
Ko Gyare-gyaren Sun Ƙare
05/12/2025
John Calvin Akan Wajabcin Gyara Ikilisiya
10/12/2025Kafofin Da Aka Samo Asalin Tsarin Tauhidi
Babban tushen da masani a fannin tauhidi tsari (systematic theologian) yake dogaro da shi shine Littafin Mai-Tsarki. A zahiri ma Littafi Mai Tsarki shi ne tushe ga duk sauran fannonin Tauhidin nan uku, wato tauhidi dangane da Littafi Mai Tsarki, tauhidi dangane da tarihi da tauhidi bisa tsari na ƙwarai.
Tauhidi na Littafi Mai-Tsarki
Aikin Tauhidi dangane da Littafi Mai Tsarki shi ne ya duba, ya binciki tarin bayanai game da Nassoshi a yadda ya faru cikin duk lokaci, kuma wannan aikin ya kasance kafa ga tauhidi da ke bisa tsari na ƙwarai. Masanin Littafi Mai Tsarki yakan binciki nassi, sannan ya matuƙar binciki yadda sharuɗɗa, da manufofi, da jigogi suka ci gaba da bayyanuwa cikin Tsoho da Sabon Alƙawari, domin ganin yadda ake amfani da su, da yadda ake fahimtar su cikin yanayi na tarihin sauƙaƙƙen-wahayi.
Wata matsala da ake samu a manyan makarantu na tauhidi a yau it ace wata hanyan yin tauhidi a Littafin Mai -Tsarki da ake kira “atomism” wanda a cikinsa ake daukar ‘kwaya’ ta nassi tana tsaye da kanta ba tare da hada ta da sauran nassosi ba. Zai iya zamana cewa, wani babban masani ya yanke shawara ya ƙaiyade binciken sa game da ceto daga koyaswar Bulus da ke cikin Galatiyawa kaɗai, sannan wani kuma ya mai da hankali musamman ga bincike game da ceto daga koyaswar Bulus da ke cikin Afisawa kaɗai. Sakamakon haka shi ne, kowannen su zai kawo ra’ayi dabam game da ceto, ɗaya daga Galatiyawa, ɗayan kuma daga Afisawa-amma akwai matsala na rashin bincika yadda ra’ayoyi biyun suke daidaita. Kenan, abin da ake zato a nan shi ne cewa ba Ruhun Allah ne ya bishe Bulus ya rubuta Galatiyawa da Afisawa ba, don haka babu wani zuzzurfan tarayya, ko daidaita da Maganar Allah. A cikin wasu yan shekarun nan, ya zama ruwan dare a ji malamai suna cewa akwai bambance-bambance koyarwa tsakanin Bulus “na farko” da Bulus “ba karshe”, cewa yawan bambance tauhidi a cikin Littafi Mai-Tsarki daidai yake da yawan marubutan. Cewa akwai tauhidin Bitrus, akwai tauhidin Yahaya, da tauhidin Bulus da tauhidin Luka, kuma ba su daidaitu da juna ba. Wannan kuwa ra’ayi ne mara kyau game da daidaito da jituwa da ke cikin Nassi, kuma shine hatsarin da ke tasowa idan mutum yam ai da hankali kan karamin yanki na Littafi Mai-Tsarki ba tare da ya duba dukkan tsarin saukakken wahayi, ko bayyanawar Allah gaba daya ba.
Tauhidin Tarihi
Fanni na biyu, kuma wata kafa da aka samo tauhidi dake bisa tsari na ƙwarai, shi ne, tauhidin tarihi.
Masanan tauhidi na tarihi sukan duba yadda koyarwa ta bunkasa a tarahin rayuwan Ikklisiya, musamman a lokatan rikice-rikice, lokacin da karkatattun koyaswa suka fara tasowa, Ikklisiya kuma ta mai da martini. Masanan tauhidi na yau sukan ji takaici idan ake ganin wai sababbon rikic-rikice koyarwa sun taso a Ikklisiya ko makarantu, alhali Ikklisiya ta raga ta fuskanci kusan dukkan irin wandannan muhawarorin tun tarihi. A baya, Ikklisiya ta gundanar da manyan taruka kamar Majalisar Naisiya (AD 325) da Majalisar Chalcedon (AD 451). Nazarin wadannan abubuwan kwa shi ne aikin masanan tauhidi na tarihi.
Tauhidin Tsari na Ƙwarai
Fanni na uku shi ne, tauhidi tsari na Ƙwarai. Aikin masanan tauhidi tsari shi ne ya dubi ainihin wurin da aka samo takardu masu ɗauke da bayanai, yadda aka samu bayanai da suka kawo bunƙasa cikin duk jayayya, da majalisar ikklisiya da kalaman nan na furci da ikirarin bangaskiya. Da kuma zurfin fahimta na manya ƙwararrun masana wanda ikklisiya ta ci albarkacin su cikin tsawon ƙarnoni. Sabon Alƙawari ya bayyana mana cewa, Allah cikin alherin Sa ya ba mu malamai (Afisawa 4:11-12). Ba duka malaman ne masu zuzzurfan hikima kamar irin su Augustin, da Martin Luther, da John Calvin, ko kuma Jonathan Edwards ba. Waɗannan ba wai suna da iko irin na manzanni ba, amma kawai tsantsan yawan zurfin binciken su, da zurfin fahimtar su ya kawo wa ikklisiya riba cikin kowane tsara. Ikklisiyar Roman Katolika ta kira Thomas Aquinas da sunan “the doctor angelicus,” ko “angelic doctor” ma’ana “likita mala’ika. Ba wai Roman Katolika sun yarda cewa Aquinas ba shi da kuskure ba ne, amma babu wani masanin tarihi ko tauhidi na Roman Katolika da zai iya yin watsi da irin gudummawarsa.
Masanin tauhidi tsari na ƙwarai, ba kawai binciken sa ya tsaya ga Littafi Mai Tsarki da kalaman nan na furci da ikirarin bangaskiya kaɗai ba, amma har da morar zurfin hikima na manya ƙwararrarun malaman da Allah ya tanadar cikin dukan tarihi. Masanin tauhidi da ke bisa tsari na ƙwarai yakan dubi dukan bayanai da ke akwai -daga Littafi Mai Tsarki, da tarihi, da kuma ta tsari na ƙwarai-sannan ya haɗa su wuri ɗaya.
Da an buga a cikin Kowa Masanin Tauhidi ne na R.C. Sproul.
An fara buga wannan tsararren rubutu ne a shafin ma’katar bishara ta Ligonier.


