuma na musunta shi ya zama shugaban ikklisiya, wanda ta wurin tsananin muguntar sa ya lalata, da kuma wargaza Ikilisiya, bayan ya raba ta daga Kristi, Shugabanta na gaskiya kuma Kan ta kaɗai.” Ya san cewa mutane da yawa suna kira da a kafa majalisa ta duniya don magance matsalolin ikklisiya, amma yana fargaban cewa irin wannan majalisa ba za ta taɓa haɗuwa ba, amma kuma idan ta yi hakan, iko zai kasance a hannun Paparoma.
Ya ba da shawarar cewa ikklisiya ta bi tsarin tsohuwar ikklisiya, su riƙa sassanta al’amura na ƙananan hukumomi ko na lardunan su daban-daban. Amma, mun danƙa dukan batun gaba ɗaya ga Allah, wanda zai ba da albarkar da Ya ga ta dace ga ƙoƙari gyaran: “Hakika, mu masu marmari ne, a yadda ya kamata, cewa hidimar mu ta bishara za ta kai ga zama abin yabo ga duniya, sai dai samun nasarar hakan yana hannun Allah, ba a gare mu ba.”
An fara buga wannan tsararren rubutu ne a shafin ma’katar bishara ta Ligonier.


