Aƙidu da Furucin Imani na Furotestan
01/01/2026
Shawarar Luther Domin Rayuwa ta Krista
08/01/2026
Aƙidu da Furucin Imani na Furotestan
01/01/2026
Shawarar Luther Domin Rayuwa ta Krista
08/01/2026

Mene ne Ranar Gyara

Faruwa guda ɗaya a rana guda ɗaya ya canza duniya. Ranar ita ce 31, na Oktoba, 1517. Ɗan’uwa Martin, wanda monk ne (wani ɓangaren mabiya addini da ke ɗaukar niya ta rayuwa cikin talauci, da tsarki, da biyayya), kuma malami-masani, ya wahala da ikklisiyar sa, ikklisiya da ke a Roma. Ya damu matuƙa saboda wata faruwa da ba a taɓa gani ko yin irin ta ba, abin da Ikklisiyar katolika take yi wanda mutane za su yi ayuka na neman tuba daga zunuban su, ko su sami ragi kan lokacin da za su yi a purgatory ko fogatiri (wani wuri da wai idan mutum ya mutu cikin zunubi, za a saka shi ya ɗan sha tsanani sannan a tafi aljanna daga baya), Labarin yana nan cikin kamannin wani ƙasaitaccen fin na Hollywood. Bari mu ga ‘yan wasan wannan yanayi.

Da farko, akwai matashin bishof- matashi ne sosai yadda bai kai tsarin da ikklisiya ke buƙata na matsayin ba, shi ne-Albert na Mainz. Ba kawai ya yi Bishof a kan yankuna biyu na bishofs kawai ba, amma har ya so a ƙara masa yankuna na bishofs a nan Mainz. Wannan ya ƙetare dokokin ikklisiya. Don haka, sai Albert ya yi roƙo a wajen Paparoma na Roma, Leo X. Wanda ya fito daga iyalin De Medici. Saboda kwaɗayi, Leo X ya bari sha’awar sa ta wuce arzikin da yake da shi. Wannan yanayi ya tsoma shi cikin ruɗani.

Sa’adda Albert na Mainz ya roƙi dama domin a cire masa hakkin kiyaye wasu dokoki, sai Leo X ya yarda. Albert kuwa riƙe da wannan dama da aka ba shi, ya dinga sayar da wani abu da ke a matsayin sayen gafara, domin zunuban da suka wuce, da waɗanda aka aikata yanzu, da kuma waɗanda za a aikata nan gaba. Dukan wannan ya zama abin damuwa matuƙa ga Martin Luther. Ko za mu iya sayen hanyar mu zuwa Sama? Ya zamana dole Luther ya yi magana.

Amma me ya sa ranar ta kasance 31, na Oktoba? 1 ga Nuwamba muhimmiyar rana ce a kalandar ikklisiya a matsayin Ranar Tsarkaka. A ranar 1 ga Nuwamba, aka yi wani babban baje koli,wanda aka fito da wasu sabobbin abubuwa na da can, har ma da wasu ɓangarorin jikunan tsarkaka da suka daɗe da muta, da dai ire-iren haka, aka baza kolin su a garin Wittenberg babban birnin garin su Luther. Matafiya masu yawon buɗe ido, suna zuwa daga wurare daban-daban,suna russunawa cikin sujada a gaban waɗannan abubuwa da aka baza, wai ta yin haka suna cire daruruwan shekaru in ma ba dubbai ba daga cikin shekarun da ya kamata su yi a fugotiri. Wannan ya sa ruhun Luther ya yi tsananin ƙuna. Sam babu abin da ya dace cikin duk abubuwan.

