06/10/2026

Menene Kame Kai?

Allah Allah ne na tsari, ba na hargitsi ba (1 Kor. 14:33). Ana yawan daraja yin abubuwa barkatai ba tare da shiri ba a al'adunmu, kuma tabbas akwai madaidaicin wuri domin hakan, amma yana iya rikida cikin sauki ya koma gangancin rishin tunani, wanda shi ne cikakkiyar kishiyar kamun kai. Saboda haka, idan kai ko ni muna nuna kamun kai, muna koyi da Mahaliccinmu ne.