Menene Bautar Allah Ɗaya?

01/10/2026

Yesu ne Sabuwar Dawuda

08/10/2026

Menene Bautar Allah Ɗaya?

01/10/2026

Yesu ne Sabuwar Dawuda

08/10/2026

Menene Kame Kai?

Yaya kake iya kame kanka? Watakila kana karanta wannan bayani ne a kan wayar hannu, kuma wayoyin hannu na iya rage kwazo wajen kame kai fiye da kowane abu a duniyarmu. Masana sun gaya mana cewa yawan gungura abubuwa a waya ba tare da tsayawa ba yana sa mutum ya saba da neman jin dadi na nan take, kuma hakan yana karfafa halayen zaman banza da jinkirta yin abin da ya kamata a yi.

Amma ɗan nazari zai gaya mana cewa ba za mu iya ɗora wa wayoyinmu laifi ba—ko kowane abu na zahiri a duniya—domin rashin kamun kanmu. Laifin yana kanmu ne kai-tsaye; ashe ma’anar tana cikin kalmar “kame kai” da kanta, ko ba haka ba?

Kalmar nan kame kai ba ta bayyana a fassarorin Littafi Mai Tsarki na Turancin zamani ba, amma wadda take da dangantaka ta kusa da ita, wato kamun kai, tabbas tana nan. Kamun kai, wato mulkin kai, hali ne na tsoron Allah; lallai, siffa ce irin ta Allah. Lokacin da Allah ya fara halittar sama da duniya, ya yi aiki ne bisa ga ƙayyadadden nufi kuma a cikin ƙayyadadden lokaci (Far. 1). Bai gudanar da aikinsa ba tare da tsari ba, ba tare da tabbacin abin da zai yi daga rana zuwa rana ba, yana ƙirƙira yayin da yake tafiya. Kuma a yanzu haka, yana ci gaba da yin aiki a kan wannan tsari (Yohanna 5:17).

Allah Allah ne na tsari, ba na hargitsi ba (1 Kor. 14:33). Ana yawan daraja yin abubuwa barkatai ba tare da shiri ba a al’adunmu, kuma tabbas akwai madaidaicin wuri domin hakan, amma yana iya rikida cikin sauki ya koma gangancin rishin tunani, wanda shi ne cikakkiyar kishiyar kamun kai. Saboda haka, idan kai ko ni muna nuna kamun kai, muna koyi da Mahaliccinmu ne. A zahiri, ko da yake yana iya zama kamar wani sabani, za mu iya cewa mutumin da ya fi kowa kamun kai shi ne mutumin da Allah ya fi iko da shi.

Akwai nassosi uku a cikin Sabon Alkawari waɗanda suka fi fito da muhimmancin kamun kai fili.

1. 1 Korintiyawa 9:24–27

Na farko shi ne 1 Korinthiyawa 9:24–27. A nan Bulus ya kwatanta rayuwar Kirista da gudun tsere dogon zango da kuma wasan dambe. Ya kwatanta kamun kai wanda dukkan ‘yan wasa dole ne su nuna yayin da suke gudu. Tun da yake da yawa daga cikinmu muna rayuwa ne a cikin al’ummar da ta shagala da wasanni, mun fahimci cewa manyan ‘yan wasa dole ne su bi tsauraran ƙa’idoji na abinci, motsa jiki, kamun kai, da barci, ba wai kawai a ranar da suke tseren ba, amma a kowace rana.

Bulus ya yi amfani da wannan ga dukan rayuwar Kirista: “Ina horar da jikina, ina sanya shi cikin ikona, domin bayan na yi wa wasu wa’azi, kada in zama wanda aka ƙi” (1 Kor. 9:27). Ɗan wasan da ke tseren dogon zango ba ya rasa manufa ko dalili. Amma Kirista ma ba haka yake ba. Horar da kai na tsawon rai yana farawa sa’ad da muka yi tambayoyi irin su: Wane ne ni? Don me nake nan? Menene burina, kuma ta yaya ya kamata in yi niyyar cimma su? Amsa ta farko a cikin Gajeriyar Littafin Koyarwa na Westminster ta bayyana ainihin gaskiyar ta hanyar tunatar da mu cewa “babban ƙarshen mutum shi ne ya ɗaukaka Allah, kuma ya ji daɗinsa har abada.” Komai a rayuwata dole ne ya kasance ƙarƙashin wannan babban buri.