Martin Luther, wannan malami-masani, ya ɗauki alkalamin sa a hannu, ya tsoma cikin tawadar sa, sa’annan ya rubuta bayani na zurfafan batutuwan nan nasa guda casa’in da biyar, a ranar 31, Oktoba, 1517. Ya yi hakan ne da nufin tayar da mahawara, da kuma jawo kyakkyawar nadama cikin ruhaniya a tsakanin ’yan’uwansa  na cikin ikklisiya. Waɗanna zurfafan batutuwa sun haifar da abin da ya fi ƙarfin muhawara. Haka kuma waɗannan muhimman batutuwa guda casa’in da biyar sun nuna cewa ikklisiya tana buƙatar abin da ya wuce kwaskwarima, tana buƙatar Gyara ne. Ita Ikklisiya -da duniyar ma -ta canza, ba za ta sake kasancewa yadda take a da ba. 

Ɗaya daga cikin batutuwa casa’in da biyar ɗin da Luther ya bayar shi ne furucin da ke cewa, “Dukiyar Ikklisiya ta zahiri ita ce, bisharar Yesu Kristi.” Wannan kaɗai shi ne ma’anar Ranar Gyara. Ikklisiya ta ɓatar da fahimtar ta na bishara, domin tun da daɗewa ta yafa ƙyalle bisa ƙyalle na al’adu a kan shafunan Maganar Allah. Al’adu kaɗai suna yawan haifar da tsari da ke mai da hankali kan aikata ayuka kawai, irin tsari na yin ayuka domin samun karɓuwa a gaban Allah. Ainihin abin da farisawa suka yi kenan, haka kuma ya kasance da Roman Katolika na tsakiyar zamani. Ko ba Kristi da kansa ya ce, “Karkiya ta sassauƙa ce, kaya na kuma marar-nauyi”? Ranar Gyara, ranar biki ne na farin cikin kyaun bisharar ‘yantarwa ta Yesu Kristi. 

Mene ne Ranar Gyara? Rana ce wadda hasken bishara ya ratso, ya kuma haskaka daga cikin duhu. Ita ce ranar da ta fara nuna Gyara na Furotestan. Ita ce ranar da ta kai su Martin Luther, da John Calvin, da John Knox, da wasu Masu-Gyara dayawa, zuwa ga taimakon ikklisiya ta nemi hanyar komawa ga Maganar Allah a matsayin ta na kasancewa ita kaɗai ke da iko-duka a kan bangaskiya da rayuwa, da kuma jagorantar ikklisiya ta koma ga tsattsarkar koyarwa ta barata ta alheri ne kaɗai, kuma ta hanyar  gaskantawa ne kaɗai,  cikin Kristi kaɗai. Ya hura wuta daban-daban zuwa ga ɗaukar niyyar yin ayukan mishan, ya yi jagora zuwa ga rubuta waƙoƙi, da raira waƙoƙi na jama’a duka a lokacin sujada cikin ikklisiya, kuma ta haifar da tarayya na bishara da wa’azi domin jama’ar Allah. Biki ne na samun canji a ɓangaren tauhidi, da ɗabi’un mujami’u, da kuma al’adu.   

Saboda haka ne muke bikin Ranar Gyara.  Wannan ranar tana tuna mana mu kasance da godiya domin rayuwar mu ta da, da kuma don shi monk, wanda ya zama Mai-Gyara. Bayan haka ma wannan ranar tana tuna mana da aikin mu, da hakkin da ya rataya a kan mu, da kuma buƙatar mu ci-gaba da fifita hasken bishara ya kasance tushe, wato, cibiyar duk abin da muke yi.


An fara buga wannan tsararren rubutu ne a shafin ma’katar bishara ta Ligonier.

Stephen Nichols
Stephen Nichols
Dr. Stephen J. Nichols shi ne shugaban Reformation Bible College, kuma babban ofisan harkokin ilimi na Ministirin Ligoniya. Yana koyaswa a wata kafa ta yanar gizo na 5 minutes in Church History. Shi mawallafin litattafai dayawa ne, sun haɗa da, Beyond the 95 Theses da A Time For Confidence, da kuma R.C. Sproul: A life.