
Ikon Tsarkin Allah da ke Canza Rayuwar Yau da Kullum
19/11/2026Yesu ne Sabuwar Haikalin
Me kake tunani sa’ad da kake tunanin haikali a cikin Littafi Mai Tsarki? Wataƙila kana tunanin wani kyakkaywan tanti da aka yi wa ado a cikin jeji, wanda aka hada shi da kyawawan labule tare da sandunan zinariya da suka kewaye wuri mai tsarki. Ko kuma wataƙila ka yi tunanin wani babban gini mai kerubobi da ke gadin ƙofar shiga Wuri Mafi Tsarki, tare da itatuwan rumman da aka zana a jikin ganuwar da aka ƙawata da zinariya. Wataƙila ma ka yi tunanin manyan duwatsun da aka sassaka, da aka zana aka kuma kafa su a sarai a sama, suna tsaye a matsayin abin mamaki na zamanin Hiridus na duniyar dā a Urushalima. Dukan waɗannan hotunan kwatanci ne na gaskiya na lokuta daban-daban na haikali a cikin Littafi Mai Tsarki. Abin da zai iya zama abin mamaki, shi ne cewa Nassi ya gaya mana cewa lokacin da muke tunanin haikali, ya kamata mu yi tunanin Yesu. Duk wani abu dabam inuwa ce kawai da ke nuna Shi.
Haikali na farko da ya bayyana a cikin Nassi shi ne lambun Adnin. Kamar tantin sujada da haikalin da aka yi daga baya, Allah ya halicci Adnin ya zama wuri mai tsarkinsa, mazaunin da zai kasance tare da mutanensa. Kafin faɗuwa cikin zunubi, Adnin an nufa ta zama wannan wuri mai tsarki. Saboda wannan dalili, Allah ya yi tafiya a cikin Adnin kamar yadda ya yi daga baya a cikin tantin sujada (Far. 3:8; Lev. 26:12; M. Sha. 23:14; duba kuma 2 Sam. 7:6–7). An shiga Adnin da tantin sujada daga gabas (Far. 3:24; Fit. 26:18–22), kuma kerubobi ne suka tsare Adnin da haikalin Sulemanu (Far. 3:24; Fit. 26:31; 1 Sar. 6:23–29) waɗanda suke cike da bishiyoyi (Far. 2:16; 1 Sar. 6:20–36). Adamu da firistoci su ne za su “yi aiki kuma su kiyaye” wurare masu tsarkinsu (Far. 2:15; Liss. 3:8; 8:26; 18:5–6). Adnin haikali ne.
Domin Adamu ya faɗa cikin zunubi, an fitar da shi daga wuri mai tsarki. Lokacin da Allah ya ceci mutanensa daga Masar, cikin alheri ya sake kafa wuri mai tsarki inda masu zunubi za su iya tunkararsa cikin tuba da sujada ta hanyar maimaita miƙa hadayu (Ibran. 10:1). Allah ya kafa wannan “Alfarwa ta Taruwa,” wato mazauni, domin ya kasance tare da mutanensa (Fit. 29:45–46). Amma bayan an kammala mazaunin, Isra’ila suka ga cewa gajimare mai tsarki na gaban Allah ya bukaci tsarki ga dukan waɗanda za su kusanto. Saboda haka, babu wanda zai iya shiga, har ma da Musa (Fit. 40:35). Sarki Sulemanu ya gina wani babban Haikali wanda ya fi alfarwar sujada girma, kuma wannan gajimare ya lulluɓe wannan haikali, yana nuna alamar cewa firistoci ma ba za su iya shiga gaban Mai Tsarki ba (1 Sar. 8:10–11).