2. Galatiyawa 5:22–23

Nassi na biyu shi ne Galatiyawa 5:22–23, inda Bulus ya lissafo amfanin Ruhu: “kauna, farin ciki, salama, haƙuri, kirki, nagarta, aminci, tawali’u, kamun kai.” Ka lura cewa wannan jerin amfanin Ruhu ya zo ne nan da nan bayan wani jerin “ayyukan jiki” (Gal. 5:19–21), kuma bisa ga ainihin ɗabi’arsu, waɗannan “ayyukan jiki” shawa’o’i ne na mugunta, marasa kamun kai. Sha’awoyin ɗan-adam na yau da kullum sun fita daga iko; suna kama da kogin da ya ɓalle wa gaɓoɓinsa, wanda ke haifar da barna da halaka ko’ina.

Ka lura kuma cewa “ƙauna” da “kamun kai” ne suka kewayi lissafin amfanin Ruhu a farko da ƙarshe. Mun sani cewa a cikin Sabon Alkawari, ana yawan ɗaukar ƙauna a matsayin mafi girman nagarta—“mafi girma cikinsu ita ce ƙauna” (1 Kor. 13:13)—amma har ƙauna ma dole ne a yi mata jagora kuma a tsara mata madaidaiciyar hanya. Kamun kai, ko horon kai, ya amince da wanzuwar sha’awoyin ɗan-adam na abinci, abin sha, hutu, jima’i, nishaɗi, wasanni, da duk sauran su, amma yana gina hanyoyin kiyaye su cikin tsanaki domin kada su ɓalle wa gaɓoɓinsu su rikida su zama sha’awoyi na mugunta marasa iyaka. Ba don haɗari ba ne sa’ad da Bulus ya rubuta wa Titus, wanda yake hidima a Kireta—wani tsibiri da aka sani da rashin tarbiyya—ya ambaci buƙatar zama masu “kamun kai” sau da yawa sa’ad da yake magana da rukunoni daban-daban na wannan al’umma: “maza tsofaffi,” “mata matasa,” “samari,” lallai “dukan mutane” (Titus 2:1–12).

3. 2 Timoti 1:7

A ƙarshe, yi la’akari da 2 Timoti 1:7: “Gama Allah bai ba mu ruhun tsoro ba, amma na iko da na ƙauna da na kamun kai.” Ina tsammanin wannan kalma ce da ta dace da lokaci ga Kiristoci masu aminci da ke rayuwa a ƙarni na ashirin da ɗaya. Al’adar da ke kewaye da mu ta ƙara zama mai ƙasƙantarwa, fushi, da rashin haƙuri, har ta kai masu bi za su iya jin tsoro saboda adawa da zalunci. Ya bayyana sarai daga Sabon Alkawari cewa Timoti mutum ne mai ɗan natsuwa da jin kunya wanda yake buƙatar a ƙarfafa shi ya ci gaba da yin hidima “ko lokaci ya yi, ko bai yi ba” (2 Tim. 4:2).

Wani darasi da za mu iya ɗauka daga wannan nassi wataƙila yana da ɗan ban mamaki, amma yana da kima ƙwarai. Kamun kai, ko horon kai, shi ne maganin tsoro da damuwa waɗanda za su iya addabar mu cikin sauƙi. Domin ainihin asirin horon kai shi ne kasancewar Allah da ikon Allah tare da mu a matsayin mutanensa; haƙiƙa horon-Allah ne—wato Maganar Allah da Ruhun Allah suna jagoranci da kuma juya duk abin da nake yi da faɗa a matsayin ɗan Allah wanda aka haɗa shi da Yesu Almasihu, har ma yayin da nake tarayya a cikin tunanin Almasihu kansa (Filib. 2:5).


An fara wallafa wannan talifi ne a shafin Blog na Ministirin Ligonier. [Blog ɗin Ministirin Ligonier]

Paul Yeulett

Paul Yeulett

Rev. Paul Yeulett shi ne ministar a Grove Chapel da ke London.