Bayan Nebuchadnezzar ya ruguza haikalin Sulemanu kuma ya kai Isra’ila bauta, daga baya sarkin Farisa, Cyrus Mai Girma, ya ƙyale Isra’ila su koma ƙasarsu kuma su kafa sabon haikali (Ezra 1; 2 Labarbaru 36:22–23). Amma sa’ad da tsofaffin maza waɗanda a dā suka ga haikalin Sulemanu suka ga wannan sabon ginin, sai suka yi kuka da baƙin ciki, gama sun san cewa wannan haikali na biyu ba zai taɓa cika abin da annabawa suka faɗa ba (Ezra 3:12). Annabawan Tsohon Alkawari sun yi tsammanin cewa al’ummai da yawa—Yahudawa da Al’ummai—za su zo Urushalima su yi bauta a haikalin (duba Ishaya 2:1–5). Duk da haka sun fahimci cewa wannan haikali zai fi na Sulemanu girma nesa ba kusa ba; wannan sabon haikali zai girgiza sammai da duniya, ya zama ɗaukaka da ceto ga dukan mutane (Haggai 2:5–9), ainihin abin da Allah ya ce, “Zan kasance tare da ku” (Haggai 2:4).
Haikalin da tsarkakan Tsohon Alkawari suka yi marmarinsa ya zo a cikin Ɗan Allah wanda ya zama mutum. Yesu Banazare ne ya zo domin ya zauna, ko kuma ya yi “alfarwa” a tsakaninmu (Yohanna 1:14). Shi ne ainihin kasancewar Allah, inda dukan cikar allahntaka take zaune a jiki (Kol. 2:9–10). Yesu da kansa ya faɗi haka sa’ad da ya gaya wa Yahudawa, “Ku rushe wannan haikali, a cikin kwana uku kuma zan tada shi” (Yohanna 2:19). Yayin da Yahudawa suka ɗauka cewa maganganunsa na zahiri ne, Yesu yana magana ne a ruhance game da kansa, ainihin haikalin Allah (Yohanna 2:20–21). Hakika, a matsayinsa na firist, ya miƙa kansa ta wurin cikakkiyar rayuwarsa da mutuwarsa ta hadaya, domin masu zunubi su sami damar shiga gaban Tsarkakken Allah a cikin haikali ta wurin hadayarsa (Ibr. 9:11–14; 10:19–20). Yesu ne firist, hadayar, kuma haikalin, duka a lokaci guda.
Amma Sabon Alkawari kuma ya kwatanta haikalin a wata hanyar. A cikin 1 Korintiyawa 3:16–17, Bulus ya bayyana cewa:
Ba ku sani ba ne cewa ku haikalin Allah ne, kuma Ruhu Allah yana zaune a cikinku? Idan kowa ya lalata haikalin Allah, Allah zai lalatar da shi. Domin haikalin Allah mai tsarki ne, ku kuwa ne wannan haikalin.
Sa’ad da Bulus ya rubuta cewa “ku ne haikalin Allah,” kalmar “ku” ba ta mutum guda ba ce, amma mutane da yawa, wanda ke nufin Bulus yana yi wa mutanen Allah magana ne a matsayin ikilisiya baki ɗaya. Ma’ana, ikilisiyar Yesu Almasihu ita ce haikalin kuma. Domin kuwa, ana siffanta masu bi da surar Almasihu (Rom. 8:29), tun da Ruhunsa yana zaune a cikinmu. Kasancewar Allah da ikonsa suna cikin ikilisiyarsa, yana shafa mata Ruhu don aikin albarkaci ga al’ummai da bishara (Mat. 28:18–20; 2 Kor. 4:1–6). Mu, jikin Almasihu, haikali ne a cikinsa, domin yana mai da mu kamar kansa. Saboda haka, ikilisiya ita ce bayyananniyar nuna tsarkin Allah yayin da muke wakiltar Almasihu a wannan duniyar. A cikin Almasihu, mu birni ne a bisa tudu (Mat. 5:14) da kuma haske ga al’ummai (Isha. 49:6 tare da Ayyukan Manzanni 13:47), ta yadda duniya za ta iya ganin haikali na gaskiya ta wurinmu.
Yayin da Nassi ya kwatanta haikali da kyawawan labule, ganuwa da aka yi wa ado da zinariya, da kuma gine-gine masu ban mamaki, waɗannan duka inuwa ne masu nuni ga kyawawan abubuwan da suka riga suka zo (Ibr. 9–10). Ba muna neman wani haikalin ba ne. Muna da Shi.
An wallafa wannan makala ne da fari a Ministirin Ligonier Blog. [Blog ɗin Ministirin Ligonier]


